Episode 1️⃣
‼️Abdulbaseet ‼️
Na : Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Check out on wattpad @bintnagsRuwan sama ake tafkawa kamar da bakin kwarya titin azman yayi tsit babu ko mota daya da take shigewa bare keke, sauri take kamar zata tashi sama duk da ruwan na dukan ta ama ta kwamace ta ci gaba da tafiya ko allah ya temake ta, ta sami abun hawa tana cikin tafiya, abun tun baya bata tsoro abun har ya fara bata tsoro chan ta fara jero yan adduoin ta da azkar dinta,su suka dauke mata hankali ta cigaba da tafiya.
Giffffffffffff kake ji mota tayi kanta kasan cewar motar a guje ta taho dan ko burki bana kyautata zaton yanayi a motar nan.... hummer jeep ce sabuwa dal da ita, gabaki daya baka gashi an zuge ta da gilashi baki da baka hango na ciki.
shiru kake ji har wajen minti biyar ba'a fito duba abun da aka kade ba sai chan kuma aka fito daga motar, wani dogon saurayi ne sanye yake da hoody da wando da pcap duka bakake sai 👟 👟 takalma sa kuma farare ya zuba uban bakin gilashi da ya cika masa fuska.
Ya karaso wajen da take, ya kali gabas da yamma kudu da arewa babu wanda yake gilmawa ta wajen sai uban ruwan saman da ke sauka a kansu.... cicibarta yayi ya sanya ta bayan motarsa kasan cewa a sume take saidai ba jini ko daya da yake fita daga jikin ta, sannan ya taka motar sa ya bar gurin.Kai tsaye bayero clinic ya kaita cikin hanzari suka karbe ta dan ganin irin yanayi da take ciki
Nan kallo ya koma kan sa dan yadda yake haka ya siga clinic din kamar wani shedan ya sha bakaken kaya daga samar har kasa gannin kallon yayi masa yawa yasa ya zari face mask ya saka a fuskar sa shima kuma baki....Nan likitan da zai duba ta ya karaso ya ke tambayar shi abun da ya faru? Sai da ya gama yan muzuran sa sanna ya amsa cikin dashashiyar murya sai kace wanda ya shekara bai yi magana ba
" a hanya na tsince ta a bakin titi da alama mota ce ta bige ta🙄" ya fada cikin harshe turanci.
Nan Likita ya dora masa allamun tambaya dan tunda ya shigo da ita shi bai yarda da shi ba da gani wannan mutumun ba kalau yake ba dan bai yi kama da wanda za'a yarda da shi ba....likitan ya ce masa gaskia idan yana so a duba ta sai ya kawo police report ko kuma ya dauke ta ya kaita general hospital inda zata sami cikakiyar kulawa inda kuma akwai kwararun likitoci.
Nurse ce ta shigo office din likitan da gudu har tana haki tace DR parient din da ya kawo tana convulsing (jijiga) tana bukatar kulawar gagawa a guje shi ma ya fita likitan suka shiga dakin da take.Cikin dan kankanin lokaci suka tsaida jijigar suka saka mata ruwa, likitan ya bawa nurses yan gwaje gwajen da Xrays din da za'ayi mata sannan ya koma.
Yana zaune inda yabar shi, chan wani tunani yazo wa likitan yace rayuwar wannan baiwar allahn yakamata na fara cetowa kafin na ji da wannan bawan allahn.
Yanda likita bai kula shi ba shima bai kula likitan ba har nurses suka shigo da sakamakon gwanjin da aka yo mata, likita ya kalla yace Alhmdulillah jin haka yayi sauri ya dago ya kalli likitan, sakamako yanuna normal kawai dai zafin buguwa ne ya sa mata cerebral contusions, mun bata magun guna da karin ruwa da za'ayi mata zata farfado akowane lokaci daga yanzu, ga wannan kaje ka biya bill.
Har cikin zuciyar sa ya ji dadin jin ba wani babban abu ne ya same ta ba hakan yasa yace Thank you Dr ya dauki takardun ya fice.
Bayan yaje ya biya kudin sannan ya koma dakin da aka kwantar da ita
Sai a lokacin ya kalli fiskar ta dan ko da ya dako ta bai kalli fuskar ta ba............farace tassss dan duk inda ake irga fararen mutane to za'a sako ta a ciki, kasan cewar kanta ba dankwali hakan yasa gashin ta duk ya zubo kan fuskar ta da wuyan ta ya rufe hakan yasa bai wani tantance ta ba, gannin kafafunta santala santala a waje yasa ya ja mata zanin ta zuwa kasa.... wani abun hannu da ya makala a hannun sa mai kararawa ya dan buga kasancewar yayi motsi da hannun wajen rufe mata kafa, a hankali ta bude idon ta tana neman inda ta jiyo sautin, babu abun da idon ta yakai ga gannin sai hannun sa mai awarwaron kararawa, daga ido tayi taga fuskar sa amma fusar a rufe yasha baki kamar kidnapper hakan ya bata tsoro da sauri ta rufe ido ta fara jero addu'oin tsari.
Ji tayi ya dau wayar ta da aka ajiye mata a gefen gadon ya hau latsawa ,Message yayi composing ya duba contacts dinta ya nemo mama ko mommy ama duk bai gani ba, chan yaga ansa yaya Ado, nan ya tuno kalamar yaya da abun da take nufi hakan yasa ya tura wa yaya ado message din sannan ya ajiye mata wayar dadai kanta sannan ya fice, ta bude ido a hankali ta bi bayansa da kallo.Lafiyar wannan mutun kuwa toh meye hakan anya kuwa wannan dan musulmi ne???? Wannan tambayoyin tai ta jera wa kanta har taji shigowar yan gidan su dakin.....
Umman ta ce da yaya Ado suka shigo dakin tare da likita nan likitan ya kwashe labarin abin da ya faru daga zuwan su asibitin har yanzu ya kuma zari dubi dari cash yace wannan ne kudin da ya bayar kafin ya tafi....To me zasu ce ??
Godiya ko me zasu yi wa wannan bawan allahn??????
To be continued on Sunday insha allah *****************************************************
Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼
Bintnagz
Abdulbaseet will be online every Saturday and Sunday
YOU ARE READING
𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓
RomanceSalama, You are the first person on earth that my heart has truly shaken for. I never imagined something like this would happen to me in my life; I thought I would live a single life just like my father, Mr. Glassman. I never thought girls could be...