Episode 4️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Check out on wattpad @bintnagsHakikanin gskia wannan shine wanda salama ke nema......
jiki a sanyaye ta gyara tsayuwarta, bata ma karasa siyan abun da zata siya ba taji ita gida kawai take son tafiya hakan yasa ta dau kayan taje counter wajen biyan kudi, Dubu 6700 haka aka buga mata lissafin ta, ta sa hannun tana lalubar kudi amma bata jiyo suba, nan da nan wani gumi ya keto wa salama da tayi saurin sharewa, ta bude wallet dinta ta zazage jakarta ama shiru babu ko sisi inba naira 10 da mai adedeta sahu ya bata ba dazu.
Inallilahi ta fada a fili nan abun kallo ya koma kanta ta rasa inda zata sa kanta, ga kaya ta jido a hakan ma bata gama siyaya ba yanzu ya zatayi da wannan abun kunyar.
Ganin yarda mutane suka bita da kallo ya janyo hankalin Abdulbaseet yaji yana son sanin mai ke faruwa duk da ba shiga sabgar mutane yake yi ba balle ayi dashi.
Sai yanzu ya kallli face dinta dan ko dazu daya tare mata kaya bai kalli fuskarta ba, kallo daya yayi mata ya gane halin da take ciki, kawai ji yayi kafafunsa sun dauke shi sun kaishi inda take ba tare da amincewar sa ba hannun sa yasa a aljihu ya zaro ATM CARD ya bawa cashier din bakinsa kuma ya furta cire kudin ka cikin dashashiyar muryarshi sai kace wanda ya shekara bai yi magana ba nan ma cikin harshen turanci, shi a zaton sa duka ba niyya yayi ba kafarsa da hannun sa ne sukayi.Kallo ta bishi da shi kawai dan bata ma san mai zata ce ba, yana tsaye gefen ta sai satar kallon sa take yi shi kuwa bai ma san tana yiba, bakinta kuwa yayai nauyi kamar an dinke shi ta kasa furta komai bare kalmar godiya.
suna tsaye har cashier din ya gama ya miko masa card dinsa ya karba ya zura a aljihu batare da ya dako abun da yazo siya ba ya fito.Ko da tafito tunanin yanda zatayi ta koma gida take tayi tana tafiya tana tsara yarda zatayi har ta yanke shawarar zata tsare dan sahu idan yaso idan taje gida ta shiga ta dako masa kudin.....
Horn din mota taji akan ta da har ya gigitata tayi saurin tsayawa, motar da ta kade ta tabass ita ce wannan hummer baka tabasss ita ce wannan, gaban ta ya soma bugawa tara tara cak ta tsaya, me zatayi gudu ko neman temako? A dabure take dan harga allah a tsorace take , full light 💡 din da ya sakar mata ya kara razana ta, ido ta rufe tana shirin yin ihun neman temako 🙆🏽♀️ taji yace
"Do you have money for taxi?" "I thought u lost ur card and money" jin murya ta daban yasa tayi saurin bude ido dan ganin wanda ke magana, ga mamakin ta shi din dai ta gani ya zuro kansa ta window yana kallon ta.Tooooohhhhh inji mai tallar totuwa
Nan bugun zuciyarta ya karu zuwa goma goma da sauri ta girgiza masa kai, tama rasa mai zata ce masa, ashe ba bahaushe bane ta fada cikin ranta, sai kuma chan tace
I....... ha......ve cikin rawar baki kana kallonta kasan a tsorace take dashi..... bai jira jin mai zata ce ba ya figi motarsa yayi gaba ya barta a wajen a tsaye ta bi bayan motar da kallo cin mamaki.Ohhh ni salama yau naga ikon allah ta fada a filli tare da sauke ajiyar zuciya......................
Wannan shine karo na farko da Abdulbaseet ya taba yiwa wata ya mace magana tun da ya dawo Nigeria 🇳🇬 bai taba sha'awar kulawa ba ma balantana a yana shi, wani ikon allah kuma shi kanshi sai da ya bawa kansa mamakin kulata da yayi dan mata basa burge shi ko kadan hasalima gani yake duk mata kazamai ne. Tun da allah ya hallici Abdulbaseet bai taba kulla wata ya mace a matsayin budurwa ba ko kawa ba, balantana wata lalata da alfasha tazo kansa ba, babu wanda ya yarda da shi a duniya daga iyayen sa har abokansa duk da ba ma abokai ne da shi ba , mutun daya a duniya Abdulbaseet yake sakin jiki yayi wa magana ta tsawon minti biyar wato kanwar sa Hajar dan ko naima ma ba shiri suke yi ba. Shi a ganin sa magana ma laifi ce shi yasa ya kwanmace kada yayi idan ma yayi toh haka zata fito a dakushe alamun ba niya, idan kuma yaga dama sai kaji ya saki baki yayi magana irinta mutane ya saki zazakar muryar sa.
Abu daya zamu rika mu yabi Abdulbaseet da shi shine taimako, duk inda yaga mutun na bukatar temako musan man idan dai na kasa da shine to Abdulbaseet bazai yi kasa a gwiwa ba dan gannin ya temaka maka, ko da niya kuwa ko ba niya kuwa sai ya temaka dan bazai iya gani ya share ba.
****************************************************
To masu karatu a nan zamu tsaya wannan satin
Ku biyo mu sati mai zuwa domin jin yada zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama
Shin wane ne Abdulbaseet???
Mai muku fatan alheri akoda yaushe
BINTNAGZ
Make sure to vote 🗳
Comment and like
Much love and stay blessed 🙏🏼
YOU ARE READING
𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓
RomanceSalama, You are the first person on earth that my heart has truly shaken for. I never imagined something like this would happen to me in my life; I thought I would live a single life just like my father, Mr. Glassman. I never thought girls could be...