43=UKU-BALA'I

377 30 0
                                    

******
Sosai zuciyarta take bugawa a duk lokacin da Al'amarin Auranta da Dr.Erena ya zo mata filin tunaninta komai nata kwancewa yake yi komai nata take ji yana canzawa kamar ba nata ba.

Ta rasa ya zatayi ta rasa mai ya kamata tayi zuciyarta na zafi zuciyarta na raɗaɗi raɗadi mai girman gaske kudirin zuciyarta kawai take hangowa da ta dauka akan

wannan azzalumin mutumin bata so abin da zai hadata dashi a inuwa daya sam-sam ko zaman da take yi a Company sa kawai tana yi ne  don cinmma burinta amma ga yarda lamarin ya kasance har ya kai ga zancen aure a tsakaninsu.

Bata san wata irin rayuwa zatayi a gidansa ba bata san ya zata zauna ba zuciyarta na zafi tana shiga kunci duk lokacin da tunanin aurenta ya fado mata ba ta shirya masa ba ko da na kwana daya ne amma ba yarda za tayi tunda Hajiya Layla ta nuna kaunar ta akan lamarin kuma ta wannan hanyar ce kawai za su samu abin da suke so.

Sosai take mamakin yarda Hajiya Layla ta dauki lamarin da girma ta bada lokacinta da komai da ta san zai taimaka wajan tafiyar da komai yarda ya kamata.

"Areefa bawai ina son ki auri Dr.Erena bane a son raina a,a wallahi in da zan buɗe miki zuciyata ki ga bakinciki da takaicin da take yi akan wannan lamarin zaki ce naki ba komai bane amma na daure na mika zuciyata wani mataki na hakuri domin ganin ta yarje wannan lamarin ya kasance".

"Maama ban san ya zan koyi zama da makiyina ba ban san ya zan koyi zama da mutum kamar Dr.Erena ba daidai na sakan daya ne wai da sunan a idanuwa daya a matsayin mata da miji".

Wasu hawaye suka zubo mata a kunci masu dumi bata yi kokarin dauke su ba domin ko ta yi hakan ba daina zuba za suyi ba.

Hajiya Layla ce ta saka hannu ta dauke mata tana mai kwantar da ita kan cinyarta.

"Areefa ina so ki san wani abu guda san nan ki saka shi a zuciyarki auren Dr.Erena ba yana nufin kashe miki rayuwa bane auren Dr.Erena ba yana nufin numfashin ki ya daina wanzuwa bane a doron duniyar nan ki sani rayuwa ce zaki yi ta daukar fansa a gidansa wacce nake tsammani ita ce hanyar da tafi dacewa sannan ke dai ki zuba ido kiyi kallon komai zaki sha mamaki akwai ranar da zata zo da kan ki zaki zo kina bukatar al'amarin da yake wanzuwa a daidai wannan lokacin ba zan sanar dake komai yanzu ba amma duk ranar da komai ya tabbata zaki san komai".

Tashi tayi tana duban Hajiya Layla cike da mamakin furucinta sai faman juya idanu take yi tana rausayar da kai tana kokarin yin magana wayarta ta dauki Ring juyawa tayi ta dubi wayar a cikin jakarta dake yashe tun da ta dawo aiki yau gabadaya ta kasa sukuni ta kasa zaune ta kasa tsaye Hajiya Layla ce ta kai hannu ta dauki jakar ta fiddo da wayar ta mika mata ba musu ta ansa ganin mai kiran ya sanyata saurin dagawa don dama kamar ya san ta na cigiyarsa don sun kwana biyu ba su hadu ba gabadaya ta shiga wani irin yanayi na tashin hankali musamman yarda Dr.Erena ya sako ta gaba akan ta bashi dama ya turo domin neman aurenta.

Numfashi taja jin muryar Alhaji Abdulwahaaab ya ambaci sunanta.

"Areefa ina kika shige kwana biyu ne?".

Numfashi ta hadiye mai tauri kafin ta dubi Hajiya Layla.

"kai dai kawai bari al'amarin duniyar nan ne yake neman sha mini kai wallahi akan maganar mutumin ka ne Dr.Erena".

Murmushi yayi mai sauti wanda har sai da Areefa taji sosai kafun yaja numfashi.

"kisan na kusan barin duniyar nan kuma ba wanda na daurawa sai Dr.Erena kisan an tare ni a hanya akayi min dukan tsiya har sai da na rasa kai na...".

UKU BALA'I (Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora