3️⃣6️⃣

499 46 0
                                    

               Episode 3️⃣6️⃣
            ‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad************************************

Naci da bin didiqi irin na nabeel bai barshi ba sai da ya tatse Abdulbaseet gaba daya ya bashi labarin da ya dade yana boye masa dan sai da ya bashi labarin sa tassss
Nabeel yayi mamaki matuka, ya kali Abdulbaseet yace kai anya kuwa kaine mike din da na sani back in the days,
Abdulbaseet dai kawai sharewa yake dan shi kanshi yasan cewa ya riqe lamarin da sauki....
Why would you let them rule your life for u you are the owner of your life fa, babu wani shege da ya isa yayi maka rayuwa basu da ikon tsara maka rayuwa....
Look i have a way to sort this out for you, ni da ka fada mun ai duk da mun dade da solving wannan matsalar....
And ya ZATA YI SOLVING
Ya zakayi solving....?
You are trying shaaa 😃
This is very easy and short but you have to cooperate...
Let's finish this issue first and we will deal with the other one lets go step by step.....
Haka dai suka hakura sukayi bacci wajen karfe biyu na dare....
Washegari kuwa basu tashi na 12 na rana
Shi yace zai tafi main house din su suyi magana da baban sa shi kuma wa wuce hotel din sa.....
Nabeel na zuwa gida ya tarar da baban su ya fita hakan yasa shima kawai ya wuce kamfani
A nan ya tarar da yaya ado dan har yanzu yaya ado bai taba yi masa maganar Yaya Abdulbaseet ba ko sau daya duk da yasan alakar su....
Sun zaune suna lunch da har nabeel zai masa zancen Abdulbaseet sai kuma ya fasa...
Yana cikin wannan sake saken yaji wayar sa na ringing ya dubawa ya ga Mike...
Yayi saurin dauka da har zaice Mike sai kuma yace
Hello Abdulbaseet....
Yaya ado ya dago ya kalle shi alamun ya gane da wa yake magana sai kuma ya dauke kai,
Nan dai suka tatauna abun da zasu ce suka kashe wayar
Da har yaya ado zai hakura dan shima so yake ya tambaye shi dangane da Abdulbaseet ama ya gaza, haka kawai ya kai zuciyar sa nesa yace
Nabeel naga alama Abdulbaseet is among your best friend...
Dama abun da nabeel keso kennan
Nan ya bude sabon babin yabon Abdulbaseet gaban yaya ado
Yeah Abdulbaseet na hannun dama na ne, sosai ma he is a very decent and nice guy, he is very cool wallahi, i just wish he will get a cool and decent wife like him
Yaya ado yayi gyatsine alamun bai yarda ba, ya kara cewa
How many years have you knwn him
Nabeel yadan yi lissafi sannan yace  8years kenan.... munyi high school grade 5and 6 tare sai na dawo naija nayi one year sai kuma na koma sukayi the same course tare for 4 years plus this year 8 kenan in total
Yaya ado dai kawai kallon shi yake yana jin wannan dogon bayanin nabeel
Kasan kuwa bai taba zuwa naija ba sai wannan karon, tun da yake
Meyasa ba yana da iyaye ba ko suma a chan suke da zama
Noooo tum yana yaro yake chan bai kuma taba dawo wa ba sai wannan karon
Na zata a kano  yake da zama
Mai ya kawo shi kaduna....
Changes kawai irin ma rayuwa...
Ama da alama yana cikin damuwa...
Mai yasa kace haka...
Gashi nan fuskar shi kullun cike da damuwa,
Abun da nabeel yake so shi ya faru kuwa dan sai da yaya ado ya kwashe labarin abun da  ya faru tsakanin su tasss ya fada wa nabeel
Nabeel bai bar wajen ba sai da ya tabatar yayi clearing duk wani miss understanding din da ke zuciyar yaya ado dan gane da Abdulbaseet
Ama bai fada masa shi yayi kidnapping kanwarsa ba yadai fada masa yana da family issue ne da bazai iya zama da su ba shi yasa ya zabi ya bar musu garin kawai haka dai suka kare labarin nasu.....

Sai da daddare nabeel ya sami baban su yayi masa bayani mai kyau dangane da Abdulbaseet, yaji labarin kwarai da gaske dan kuwa ya taba shi sosai, ya kuma yi alkawarin insha allahu zai yi ma malam kabir daurawa magana idan yaso sai su ga yanda abin zai kasance
Ama me yana so ya fara ganin Abdulbaseet tukunna.....

Washe gari da sasafe suka bayana shi da Abdulbaseet suka tarar da shi a baban pallor dinshi....
Bayan sun gagaisa sannan babban nabeel yace da Abdulbaseet ya ji labarinshi daga gurin nabeel kuma yayi alkawarin zai taimaka masa kwarai da gske kuma yana murna da jin hakan, ama me Abdulbaseet sai yayi hakuri yakuma kai zuciyar sa nesa ya kuma iya zama da mutane....
Sai kuma yayi alkawarin zaiyi watsi da dukkin al'ada irin ta bayahude da nasara domim kuwa haramun ce a addinin musulimci,
Sai kuma yasa a ransa zai karni addini musulimci ba wai dan yarinyar da yake so ba, sai yayi alkawari ya kuma sa wa ransa ba dan ita ba dan ceto kansa daga halaka, ya kuma gano addinin gaskia...
Mahaifinshi ma sai yayi alkawarin zai koma musu ya nemi gafar shi ko ta halin yaya, sannan ya nuna musu baya son auren yarinyar da aka bashi idan kuma har sun dage da sai ya aure ta to ya karbi kadara domin kuwa mumini dole yayi imani da kada mai kyaunta ko mara kyaunta.
Addinin musulunci kuma ya halata masa aurem mata har 4 saboda haka idan ya auri wadda iyayen sa suka ummarce shi da ya aura yana da ikon karo guda uku idan har yana da halin kula da su idan kuma zai yi adalcin a tsakanin su.
Nan dai yayi tayi musu wa'azi da nasiha mai shiga jiki sannan yace su tashi su tafi zai neme su idan yayi wa mallam kabiru gombawa magana.....

*****************************************************

Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************

Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)

Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼

𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓Donde viven las historias. Descúbrelo ahora