65=UKU-BALA'I

414 33 0
                                    

Sosai ya kasa gane kansa komai yake jinsa yana sauya masa lokaci guda zuciyarsa yake ji tana harbawa da wani irin yanayi mai raɗaɗi a zuciya bai san yarda zai yi ba bai san abin da ya kamata yayi ba zuciyarsa ta cushe kwanyarsa sai hayaki take yi kamar zata kama da wuta duniyar gabadaya yake ji tana kai komo dashi jin sa yake kamar bashi ba kamar wani daban aka dauko aka ajje.

Numfashi yasake ja karo na ba a dadi yau kusan kwana uku kenan yana jinyar kansa kokari yake yi ya saita kansa amma hakan ya gagara zuciyarsa taki amanna akan abin da ake so yayi sosai yake jin GURBIN SO mai girma wanda ya baiwa Mariya ba zai iya barinsa ya so wata daban ba baya tunanin hakan zai iya

kasantuwa son Mariya ta zama komai nashi ita ce rayuwarsa dama numfashin sa baya tunanin rayuwarsa zata yi karko in har ba soyayyar Mariya bace tadawo gareshi sosai yake kallon kansa a matsayin GAWA DA RAI.

Hannayensa duka biyu ya dafe kansa da su yana faman jan numfashi mikewa yayi kan gadon yayi zaman dirshan gami da zabga tagumi

yawatawa ya shiga yi da idanuwansa komai gani yake yi yana sauya masa komai yake ganin baya burgesa a filin duniyar nan komai yake ji kamar ciwo ne a gareshi zuciyarsa yake ji tana matsewa da wani irin tashin hankali mai girman gaske ji yake yi ko wani sashi da lungu na zuciyarsa na kara yayyagewa da son Mariya kokari yake yi ko zai iya abun da ta bukata amma ji yake yi kamar kara rura wutar sonta ake yi a zuciyarsa.

A hankali ya zuro kafafuwansa zuwa kasa ya mike akan su jikinsa sanye da kayan barci farare masu dingo blue maballin gaban rigar ya gyara da ya fice ya zura silifas din dake yashe a kasa toilet ya nufa cikin rashin kwarin jiki da na zuciya.

Yana shiga ya sakarwa kansa shawa mai ruwan dumi sosai yake jin ruwan na ratse shi ta ko ina zuciyarsa dake zafi yake jin tana sauka kadan-kadan runtse idanuwansa yayi yana furta.

"Yaa Hayyu Yaa Kayyum".

Kusan minti ashirin ya shafe a toilet din kafun ya wanke bakinsa gami da dauro tawul a kugunsa da wani kuma a hannunsa yana tsane kansa da sajen fuskarsa da yake karawa fuskart asa kyau da kwarjini fitowa yayi ya tsaya gaban Mirrow yana kallon kansa sosai yake hango ramar da yayi shi kadai ya san wahalar da yake sha shi kadai ya san azabar da zuciyarsa take kawo masa gabadaya ya daina jin dadin

komai WALWALAR ZUCIYA gabadaya yanzu bai samunta har ya manta yaushe rabonsa ya jidadi da nishadi a duniyarsa.

Numfashi ya ja gami da juyawa ya nufi sif din dake manne da bangon dakin buɗewa yayi yana kallon ko wani sashi na cikin sa kaya ne makil a cikinsa a shirye hannu ya sa ya shiga dagawa yana kallo so yake yi ya zabi wanda zai saka amma gabadaya

kayan ma jin su yake yi wani iri ya jima a tsaye yana zarowa yana mai dawa ya rasa wanda zai dauko lokaci kankani duk ya yamotse sif din kafin ya zaro wani lallausar yaɗi light-blue mai dikon dark anyi masa dinkin zamani wanda ya fita sosai.

Bakin gado ya ajje su sannan ya juya ya koma wajan Mirrow din fuskarsa ya dan gyara sannan ya koma ya zura kayan a jikinsa wanda sukayi

matukar hawan sa sosai suka kara fidda masa da kyansa gami da kwarji agogon Rolex ya daura a hannunsa gami da kafa hularsa wacce ta hau kayan sosai takalmin kafarsa sau ciki baki sai daukar idanu yake yi glass ya saka a idanuwansa wanda ya kara sirrinta yanayin da yake ciki.

Key din motarsa ya dauka gami da wayoyin sa bayan ya feshe jikinsa da daɗaɗar turarurruka masu sanyin kamshi a hankali ya shiga taka kafafuwanta yanayin sa kadai zai nuna maka ba ya cikin nishadin zuciya saidai cikar halintarsa da mazatakarsa da ka kalla zaka gane namiji hadadde mai ansa sunan sa na mijin.

UKU BALA'I (Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora