3️⃣9️⃣

515 43 4
                                    

Episode 3️⃣9️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad************************************

Latest shaddar da ake yayi mai shegen tsada ne a jikin blue da covered shoe dinshi ya karkata hula, smiling salama tayi tare da fadin nabeel, kafin ta ta fadi abun da zata fada shima dayan ya bude kofa ya zuro kai , shima sanye yake da gezna ash sai kyali yake da sheki kamar wani sabon ango shima ya karkata hula ga kuma takalmi
Wani smiling suka sakar ma junan su tun da yake a duniya bai taba ganin salama da irin wannan kyau haka ba, ita kuwa kullun Abdulbaseet yayi shiga ko wace iri ce daukar idon ta take yi.
Coincidentally silver kaya tasa itama da sukayi yanayi da kayan shi.
silver material less ne a jikinta wanda akayi mata prom gown da shi sai turban da ta nada a kanta shima silver purse din hannun ta da kuma takalmin ta komai mata silver, kar kuce silver din yayi yawa kar ku manta salama farar mace ce shi yasa batayi sirki da komai ba.
My queen ya fada cikin murya kasa kasa daidai kunnen ta da ya matso kusa da ita, ta dago tadan yi masa hararar kauna sai kuma tayi Murmushi ta kali agogon hannun ta tace lets go we are already late....
Baya zasu shiga ita da sabeeha,nabeel yayi saurin cewa, baiwar allah ai da mai gurin ke ga gurin ki nan ya nuna mata front seat, murmushi kawai sukayi tare
Abdulbaseet ya bude ma salama back seat suka shiga suka zauna, nabeel da sabeeha kuma suka shiga front seat.
Nabeel ya tashi mota suka ware....
Satar kallon juna kawai suke yi,
Salama ta dago tace
How far? Why are u giving me dat look?
you look amazing...
Wat is bride called in hausa, tayi dariya tace amarya
Yace you just look like amarya
Tayi dariya tace well you are trying,
Abdulbaseet yayi dariya yace nabeel tell her how i have improved in hausa please, nabeel yayi murmushi yace
Salama ai mutumin ki sa shi a gaba nayi nace na dena jin turanci, so atleast he is improving yanxu idai zaiyi magana sai yasa hausa koda kadan ne....
Thats soo nice of you nabeel
Shi kuwa an fasa masa kai sai wani jin kanshi yake.
Haka dai sukayi ta magana kasa kasa shi da ita har suka karasa wajen....

Waje ya kwashi jama'a sai kidiy ake ana chashewa , wannan ne karo na farko da Abdulbaseet ya je biki tunda yazo Nigeria
Abun ya bashi sha'awa kwarai da gske, kallo ya koma kansu dan sun so sufi amarya da ango yin kyau
Tunda yaya ado ya hango su tare ya ke binsu da harara. Duk duk inda salama ta yi Abdulbaseet na bita a baya har sai da nabeel ya janyo shi yace ya saurara mata mana ya barta, baiga cikin murane suke ba.
Nan dai suka karasa gurin yaya ado sukayi masa alasa alheri suka dauka hotuna, sannan suka sami table suka zauna, bayan su salama sun gama attending wa mutane da suka gayata suka koma table din da su Abdulbaseet suka zauna suka ci abinci tare.
Yaya ado yayi ma salama sign taje ta same shi, ya rada mata am telling you this, yaron nan ya dena binki this is the last time am warning you 😡
Smiling tayi kawai dan taga faridah amarya  na kallon su bata ce komai ba kawai tabar gurin, dam bata so ta fuskanci wani abun.

Anci ansha a bikin yaya ado da amaryar sa faridah, ranar lahadi aka dako amarya aka kawo ta garin kano wajen dangin ango aka aka dan yi karamar wala anan gidam su ango daga bisani kuma aka dauki amarya aka tafi da ita wajen angonta dake garin kaduna.
Ranar kai amarya ma kuwa salama tayi tayi Bodado ta barta ta taje kai amarya ama Bodado taki saboda yaya ado yace mata kar ta sake ta bar salama ta tafi kaduna.
Ba yanda ta iya haka ta hakura ta zauna agida.
*****************************************************
Idan muka hada lokacin waje daya yau shekara daya kenan chir da kuluwar soyayyar Abdulbaseet da kuma abar kaunarsa salama
Cikin shekara daya kar kaso kaji yanda Abdulbaseet ya karu sossai da addinin musulunci, shi da kanshi yanzu idan yaga mutun yana abu zaice babu kyau haramun ne, kuma allah yayi hani ga hakan, karatu kuwa yanzu izun shi ashirin da biyar a Alqurani, ga kuma sauran littatafai da ya sauke, salah kuwa babu wada take wuce shi, ko mai yake yi ana kiran sallah zai mike ya je ya gaishe da ubangijin shi.
Lalle adinin allah da fadin allah gaskia ne, allah yayi mana hikima da baiwa kala kala ya kuma saukaka mana abubuwa da yawa ya kuma sa mana waraka ta hanyar bauta masa domin kuwa duk wannan bakin ran da jin kan shi da kuma  rashin kaunar mutanen shi duk sun rage domin kuwa yanzu yana hurda da mutane sosai, duk da ba wani hurda ba kawai dai gaisawa da mutane, duk sanda zai je masalaci zai gaisa da mutane, yayin dawo warshi ma zai gaisa da mutane, hakan yasa yanzu mutane sun fara sanin shi da dama, domin kuwa yana girma ma mutane sosai.
Soyayya kuwa ba'a maganar ta domin kuwa duk da basa ganin junan su shi da salama hakan nai hana su yin waya ba a kowace rana, duk wani activities dinshi ta sani shima kuma ya san nata activities din domin kuwa har timetable dinta na makaranta ya sani.

Duk da rigimar da zata zo nan gaba idan zancen auren su ya bayana, hakan bai sa sunyi kasa a gwiwa ba dan ganin sun farantawa junan su ba, sun kuma dauki junan su da mahimmanci ba. Giving up baya cikin lissafin wadan nan masoyan saboda wen ever there is way toh tabass there is hope inji malan bature.
Zancen hausa kuwa yanzu saidai muce masha allah Alhmdulillahi domin kuwa duk abin da zaki fada wa Abdulbaseet zai ji ki zai kuma fahimci abin da kike fada idan har babu karin magana da kuma hausa data dan lanqwashe, shima kuma zai yi trying yayi replying dinki back do ba dede bane saidai idan yayi sai a gyara masa.

Ta bangaren nabeel kuwa tun randa ya dora ido akan sabeeha yaji shima duniyar soyayyar sa ta sauya baki daya, duk da akwai yarinyar da yake so ita ma kuma akwai wanda take son ta. Tun da salama ta zo mata da zancen nabeel da kuma kudirin sa tayi watsi da cousin dinta, da yake ita sabeeha burin ta a duniya ta auri mai kyau , dan kuwa salama har tsokanar ta take yi da allah ya nuna mata mijin ta dan irinsu ne ke karewa da auren mazaje munana.
Soyayyar su zamu iya kiranta love at first sight domin kuwa tun da suka hadu wajen bikin yaya ado suka tsunduma cikin zuciyoyin juna.
Gashi abun na ta tafiya gwanin ban sha'awa.
Dan yanzu har competition suke yi Abdulbaseet yace sai ya ruga nabeel yin aure shima nabeel yace sai ya ruga shi yin aure.

Kunji fa....
Toh a ganin ku wazai ruga wani yin auren
Sai ku biyo ni domin jin yada zata kaya.....

*****************************************************

Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************

Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)

Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼

𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓Where stories live. Discover now