Episode 5️⃣0️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad************************************Yaya ado ya saukar da ajiyar zuciya, yace umma mai yasa bakya son yaron nan, meyasa kike ganin kamar ba tsaran ta bane???
Dannan kasan wani abu ne dangane da wannan yaron....?
Yaron nan fah ba girman nan bane balantana ka yabe shi....?
Gidan su yaron nan su kansu basu san wani abu ba game da wannan yaron...?
Ina kyautata zato yaron nan shi ya gudibda salama ama kasancewar tana sonshi hakan yasa ta boye mana hakan....??
Umma.....
Nima na dade ina kin Abdulbaseet a cikin zuciyata, bana son yaron ko kadan bana son kasancewar sa da salama, ama umma nayi da nasanin wannan karanta da nayi masa, domin kuwa Abdulbaseet mutun ne wanda zai rike amana...
Umma ban dade da sanin Abdulbaseet dan uwan farida bane, nan ya kwashe labari gabaki daya suka zayana wa Bodado abun da ya sani dangane da Abdulbaseet.
Umma bawai dan wani abu ba, bawai dan Abdulbaseet dan uwan matata bane, umma ki bawa Abdulbaseet dama su daidaita shida salama, salama zata temaka masa wajen warware masa sauran damuwar sa, shima kuma yana son salama, so mai tsanani, raba su bazai yi amfani a gare mu ba, domin kuwa ina gani salama da Abdulbaseet hadi ne daga sama.
Bodado ta sauke ajiyar zuciya cike da tausayin bawan allahn, toh dannan allah yasa hakan shi yafi zama alheri allah kasa su rike juna amana, allah kasa kada ya bamu kunya,
Wayar yaya ado ce tayi ringing yayi saurin sa hannu a aljihu ya zaro wayar....
Nabeel ne, yayi saurin daukar wayar dan ya zata zance office me, ashe zance rasuwar gwaggo ne...
Inallilahi waina ilaihi rajiun ya maimaita toh ina kano dama sai ka karaso...
Yana kashe wayar yace, kakar abdulbaseet ce allah yayi mata rasu jiya.....
Allahu akbar kabiran allah sarki, wannan tsohuwa dai da muka hadu da ita wanshe kare...allah ya jikanta ya gafarta mata allah kasa ta huta....Nan yaya ado ya kira salama ya sanar mata da zancen rasuwar, ya fita inda zasu hadu da nabeel suje jana'iza....
Yanda kasan ance Bodado ta mutu haka ta dunga rusa kuka, dan bata san yanda akai ba ga number din Abdulbaseet tana ta kira ama a kashe, kadai gwaggo ta tafi ba tare da ta roki gafarar Abdulbaseet ba, kar dai ya tafi basu hadu ba... wannan shine damuwar ta...
*********************************************************************************************************
Sai da aka yi uku sannan Abdulbaseet ya kuna wayar sa kasancewar bai dako komai ba, ga chajin wayar sa ya mutu, ga jama'a duk wanda yazo sai ya tambayi Abdulbaseet ai sunji ya dawo, ashe kafin gwaggo ta rasu duk sai da tabi dangi ta sanar da su ai jikanta ya dawo daga karatu....ji yayi duniyar gidan duk ta chanja, kamar ba shi ba yanda mutane suke nan nan da shi, kamar wani sabon mutun, kamar ba Abdulbaseet din da ake kyama ba kwanakin baya, shi da Engineer idan suka zauna karbar gaisuwa basa tashi sai dai idan za'ayi sallah, ama suna zaune....Koda su nabeel suka zo, Abdulbaseet yayi introducing dinshu ga Engineer, Engineer kamar ya maida su ciki yayi farin ciki yayi murna da ganin su dan su suka yi ma dansa jagoran ci gaba da rayuwa, sun kuma temaka masa, yazama dole yayi alfari da su....
Dan shi kanshi Abdulbaseet sai da yayi mamakin hakan...A daren ranar ya samu yayi waya da abar kaunar sa, tayi masa gaisuwa, ya kuma sanar da ita duk abun da ya faru, taji dadi sosai dan kuwa Abdulbaseet yayi abun da ta dade tana burin taga ya faru, yau ga Abdulbaseet a gida cikin dangi da bokan arzuki suna karbar gaisuwar kakarsa, masha allah, allah shine abun ambato....
Ji tayi duk wani nayi da take tatare da shi yayi sauki, domin kuwa sun fara cin ma burin su abun da suka dade suna mafarki....
Ranar da su yaya ado suka dawo sadakar bakwai, ya biya ta gida yace da bodado dan allah ta bashi aron salama domin kuwa, an samu karuwa faridah na da ciki, saboda haka yana so salama taje tunda hutu suke yi yanzu ta dan taya farida zama da kuma yan aikace aikace kafin a koma makaranta....
Duk da Bodado zatayi kewar salama ama haka ta yarda ta amince tace toh su tafi, salama ta hada kayan ta suka tafi garin kaduna.
*****************************************************
Bayan sati biyu mutane sun rage zuwa gaisuwa, Abdulbaseet ya sami hadiza da kuma Engineer a baban pallor ya sanar da su zai koma kaduna....
Nan Engineer yake cemasa yayi hakuri ya bari sai jibi domin kuwa alhaji sunusi yayan mahaifiyar sa yace zasu sami shigowa garin kano gobe, saboda haka ya bari sai sun zo sai ya tafi shima.
Haka ya ce toh ba damuwa allah ya kaimu goben....
Tsawon sati biyun da Abdulbaseet yayi a gidan su ji yayi kamar a wani waje yake na daban dan shi kanshi jin kanshi yake yi tamkar ba shi ba, abu daya yake missing shine hajar da bata nan, hadiza ita da kanta take zuba masa abinci, idan bai zo ya dauki abinci ba sai tayi masa intercom yazo an gama abinci, kada ya zauna da yunwa, idan taga yana damuwa ita da kanta zata ce masa ya dena kada ya jawa kansa wani ciwon... shidai kawai saidai ya bita da kallo dan mamaki take bashi
*****************************************************
Mota biyu akayo daga maiduguri zuwa residence din engineer bature, Engineer bature da hadiza da kuma kanin gwaggo alhaji yusuf da kuma mai gaya Abdulbaseet su suka tarbe su....
Inna falmata da ke dogara sandarta farooq ya riko hannun ta da sauran mukaraban ta, aka yi musu tarba ta musan man, ta gani da fada, sun mutunta su kwarai da gaske kamar da ba'a yi rabuwar wukamci ba.
Bayan anci ansha an dan gagaisawa ta bayan saduwa sannan aka danyi shiru.
Inna falmata ta yi gyaran murya cikin murya ta manyance da dataku tace, bature nasan sanusi yayi maka magana dangane da wannan yaro na wajen ka Abdulbaseet, mun kuma ji daga gare shi,shi wannan yaro, saboda haka abun da ya dako ni daga inda nake nazo nan ba komai bane, sai domin wannan yaro namu ne muma, yanda yake jinin ka haka yake jini na nima, shekarun baya da suka wuce irin wannan zaman ya hadamu duk dangane da wannan yaro kuma kukayi alkawarin zaku riqe wannan yaro amana, toh hakan sai yaci tura, bature kun gaza wajen kula da yaron nan, ka gaza a matsayin ka na mahaifiyan sa, matar ka ta gaza wajen rike maraya, ta gaza daukan wannan yaro a matsayin nata.
Rayuwar wannan yaro ta salwanta, ta lalace, ya gaza kulawa, ya gaza samun so da kauna, kum bari kirsta shi ya reni danka, kirista shi ya ji tausayin dan ka ya raine shi kai baka ji qan naka dan ba, tun da nake a duniya bature ban taba ganin rashin imani ba irin wanda kayi wa dan nan ba.Kasan da cewa danka bai cikin adinin musulimci ya taso ba? kasan da cewa danka christa ne? sai da ya dawo ya bar gida sannan ya gane cewa musulimci shine addinin gaskia.
Inna falmata ta juyo kan hadiza sannan tace allah hadiza jinji nace allah bazan yi kafara ba hadiza, kece ummul-abaisin din faruwar haka, hadiza yaya mata ne da ke, hadiza kiji taron allah, duniyar nan bakomai bace duniya ba matabata bace hadiza, yanda kikayi wa dan wani wallahi hadiza duniya sai tayiwa naki, ramin karya kurare ne hadiza, komi nisan jifa wallahi kau kasa zai yo.
ki duba ki gani yau ina gwaggo ina halimatu, ina mahaifin ki, ina mahifinsu sanusi, duk suna ina?
inda suka tafi duk chan zamu bisu wallahi.
Yaya na allah ne baka san wanda allah zai albarkata ba, sai kiga yayan ki biyu mata sunfi Abdulbaseet zama wani abu a duniya, chuzgunawa da matsawa ba shine ba, zakaran da allah ya nufa da chara..........*****************************************************
Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼
YOU ARE READING
𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓
RomanceSalama, You are the first person on earth that my heart has truly shaken for. I never imagined something like this would happen to me in my life; I thought I would live a single life just like my father, Mr. Glassman. I never thought girls could be...