UKU-BALA'I-3

2.8K 123 10
                                    

UKU BALA'I

NA

KAMALA MINNA

BABI NA UKU

Kuri likita yayi mata da idanu gabadaya hankalin sa da guntuwar natsuwar sa tana kan ta hannusa kuma yana mikawa nurses jaririn bayan ya yanke masa cibiya.

Abubuwa ne suka shiga yi masa dirkar mikiya a kwakwalwa zuciyarsa na ta tunano masa wasu abubuwa da baya fatan ace sun faru da wannan baiwar Allah ajiyar numfashi yayi gami da saurin duban Nurses da suma hankalinsu na kanta ganin halin da take ciki na rai kwakwai mutu kwakwai.

"maza kuje ku gyara jaririn sannan kuma ku dauko gado domin daukarta don na lura tayi matukar gajiya da galabaita".

Abin da likiti ya kokarta furtawa kenan cikin rashin tsammanin samun karfin daga laɓɓa har ya yi furuci gyaɗa kai yake yi yana gauraya kwayar idanuwansa cikin gurbin su laɓɓansa dake cikin bakin sa sai faman cizon su yake fuskarsa na kara bayyanar da rashin armashi da natsuwa.

Mikewa yayi cikin rashin kumaji duk wani azancin sa yana jin yarda yake kokarin kufce masa daurewa kawai yake yi yana yaki da batun da kwakwalwarsa da zuciyarsa suke ta sanar dashi ba zai so haka ba, ba ya faman haka ta kasance gyaɗa kai ya cigaba da yi kamar yana magana da wani ya ma rasa abin da ya dace yayi tunaninsa gabadaya ya wargaje sai akan abu daya wanda yake tsammmanin ba ɗa mai ido zai haifo ba.

Dawowar nurses ne ya dawo dashi daga duniyar fargaba da tsunduma ya shiga jan numfashi a hankali mai dauke da kayan tashin hankali
Ya dube su su duka yana mai kaɗa idanu yana mai yi musu nuni da ita nan suka shiga gyara mata jiki tamkar gawa haka suke sarrafa har suka kammala sannan suka daurata zaman gadon gami da gungurawa suka fice daga cikin dakin yana mai bin su da kallo numfashi ya ajje gami da jingina da jikin bango har zuwa lokacin zuciyarsa sai kokarin gasgata masa lamarin take wanda shi sam ba ya fatan hakan wuyar rigarsa ya gyara gami da jan jiki ya fice daga cikin dakin xan gefe ya hango Malam Bello tallabe da haba sai faman mazurai yake yi cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali kallo sosai likita ke bin sa da shi zuciyarsa na dauko tausayinsa tana jingina masa ta kowani bangare na sassan jikinsa sannu a hankali ya fara kokarin jan jiki ya isa gareshi amma sam bai san ya iso ba har sai da ya daf kafadarsa wata irin zabura yayi mai dauke da ajje wani gwauron numfashi idanuwansa fes kan likiti jikinsa yana rawa ya riko hannunsa.

"don Allah in har zaka yi furuci kayi wanda ba zai tafi da imanin zuciyata ba na rokeka".

yanayin da yake sakin furucin da kyar yasan ya jikin likita kara sanyi ya shiga gyada masa kai.
"ta haihu...".

shima ya fadi dakyar kamar wanda akayi wa dole idanuwansa na kan Malam Bello kamar yarda shi ma ya ke kallonsa zare hannunsa yayi saboda wani irin bugu da yaji ya kawo masa ziyara zuciya ya dubi Malam Bello.

"ina zuwa zan maka magana in an kammala gyara mata jiki sai ka zo ka ganta da baby ko".

ya karashe cikin sakin murmushin yaƙe bai jira amsawar Malam Bello ba ya ja jiki da sauri ya nufi dakin hutu da aka kai Habeeba ya tura ya shiga har yanzu dai jiya-i-yau da sauri ya isa gareta yana duban nurses da sukayi carko-carko da alamun yanayin da suka ganta ya tafi da yar guntuwar jarumtarta su hannunta ya kamo bayan ya dan rankwafa zuwa gareta hannun ya shiga juyawa yana mai kai dayan hannun nasa izuwa wuyanta yana taba alamun nemon motsin numfashi cak! ya tsaya kamar wanda aka cewa in yayi kwankwarar motsi ba zai ji sautin saukar numfashin nata ba gyada kai yake yi cikin raguwar faduwar gaba jin saitin kirjinta yana harbawa alamun da rai a jikinta har zuwa wannan lokaci ajje numfashi yayi mai karfi kafin ya miki ya shiga binciken ta sosai tsayin wani lokaci bayan ya kammala ya umurci Nurses akan su dauko masa kayan karin jini cikin sauri suka fice gami da daukowa ruwa ya fara sak mata gami da yin wasu allurai a cikin ruwan sannan ya juya inda ya juyo jaririn na kuka inda aka kwantar dashi kallonsa yayi sosai ɗa namiji ne fari tas dashi kyankyawa mai kama da uwarsa.

UKU BALA'I (Completed)Onde histórias criam vida. Descubra agora