66=UKU-BALA'I

395 28 0
                                    

A hankali take tafiya kanta akasa ga wani zundumemen Hijabi da ta saka a jikinta har yana sharar kasa hannayenta cikin hijabin sai wasa da su take yi.

Kallo daya zaka yi mata ka gano yanayin rashin kwanciyar hankali a tattare da ita fuskarta tayi fari sosai ga wata rama da ta zabga kamar wacce tayi ciwon shekara guda.

Ratso layin take yi tana bin gefe mutane sai binta da kallo suke yi kamar sun ga watan ramadana sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗin wannan fitowar da tayi bata taba zaton zata tsani kanta ba sai a cikin wannan kwanakin da fita ma

gagararta take yi in kuwa ta fito an dinga zundenta kenan ana nuna ta da baki wasu har tararta suke suna gaya mata magana son ransu sai dai ba yarda zatayi ita ta jawo wa kanta.

Cikin wannan yanayin ba zato ba tsammani taji an janyo mata hijabi ta baya wata irin dokawa taji gabanta yayi zuciyarta harba da sauri ta dago kanta cikin wani irin yanayi na tsoro da firgici dubansa take yi tun daga kasa har sama bata san shi ba bata san daga ina yake ba.

"Ke ba kya ganin mutane ana yi maki magana kin yi banza da mutane iye wacece ke dan kan...".

Ya lailayo ashar ya dire gami da daga hannunsa daya yana kokari kife ta da mari mai ya gani kuma sai ya sauke yana mai da numfashi.

Sosai tsoro ya bayyana a fuskarta a hankali ta shiga ja da baya tana raɓashi zata wuce don ta lura dan iskan gari ne dan kwaya in ba don haka ba ai bai isa yayi mata wannan cin mutuncin ba ta kyaleshi da sai ta keta masa rashin mutunci amma

halin da take yanzu ba zata iya ba duk da zafi da raɗaɗin da zuciyarta ke yi akan zagin kare dangin da yayi mata.

Sake fizgo mata hijabin yayi ganin tana kokarin raɓashi ta wuce ya tsaya dab da ita har suna shakar numfashin juna ba abin da ke tashi a jikinsa sai warin solisho da sukuɗaye kau da kai tayi da sauri gami da toshe hanci wani yinkuri taji zuciyarta ta nayi tana kokarin yin amai.

Ganin abin da take yi masa yasanya shi duban fuskarta da take yatsine masa tana toshe hanci wata irin ashariya ya danna mata gami da cafko hijabin jikinta ya cikuikuye.

"Ke dan kan uban ki ni kike toshewa hanci to ubanki ne ke wari ba ni ba matsiyaciya karuwan banza da wofi".

Yana fadin haka ya fizge hibajin gabadaya daga jikinta daga ita sai zani da ves ga katon cikinta da ya fito sosai wanda haihuwarsa nan kurkusa runtse idanu tayi gami da toshe

kunnuwanta wani kuka ne ya zo mata da sauri ta durkushe tana mai sakin sa shi kuwa sai faman danna mata ashar yake yi.

Lokaci kankani mutanan layin duk suka taru aka rasa wanda zai zo ya kwace ta domin kuwa suna tsoron TANGA ba wanda bai sanshi ba a fadin garin nan tattarin dan jagaliya ne kashe mutum a wajansa ba komai bane yayi zaman gidan kaso yafi a lissafa a fitowa dashi.

"In kana yiwa Allah da Annabi ka bani hijabi na".

Ta fadi cikin muryar kuka jikinta sai rawa yake yi wani takaici take ji a zuciya ji take kamar ta hadiye zuciyar ta mace.

Cilli yayi da hijabin da sauri ta rarrafa za ta dauka ya danne mata yatsun hannu ta kurma uban ihu a daidai lokacin motar Dr.Karami ta sanyo kai ganin abin dake faruwa a layin ya sanya shi taka burki ya fito da sauri yana duban mutanan da sukayi cirko-cirko suna kallon rigimar Hafsat da Tanga da sauri ya isa wajan sam bai san wacece ba amma ganin irin cin zarafin da ake yi mata ya sanya shi zuwa ya hankaɗe tanga a daidai lokacin ita kuma Hafsat ta dago kai.

UKU BALA'I (Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora