Episode 5️⃣7️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad************************************Yau juma'a babar rana yau tun safe alhaji sunusi da kanin inna falmata da Engineer bature suka dau kafa zuwa garin adamawa wato yola, domin nema wa dansu Abdulbaseet neman auren salama muhammad yar wajen Bodado.
Tun safe suke tafiya dan salar juma'a ma a hanya ta riske su, kamar yarda aka tsara yaya ado ne ya tari su hanya sannan yayi musu jagora zuwa asalin rugar su inda dangin su suke, yan ruga anyi cincirindo domin kuwa labari ya riske su na salama yar wajen Bodado ta birnin kano tayo zabe...
Datijai hudu ne suka tarbe su harda yaya ado a cikn su,aka yi masu karba mai kayu aka kawo musu wannan da wannan duk har turewa suka dunga yi, nan suka gabatar da abin da yake tafe da su da yaya ado ya ruga ya sanar da su...
Nan suka karbi bukatun su suka kuma amince suka ce sun bawa Abdulbaseet yarinya, allah ubangiji ya tabatar da alheri ya sa rai akayiwa....
Nan suka bada kudi kimanin naira dubu hamsin sannan aka tsaida ranar aure...
Wata mai zuwa na gaban sa wato august kenan a ciki za'a daura aure da yardar ubangiji.
A daren ranar suka baro garin yolo banyan anyi musu goma ta arziki, fura da nono kuwa a yinwata ana sha bai kare ba, dan galan galan haka aka dunga basu nono.
****************************************************
Yau nabeel ya kawo wa Abdulbaseet ziyara tunda shi ya gagara zuwa, tun a airport yake chachakar sa
Wato dan ya kara matsayi ya fishi da step daya shine yake faman wulakantashi, to sa rana dai ba aure bane dan wallahi zan iya zuwa in riga ka a hakan...
Abdulbaseet dai dariya kawai yake yana, shi kanshi zai so hakan ta faru ama bazai iya barin wasan ba gaskia....
Haka dai sukai ta wasa da dariya har suka isa gida...
Shima sunyi maraba da zuwan shi sosai da gaske dan gar dangin shi ya dan zaga da shi ya gaba tarbda shi a matsayin best man 😀Bayan sun gama zaga gari suka dawo gida, Abdulbaseet bai sami lokacin nabeel ba sai da ya tabatar ya gama wayar sa da salama sannan ya dawo kanshi...
So how far with the preparation
Yayi mika yace wallahi nigga i have no ideas har yanzu, sai ruwan ido muke yi ni da farooq yau yace wannan gobe nace wannan....
Ohhh Abdulbaseet ba ni cikin preparation kenan kayi dan uwa, let me park my thing and go i can see you don't need me, ya mike yana kokarin sa hula da gyara agogo....
Yayi dariya ya mike ya dan makalo shi a wuya, haba mana akawai things da kasan me and you ne kawai😉
Yanzu dai ni ba abun da zanji leave the dinner aspect for me i will deal with that.
Ya Abdulbaseet ya kalle shi cikin tsokana yace ba dinner...
Kana hauka ne ko....???
Yayi dariya suka ci gaba da hirar su dai da shirye shiryen bikin har sukayi bacci...
Chan cikin gida kuwa, mommy aziza da farida babu abun da basu hada ba na kayan lefe, abubuwa har sunyi yawa babu gurin saka wa sai akwati kawai ake karowa ana zuba kayayaki....
Dan farida yaya ado ta roka ya barta taje gida ta taya mommy hada kayan lefe, da kyar ta samu ya barta yace tazo tayi sati daya, kuma sai ya rage mata kwanakina kwankin biki da zatayi, rawar kai da shishigi babu wanda farida batayi ba da taga abu zata hasko salama a ciki sai tace a siya a saka a kayan lefe, ko da bikin ta batayi wannan rawar darin ba.Yarta aisha kwa tayi wayo dan har ta fara rarafe kamanim kuma sai juyewa sukeyi suna komawa na Bodado.
******
Chan garin kano kuwa ita kanta hadiza sai da tayo nata siyayar kayan lefen ta tura maiduguri tace a hada a cikin kayan lefe. Engineer kuwa shi da kanshi ya roki alhaji sunusi ya barshi yayi taking part a shirye shiryen nan sannan ya karbi kudi daga hannun sa.Amarya da ango kuwa babu abun da suke zuba wa inba soyayya ba dan yanzu dankon kara tamkewa yake yi domin kuwa a duk wata sai yaje kano sau uku haka, saidai duk zuwan da zaiyi da rana yake zuwa domin ya sami jirgin da zai koma da shi a ranar, idan kuwa yayi missing flight to sai dai yaje gida ya kwana sannan washe gari ya tafi, shi kuma baya son hakan dan gidan Engineer babu kowa sai hadiza da Engineer shi kuma ya saba harka cikin mutane bazai iya zaman kadaicin ba... kunji fa 😱
Tun ana saura sati uku akai lefe mommy aziza ta hana shi zuwa kano, wai yagama ganin ta sai kuma ranar aure, haka basu sami jamewa ba dan ko abun riqewa a hannu bai bata ba ba sai account ya bita da su, ya cika mata shi taffff 😂
****************************************************
Mota uku akayi daga maiduguri zuwa garin kano domin kai lefen salama, mota daya akwatina me da farida aciki sauran moto biyun kuma aka ciko yan uwa....
Hadiza itama ma daga gida ta wuce chan gidan su salama....
Chan gidan ma cike yake da mutanen Bodado, sai guda ake rangadawa kamar gidan zai tsage.....
Aka shiga jido akwatina ana kaiwa ciki tun ina kirgawa ni dai Hasna har batan kirga nayi😂
Set dai, setin akwati shida na gani to ko akwatinan nawa ne🤔 nidai naga seti shida...
Farida sai karadi take, ina binta da ido.... 👀Nan aka yi addu'a aka karbi lefen salama aka kuma tsaida lokaci nan da sati biyu za'a daura auren SALAMA DA KUMA ANGONTA ABDULBASEET
*****************************************************
Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼
YOU ARE READING
𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓
RomanceSalama, You are the first person on earth that my heart has truly shaken for. I never imagined something like this would happen to me in my life; I thought I would live a single life just like my father, Mr. Glassman. I never thought girls could be...