2️⃣2️⃣

614 45 4
                                    

Episode 2️⃣2️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad*************************************

Zu ciyar ta taji tana neman amincewa da abin da Abdulbaseet yake fada, tayi saurin rintse idonta ta zame hannun ta daga nashi..... bata tanka masa ba shima kuma bai kara cewa komai ba har suka isa bus stop din (tasha) zaria, inda zai yi mata shatar mota zuwa kano, har yazo zai bude mata mota yaji bazai iya ba yafison yadda ya dako ta ya maida ita har gida, hakan yasa ya kai motar sa car wash na wajen ya biya su kudi yace zai zo ya dauka zuwa dare su kuma suka karasa suka sami wata golf su kayi shata susu biyu har zuwa garin kano.

Suna cikn tafiya take cemasa, meyasa ya biyo ta mai yasa bai koma ba ko yayanke shawar komawa gida ne?
Girgiza mata kai yayi yace a'ah zai kaita gida ne tunda shi ya dako ta da hannun shi ya kamata ya maida ita gida,......
Its more safe, i want u to be safe salama, i dnt want u to fall into bad guys like me....
Murya kasa kasa tace u are not a bad guy...
leka ta yayi ya kali idon ta kawai yayi smiling😊 din da ya dade bai yi ba....
Ji tayi kunya kamar ta rufe ta.....
And wen will u be becoming back home....?
Never na fada a gajarce
Why????? Ita ma ta fada a gajar ce
Ya kara dagewa yayi smiling tare da fadin its a long story salama and i dnt want u to look at me with those pity eyes of urs
Alright fine i will wait for u till u are ready to tell me .....
Alama yayi mata da hannu alamun ok 👌
A haka sukayi ta tafiya ba tare da sun kara cewa komai ba har suka isa garin kano.....
Har kofar gida Abdulbaseet ya kai salama ita kuwa tana tayi masa godiya sannan shi kuma ya juya ya koma garin kaduna har yayi nisa ya tuna cewa ashe bai karbi number din salama ba 🙆🏻‍♂️🤦🏻‍♂️ kamar ya koma ama ina yayi nisa saidai allah ya kuma kadara saduwar su da alheri idan suna da rabon ganin juna kenan.

*****************************************************
Da salama ta shiga gida yau kwanan ta hudu rabon ta da gida, tana shiga ta taga umman ta a bakin fanfo tana alwala, jin muryar yarta da ta dade tana bege yasa ta tayi saurin katse alwalar ta rugo da gudu tana kiran sunan ta salama, salama, ke ce kuwa a rikice take tana jujuyata, salama daga ina kike, ina kika shi, lafiyar ki kalau dai ko.
Kuka ta fashe da shi ita ma umman tasau ta fashe da kuka suka rungume juna suna shashe kar kuka, yaya ado ne ya shigo ya tarar da su awannan yanayin abun da ma ya sa suka sasauta da kukan kenan, suka samin guri kan tabarma a tsakar gida suka zauna.

Salama meyasa kika bishi ba saida nayi miki kashe di dangane da wannan yaron ba, ke a ganin ki yayi miki kama da wanda zaki yarda da shi, me yayi miki, yana ina ma ....yaya ado ya tambaya cikin bacin rai.

Yaya ba shi bane.....😢
Rabona da shi tun lokacin da aka salame shi daga asibiti , ya rage mun hanya shi kuma ya koma gida.

Inji uban wa....???
Yaron da muka ga ya tura ki cikin mota kina ja yana ja.....

Wani dan tunani tayi sannan tace
Wlh yaya sabani muka samu ne, shi yasa
Kuma a hanya ya sauke ni shi kuma ya tafi....

Ina ya tafi da shima har yanzu bai koma gidan su ba in ji Bodado ,ni da yayan ki da kuma kawarki muka je gidan su ama ba labarin shi shima......

Toh ni gskia ban sani ba.....
Umma ni ku daina mun zancen shi dan allah
Ni da yakamata ku tambaye ni lafiyar jikina

Toh indan ba shi ya dauke ki ba ina kika shiga tsawon kwana biyu kika bar mahaifiyar ki cikin tashin hankali , ashe baki da wayo salama ina miki kallon mai hankali ashe baki da shi. Bazaki bude baki kiyi mana magana ba.

Kuka kawai ta fashe da shi, tare da fadin ai wata mata ce ta dauke ta waya mutu wayayi rai karyayaki irin na salama da kyar ta samu ta kubuta daga hannun ta da kuma kafin addu'ar su, har dai ta sanu suka yarda da abin da ta fada sannan.
Bodado tace komai ya wuce ai yanxu tunda allah ya bayana mata yarta Alhmdulillah allah kuma ya tsare gaba.
Tace da yaya ado yaje ya sanar wa da iyayen Abdulbaseet cewar kanwarsa ta bayana kuma ba tare suke ba ita da Abdulbaseet din ba.

Koda aka sanar wa da mahaifin Abdulbaseet Engineer kenan cewa salama ta bayana yaji dadi na haki ka dan atleast yanzu da dansa kawai zaiji ba tare da yaji wa su Bodado wani abun ba, ya taya su murna sosai ya kuma godewa allah.

Alhmdulillah yanzu dai sudabarun hadiza baya cin Engineer yanzu dan yanzu yafi karfi gun gwaggo dan yanzu gwaggo ke yarda da duk abun da tace koda kuwa meye, tana fada ya zauna daram babu makawa sai gwaggo ta aika ta shi dan idon ta arufe yake.
Sunyi sunyi a rufe account din Abdulbaseet ama Engineer yayi kememe ya hana yace duk wanda ya taba masa account zasu sa kafar wando daya.
Shi a ganin Engineer idan har inda Abdulbaseet yake yana jin dadi kuma ya fiye masa zama da gwaggo da kuma hadiza ga kuma wannan aure da suka bijiro da shi idan har hakan zai kwantar masa da hankali toh yayi zaman sa  ba sai ya dawo ba. Hakan yasa ya cigaba da cika masa account da kudi iya yanda yasan zai ishe shi har yayi masa ragowa.

****************************************************
Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************

Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)

Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼

𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin