UKU-BALA'I=18

630 30 0
                                    

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA GOMA SHA TAKWAS.

        In ka rike mani za na rike maka ribar zama yarda da juna. farin cikina zana sanar maka kai ka damu Dani
     --Usaini Danko

A hankali yake ajje komai na shi kan table din dake girke cikin kayataccen office din sa kallo daya zakayi masa ka gane hanzarin da yake yi cikin aikinsa gabadaya hankalin sa bai wajan abin da yake yi idanuwansa na wajan kofar office din ji yake yi ajikinsa akwai wanda zai shigo zuciyarsa tana sanar dashi hakan.

Bayan ya kammala komai a hankali ya fara takawa kan ƙafafuwansa don ji yake yi kamar abin da yake muradin gani kuma zuciyarsa na sanar dashi tabbatarsa kamar ba zai tabbata ba gareshi sosai yake ganin tafiyar lokaci wanda yake hango kurewa a cikin sa duk dakika daya gani yake yi kamar tafiyar awa daya ce.

Wajan sakatariyarsa ya dosa yana faman jan numfashi.

"Sir Morning".

Abin da ta fadi kenan bayan ta dago kanta jin alamun mutum kusa da ita.
Hannu ya daga mata alamun amsawa kafun ya shiga waige-waige na yan dakiku sannan ya sauke idanuwansa akanta yana mai nisawa.

"Areefa ta shigo aiki yau kuwa?".

Mamaki taf! A fuskarta take dubansa sosai take lura da canjin ogan nata tunda Areefa ta shigo cikin ma'aikatar nan gaɓadaya hankalinsa da natsuwarsa suka karkata akanta ba ta san mai hakan ke nufi ba...ko da dai bai kamata tayi mamaki ba domin ta san waye Dr.Erena tuni ta diga masa ayar tambaya katotuwa.

Kaɗa idanu tayi kafun ta motsa tika-tikan laɓɓanta wanda suka sha jan jambaki sai faman kyalli suke yi.

"gaskiya bana zaton ta shigo don ban ji duriyar ta ba yau sam!".

Ta karashe tana mai kafeshi da idanuwa sosai da sosai kai taga ya shiga girgizawa yana faman cizon laɓɓansa gami da haɗa hannayensa waje daya yana lankwasawa suna bada wani sauti mai zurfi.

A hankali ya fara taka kafafuwansa da sanyi a cikin su amma yarda yake tafiyar cikin hanzari bai bayyanar da haka din ba kofar fita daga sashi ya dosa yana faman hanzari cikin tafiyarsa cikin kankanin lokaci ya sauka daga benen zuwa tsakiyar cikin company din idanuwansa ya ware yana yawatawa cikin sashi da sashi na ko ina.

Ya jima cikin wannan yanayin kafun ya isa wajan daya daga cikin ma'aikatan da suke nan din ko wanne da bangaren sa kamar office.

"Mufeeda Please ko kin ga Areefa ta shigo yanzu?".

ya fadi har lokacin idanuwansa ba su tsaya waje daya ba.

Dago kanta tayi jikinta sanye da abaya kamar ko yaushe dubansa tayi da wani irin yanayi kafun ta kau da kanta sosai taji sunan da ya ambata ya shiga kuwwa cikin kwakwalwarta sosai take jin sunan yana haifar mata da wani irin yanayi mai girma gareta zuciyarta taji tana zaro mata wani lamari mai girma da ta daɗe da binne shi a filin zuciyar ta ta sunan Areefa take ji kamar a mafarki abubuwa da yawa take ji a ranta game da sunan.

UKU BALA'I (Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora