4️⃣3️⃣

442 38 1
                                    

Episode 4️⃣. 3️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad************************************

Yana tsaye bakin kofa yaya ado ya bude koda, Abdulbaseet yayi masa smiling ba shiri shima yaya ado ya mayar masa...
Ango ango!!!Abdulbaseet ya fada
Yaya ado yayi dariya yace
why are you late?
Amarya tayi fushi?
Am so sorry na tsaya wajen karatu ne ya kali agogo yace not that late actually
Sukayi dariya suka shiga ciki
Suna shiga yaga yayanin wani iri idanun mutane akan shi nabeel yayi tsuru kamar tsohuwar mage....
Yeah Ya juya kalli yaya ado alamun wadan nan fah???
Kafin yaya ado yayi magana
Ina har farooq ya taso yayi hugging 🤗 din Abdulbaseet
Glad to see you brother, its soo nice seeing you again
Alhmdulillah ya fada tare da dukan bayan abdulbaseet.
Ido kawai ya ware yana binsu da kallo, dukan su suka mike baki daya kowane da fara'a a fuskar shi banda nabeel da Abdulbaseet da suke a rude.
Hawaye suka zo idon alhaji sunusi yayi saurin sharewa dan yaga fuskar kanwar sa a fiskar Abdulbaseet.
Have a seat my son!!
Alhaji Sunusi ya fada, hakan ya kara rikitar da tunanin Abdulbaseet...
Yaya ado ya kama hannun sa ya zaunar da shi duk suka zauna, faridah ta shiga jido kayan abinci tana kawo wa tana ajiyewa, dan yau mai special ce....
Abdulbaseet dai sai yan muzurai suke yi shi da nabeel da magana ta ido da su kansu basa gane mai suke cewa.
Sai da suka chi suka sha sannan alhaji sunusi yayi gyaran murya yace da Abdulbaseet ya dawo kusa da shi ya zauna.
Jiki a sanyaye ya taso yazo ya zauna kusa dashi.
Abdulbaseet ka saki jikin ka nima a matsayin mahaifin ka nake, ni yayan mahaifiyar kane Abdulbaseet, halimatu kanwata ce ciki daya muka fito ni da ita, waddanan kuma yaya nane cousins dinka ne, faridah ya tace, farooq ma dana ne.

Mommy aziza ta kalle shi tace Abdulbaseet ka saki jikin ka, muna samun labarin ka muka doko kafa domin zuwa mu ganka, tun kana yaro daddyn ka neman ka domin kuwa har kasar engila yaje neman ka ama bai same ka ba, munyi cigiya da begen ka har mun sare da kai yaro.

Hawaye suka zo mata, faridah tayi saurin cewa haba mommy kar ki samu kuka muma.
Abdulbaseet da yake binsu da kallo daya bayan daya yadan lumfasa ya kalli nabeel da shima mamaki ya rufe shi.
Gani yake kamar hadin bakin ne abun dan bai ce komai ba.

Abdulbaseet we are sorry for not been there for you in life, bawai bama sanka bane ba, bawai damu da kai bane ba, a'ah dangin baban ka sun nuna fin karfi a gare mu, sun nuna mana cewa sunfimu karfi a wajen ka .
Bamu taba zata bature zai aikata abun da ya akata ba Abdulbaseet, bamuji dadin abun da yayi ba ko kadan.

Ji yayi abun da yake fada ya kasa samun waje a zuciyar Abdulbaseet, kalaman sa yana masa yana yi dana gwaggo, ya yarda da abun da gwaggo ta fada masa gashi yanzu yayi nadama, yayi karatun ta nutsu baza'a kara kaishi a baro shi ba.

Mikewa kawai yayi tare da duba agogon sa daya saura, ya kali nabeel yace, nabeel muje ko, lokacin sallah na gabatowa.

Ido kawai suka bishi da shi, nabeel dai da yayi mutuwa zaune yadan kifta masa ido alamun ya zauna ama ina har ya yi hanyar kofa, su kuma duk suka bishi da kallo,
Farida ce ta bishi tana haba Yaya Abdulbaseet, dan allah kar kayi haka, think about this again, they came all the way from maiguri just for you, they saw u and recognised you from the very first look on our wedding photo album,
Ya juyo ya bata wani uban kallo na hold your shit to your self baya bukatar jin komai daga gareta, hakan yasa itama tayi shiru ta bashi hanya kawai ya wuce, yana fita nabeel ya brishi a baya yana basu hakuri.

Suna fita sukaci karo a kan bene dan jiyayi kamar kafafun sa bazasu dauke shi ba,
Nabeel ya tsaya yana kallon shi, jin takun nabeel yasa ya juya yana kallon shi.
Nabeel are you behind all this ????
Wane irin magana ne wannan kaman ya behind this, kana kallo fa nima samu na kayi cikin wannan situation din, Ado was behind it dama nasan da wata a kasa tunda naga yace muje gidan shi kuma ni da kai nasan tabas there must be something.

Suna cikin wannan sukaji yaya ado ya sako daga sama shima da gudu...
Nabeel!!!!!nabeel!!!!!Abdulbaseet !!!!ya fada yana kwala musu kira, yaci karo da su ya tsaya yana haki yace
Abdulbaseet pls and please think about this kada kayi regretting anjima, i knw how it feels Abdulbaseet ama please attend to your uncle don't let him down please, you need somebody to support you in life, you need somebody to be your leaning shoulder, kyauta ce allah ya baka Abdulbaseet kada ka banzatar da wannan kyauta da allah ya baka.
"Exactly"nabeel ya fada.....

This is a great opportunity this is your reward my friend accept this and Allah shall reward you more go in and have there blessings, they are your true family, nasan abun da kake tsoro ama ba duka aka taru aka zama daya ba, people are different and baka san inda zaka samu na allah ba.
Hawaye suka ci karfin Abdulbaseet ya tsuguna a bene yaci kukan shi mai isar shi,
Nabeel da yaya ado na lalashin shi har ya hakura ya tashi suka koma ciki...
Yana komawa ya tada sun yi jungun jungu suna jiran tsamani, alhaji sunusi na ganin shigowar shi ta tashi yayi hugging dinshi yana well done my son, yana bashi hakuri
Before you knw it har an zama family, suka zo sukayi jam'i suka gabatar da sallar azahar sannan faridah da yaya ado suka shiga kitchen....
Nan suka zauna suka tatauna, Abdulbaseet ya kwashe labarin abun da ke faruwa ya fada wa alhaji sunusi tun daga farkon dawowar sa har yau. Duk da baiso ya tona wa ubansa asiri ba gannin nabeel yasan koda yayi karya sai ya ce ba haka akayi ba dan yama fishi jin haushin iyayen sa.

*****************************************************

Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************

Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)

Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼

𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓Where stories live. Discover now