Episode 7️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz (Hasna mansur nagoda)
Wattpad : BintnagsKafin gwaggo kuwa ta dawo hajiya hadiza ta gama shirye shiryen da zatayi akan Abdulbaseet da mahaifin sa da kuma gwaggo ita kanta. Yaran ta su kansu hajar da na'ima ta gama hure musu kunne dangane da Abdulbaseet na kada su sake su dauke shi a matsayin dan uwa domin kuwa Abdulbaseet makiyin su ne kuma rival din su ne.
Da yake kafin gwaggo ta tafi ta sa an gyara mata daya daga cikin apartment din kusa da nata, an kuwa gyara shi an kawata shi tamkar turai dayake dalla na aiki.
A deren alhamis Abdulbaseet da gwaggo suka sauka, direba aka sa ya je ta dako su daga airport ya kawo su gida cikin dare, babu wanda ya tarbe su kuwa,dan duk sun kwanta bacci, gwaggo dai batace komai ba tasa yan aiki suka kai masa kayan sa apartment dinsa, shi kuma tace yaje yayi wanka ya chanja kaya ya fito su ci abinci sai yakoma yaje ya huta.Washe gari Abdulbaseet bai tashi ba sai 9am gwaggo tasa akayi masa breakfast na gani na fada, ta kira kuma sauran yan uwan nasa da mahaifiyar su apartment dinta, dan kuwa Engineer tun karfe 7am ya fita wai ya tafi aiki.
Da salamar su suka shigo, cikin nutsuwa suka ja kujerun dinning table suka gaishe da gwaggo, kallo kawai yabi su da shi dan gani yake tamkar yazo wata duniyar dan mutanen sun banbanta da na kasar su .Yanda basu sakar masa fuska ba shima bai sakar musu ba ya daure abun sa.
Sai da suka zauna suka fara cin abinci sannan gwaggo tace Hadiza ga danki nan yanda zaki riki yayan ki amana haka na baki amanar abdulbaseet kaima Abdulbaseet ga Hadiza nan ka dauke ta tamkar uwa a gare ka kayi mata biyaya kaji Abdulbaseet, duk da Abdulbaseet ba gane mai suke cewa yake yi na ama shiru yayi bai tanka musu ba, in banda girgiza kai da yake yi.
Hajar ce tace gwaggo na zata ai yayan namu baya jin hausa.....gwaggo ta danyi murmushi tace ina kyautata zaton haka dan tun jiya banji yace komai ba sai dai gyada kai da ina kwana, dariya suka yi baki daya, naima tace yaya do you get what we are saying? Murmushi yayi yace Dont worry about me sister , am a fast leaner but the language sounds different.
Sukayi dariya baki daya suka ci gaba da cin abincin su, ama hadiza dai fuskar nan a daure take.Sai da akayi kwana biyu sannan Abdulbaseet yasa mahaifinsa a idon sa, yauma kasan cewar lahadi babu inda zaije gwaggo ta kira shi bangaren ta shi da Abdulbaseet, sai fusge fusge Engineer yakeyi da shan kunu kamar yaga kashi, dan koda ya gaishe shi bai amsa ba,
Nan dai gwago tayi tayi masa nasiha da fada sannan tace Abdulbaseet ya basu guri
Nan gwaggo tace da Enj wallahi talahi idan har ya nunawa Abdulbaseet banbancin a tsakanin shi da yaran Hadiza wallahi bata yafe masa ba. Babu yanda ya iya haka yace toh sannan ya tashi yatafi.Haka rayuwa tayi ta tafiya a gidan Engineer babu ruwan kowa da kowa a gidan kowa sabgar gabansa kawai yake yi babu mai kula shi sai gwaggo sai kuma yar kanwar sa hajar da takan zo dakin sa su danyi hira shima sai ta faki idon maman su batanan sannan, naima kuwa ko hanya suka hada ita da Abdulbaseet sai ta chaza ta,mahaifiyar ta ma haka dayake ita halin su daya da mahaifiyar ta, abinci kuwa wannan sai sai gwaggo ta bashi, Engineer kuwa sai ma suyi sati basu hadu ba, babu ruwan sa da shi.
Gwaggo tace ya samawa Abdulbaseet aiki a company din su Engineer ama keme me Engineer yaki yace ai basu da vacancy ama zai dunga bashi albashi duk wata, kasan cewar abun Hadiza na aiki akan gwaggo ita ma hakan yasa ta yarda ba tare da ta musa ba, hakan yasa duk wata Engineer ke bawa Abdulbaseet dubu dari biyar.
Toh tun gwaggo tana iya bakin kokarin ta akan Abdulbaseet to ita ma yanzu abu yaci tura ita ma an mata dan sudabaru akansa, itama yanxu babu ruwanta da shi sai gaisuwa, abinci kuwa saidai ta sa a kaimasa apartment dinsha shi ma kuma yace kada a kara kai masa abinci apartment zai dunga neman abincin sa da kansa.
Haka rayuwa ta ke guna a gidan Engineer bature da ahalinsa............Wannan shine baban dalilin da ya maida Abdulbaseet haka ya zama soo hopeless and depressed bashi da kowa wanda yake supporting dinsa wanda zai saurare shi ko kuma wanda zai tausaya masa kowa ya juya masa baya, bashi da kowa a nigeria bai san kowa ba gashi da wuyar sabo, dadi da kari baya san mutane, hakan yasa ya yanke shawarar komawa London,koda yayi wa gwaggo zancen komawa London cewa tayi kar ta sake jin ya ambaci London din nan, kada kuma ya sake shigo mata apartment idan har zancen tafiya zai mata, meye ba'a yi masa anan din idan zai tafi sai ta tatara ya koma ai, bala'i dai kala kala.
Haka yayi ta hakuri yana jiran opportunity din da zai koma tazo masa.
*****************************************************
Abdulbaseet saurayi ne dan kimanin shekara 29 dogo ne na gske gashi fari tass shima ga dogon hanci, gashi fafada burin ko wace ya mace. Yana da wani irin hali na rashin son hurda da hada sabga da mutane, musaman mata, shi a tuna nin sa duk mata hankalin su a kwari yake, raini baban abun da ya tsana kenan shi yasa nesa nesa dai kawai. Ga rashin son magana dan shi sai ya kwana ya tashi baice ufan ba sai dai idan Hajar ta shigo dakin sa ta sashi magana dayake tasu razo daya, duk wani abu da zai sa Abdulbaseet ya zama normal human being ya kaurace masa, bama zai bi hanyar ba,idan kowa yayi dama to insha allahu idan Abdulbaseet yazo hagu zai yi, baya son a ga fiskar sa ko kadan hakan yasa idan har zai fita sai ya saka bakaken kaya, bai yarda da kowa ba bai kuma amince da kowa ba hakan yasa yake tafiyar da rayuwar sa shi shi kadai.....................To wannan kenan
Sai mu hadu a kashi na gaba domin jin yarda zata cigaba da wakana.......
Mai yi muku fatan alheri a koda yaushe.....
Bintnagz (Hasna mansur nagoda)Make sure to dropped ur comments
Votes 🗳 like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼
ESTÁS LEYENDO
𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓
RomanceSalama, You are the first person on earth that my heart has truly shaken for. I never imagined something like this would happen to me in my life; I thought I would live a single life just like my father, Mr. Glassman. I never thought girls could be...