32=UKU-BALA'I

448 42 0
                                    

*******
Zuciyarta take ji tana yi mata nauyi, da abu mai girman gaske. komai take ji yana zama kamar tarihi gani take yi kamar ba ta kwashe wadannan

shekarun da suka bawa rayuwarta baya ba  wai ita ce yau ta gama makaranta  wai ita ce yau ake bikin kammala makarantar su, a matakin sakandire. gani komai take yi kamar ba gaske ba, gani takeyi tamkar mafarki ne take yin sa wanda a ko wani lokaci zata iya farkawa.

A hankali ta kai yan yatsunan Hannunta na dama zuwa bakinta tana cizawa, kamar zata zare su daga jikinta komai take ji yana tabbatuwa, komai take ji yana gasgatuwa, komai take ji yana zama zahiri ba badini ba.

runtse idanuwanta tayi tana mai buɗewa ta shiga yawatawa da idanunta zuwa harabar makarantar dalibai birjin kowa sai murna yake yi da farinciki fuskokin su dauke da tsananin farin ciki mara gushewa.

'Yaa Allah'.

Ta furta cikin wani irin yanayi mai girman gaske zuciyarta take ji tana buɗewa sosai tana haifar mata da wani lamari mai girman gaske

kwanyarta take ji ta shiga shawagi da ita cikin wata irin duniya na farinciki sosai take jin duk wata gaɓa ta jikinta tana ansa sakon da zuciya da ruhi suke miko musu na farin cikin da take ciki a yau din nan.

"Wayyo Allah na. Mariya gabadaya na gaji wallahi".

Muryar Baseera ce ta doki dodon kunnuwanta da sauri ta dago kai tana dubanta tana mai sakin yak'e gami da gyaɗa ma kai.

Kuri Baseera tayi mata da idanu kamar mai son gano wani abu daban a hankali ta shiga janye hannayenta data dafa kafadun Mariya idanuwan na kara yo waje da yanayi na damuwa ba bacin rai.

"Meye haka Mariya, me fuskarki ke kokarin nuna min ba dai zaki ce mani ba kya farin ciki da wannan ranar ba Yaa Allah!".

Ta karashe tana mai dafe kanta da take ji yana sara mata da wani irin yanayi mai girma da tashin hankali a cikinsa runtse idanu tayi kafun ta buɗe su kan Mariya da tayi shiru idanuwanta da wani yanayi na damuwa a ciki.

"Ban san me zan ce miki ba kuma Mariya, Shekaru fa tafiya suke yi kamar gudun ruwa a kogi ya kamata ace wannan shekarun da kika shafe kin canza komai a duniyarki, ki duba ki gani kin canza tsarin ki ya canza ke kan ki kin san komai game dake ya sauya sai dai abu daya...".

Tayi shiru tana jan numfashi mai dauke da damuwa mai girman gaske kau da kai tayi daga barin kallon Mariya ta juya kan dalibai dake ta fara'a da farin ciki.

"...Zuciyarki Mariya taki sauyawa, komai ya ki canzawa a cikinta kin ki baiwa rayuwarki damar kawo maki farin ciki a filin duniyarki Ban san mai ya sa ba?".

Sake kusantowa tayi gareta tana dafa kafadarta.

"ki na tunanin rayuwa zata yuwu a hakan kina tunanin wanan tsarin da ki daukar wa kan ki zai haifar miki da ɗa mai ido a rayuwarki ina! haka ba zai taba yuwuwa ba ya kamata ace kin sauya Mariya ki sauya rayuwarki!!!".

Ta karashe cikin murya mai amo da sauti tana rike kafadun ta tana girgizawa har sai da mafiya yawan dalibai suka dube su sosai.

Runtse idanu Mariya tayi tana mai toshe kunnuwanta da hannu bibbiyu lokaci guda idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir jikinta lokaci guda ya shiga rawa kamar wanda ruwa yayi mata duka sosai da sosai a hankali take duban Baseera da idanunta bakin ta na faman rawa kafin ta ciji laɓɓanta tana jin yarda zuciyarta ke matsewa a waje daya da girman damuwar da take ciki.

UKU BALA'I (Completed)Where stories live. Discover now