2️⃣4️⃣

592 43 10
                                    

               Episode 2️⃣4️⃣
            ‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad*************************************

Yaya ado ya gani tare da ita da kuma wata yar farar datijuwa da dukanin alamu mahaifiyar suce , nabeel dai kawai sakin baki yayi yana kallon Abdulbaseet da yani ya kidime daga ganin salama, haka har suka zo suka wuce suka shiga mota fuskar salama cike da farinciki da kuma annasuwa, ta kara kyau gwanin ban sha'awa
Har tazo ta shige Abdulbaseet kamar wani gunki ya kasa tabuka komaiii sai da nabeel ya bugo shi sannan ya samu ya zauna har yanxu baki a bude.

Ohh boy close the mouth mana, who is she
Is she your first love.......??
Rufe bakin yayi yayi, yayi ajiyar zuciya sannan yace.....
I have to gooo nabeel.....
Mukulin mota ya zara ya bi bayan motar tasu a guje .....
A wani estate suka sauka suka, sai da taga shigar su sannan ya koma cikin mota ya zauna ya sauke ajiyar zuciya.....
Wannan wane irin yanayi ne yake ji game da salama da yake wahalar da shi da shi kanshi bai san yana yi ba, yana cikin tuna nin nan ne ya jiyo bude balcony dinta ta sama ta fito tana tsaye tana waya sai faman dariya take da alama tana jin dadin yanayin da kuma hirar da take yi.
Gilas din window dinsa yaja kasa yana na kalanta, wani kwanciyar hankalin da sanyi suka ziyarci zuciyar sa, yayi murmushi yadan girgiza kai tare da fadin sunnan ta😁
Ji yayi kuma wata zuciyar na tuhumar sa da wa take waya haka, ji yayi kamar yayi tsuntuwa ya je inda take, horn yake da shirin yi mata ama ina kafin yayi har ta shige ciki.
Takaici kamar ya kashe shi haka yayi ta jira ama shiru bata sake fitowa ba har dare ya fara yi hakan yasa ya koma hotel,
Nabeel na lobby yana jiran dawowar sa.... yana ganin sa suka dunguma zuwa ciki.

Kwanciya yazo yi nabeel ya figi shi tare da mai ihu
Who the hell do u think you are mike
Do you think i will be following u like this begging you to tell me what's wrong with u
Ok fine this will be the last time i will be following u around like this, hold ur stories and this is my way out ......
Gogan naku kuwa ko dagowa ya kalle shi bai yi ba shi abun da ke damu shi abun da yake gabanshi duk sun fiye masa wannan hargagin na nabeel, gyara kwanciyar sa yayi kawai ya kashe fitila ya shiga tunanin burin rayuwar sa wato Salama.

Da yake yau asabar da Abdulbaseet ya tashi kai tsaye gidan nabeel yayi, ya tarar da shi a garage yana shirin fitowa da motar sa yayi masa horn ya juyo ya kalle shi harda zai dauke masa kai sai kuma ya karaso inda yake yana tambayar shi....
Kafin yayi masa magana har Abdulbaseet yace
To where bross???
I have some business to take care of....
Lets go then.....
To where i taught u dnt want me in ur life and why are u trying to be in mine....
Nabeel now, let it go,i was a bit off yesterday but am sorry....
Nan dai Abdulbaseet yayi ta lalabashi harsai da ya sako sannan ya shiga motar Abdulbaseet suka fita.

A hanya nabeel yake cemasa akawi Friend dinshi da yake aiki under company dinsu da maman shi da sister dinshi suka zo daga kano yana so yaje ya gansu dan da yanma zasu tafi so yana so yaje su gaisa kafin su tafi suna dikko estate.

Sai da suka tsaya suka yi musu dan shopping sannan suka tafi chan. Suna isa gaban Abdulbaseet ya fadi tabas nan ne estate din da yaga salama a ciki.
Kardai Yaya Ado ne friend din nabeel 🙆🏻‍♂️
Zuciyar sa ce ta fara dukan goma goma. Har nabeel yaso ya gano shi sai kuma dai ya wayan ce. Haka sukayi parking suka haura sama, suna kwankwasa wa Salama ta bude
Wani gumi ne ya keto wa Abdulbaseet yayin da sukayi ido hudu shida salama.
Wani kallo suka sakar wa juna da sukai sakam 60 sunayi har sai da nabeel ya gane ya zunguro shi tare da fadin hey mike Sannan ya dawo hayacin sa har yana firgita..... hanya ta basu suka shiga suka zauna ko wanen su da abunda zuciyar sa take saka masa.
Ta shiga daki ta kira umman su dai dai lokacin da yaya ado ya fito daga nasa dakin.....
Wa zai ganin Abdulbaseet!!!!
Suna hada ido Abdulbaseet yayi saurin sunkuyar da kai kasa ji yayi kamar ana sukarsa na ba gaira babu dalili......
Nan suka gaisa yaya ado yayi introducing dinsu ama bai nuna yasan Abdulbaseet ba kwata kwata. Har umman su take tsokanar nabeel dayake shi ma bature ne yayi zaman turai shi yasa yake da aboki bature to yadai daure ya koyawa abokinsa hausa koda gaisuwa ce, haka dai sukai ta hira har da dariya. Sai dai gogan naku hankalin sa na kan salama dan tunda ta shiga daki idon sa na kan dakin ko kiftawa bayayi...
Chan ya dau excuse yace bara ya fita kamar bai rufe motarsa da kyau ba bara yaje ya gani.

Yana fita ya dan zauna kan motar tashi idonshi kan window din dakin da take ciki, akan idon shi ta zuge labulen windon ta zuro kanta.....
Wani smiling ya sakar mata da ita kanta saida taji kunya ya yi smiling ita ma tare da sunkuyar da kai.
Waving yayi mata da itama bata san sanda tayi waving dinshi back ba.
Hannun yayi mata ma'ana ta sako....
Girgiza masa kai tayi tare da dan yin smiling
Ya dan yi mata alamun tausayi hakan yasa ba shiri ta sako a guje ta dayar kofar......
Yanda ta taho a guje shima haka ya tafi a guje har tana shirin yin tuntube hakan yasa yayi saurin yin hugging dinta...........  🤗

****************************************************
Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************

Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)

Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼

𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora