9️⃣

618 44 0
                                    

                 Episode9️⃣
             ‼️Abdulbaseet ‼️
Na :Bintnagz (Hasna mansur nagoda)

Tunda allah ya hallice shi yauce rana ta farko da ya dauki shadda zai sa, yayi ta tunani yaje ya dawo akan ya saka ko kar ya saka shaddar, chan ya hango wani farin yadi mai laushi da yayi kama da yan kantin da yake sawa, ba shiri ya cire ya zura farin yadin
Wando da riga ne jamfa wanda sukayi matukar karbarsa, darajarsa da quality dinsa suka kara fitowa yayi kama da namiji na kwarai abun sha'awa da shi.
Shi kuwa nauyin jikinsa da kunyar kansa yake ji haka dai ya daure ya fito.

Suna tsaye bakin mota suka hango tahowarsa,salama ce ta fara ganin sa, cikin nutsuwa ta kale shi tun daga sama har kasa, itama duk da maza basu fiya burge ta ba ama harga allah yayi mata kyau,
Jin Hajar tace yayaaaaaaaaa ya katse mata tunanin ta.....
Wowww this is my yaya wait ina zuwa, ya ruga da gudu ta je dakin sa dan dako masa hula, ta bar shi tsaye shi da salama......
Ina wuni salama ta fada cikin siririyar murya jin ya dan yi shiru bai amsa ba ta tuna da cewa ashe baya jin hausa ne ko bai san yanda zai yi replying dinta bane
Jin yace lafiya lau yasa ta daga ido ta kalle shi suka hada ido
Tayi sauri dauke ido.......
Sai yau Abdulbaseet yayi wa salama kallo na hakika tayi kyau matukar gske gata kyakyawa anya kuwa wannan kyan dan ba haushe ne wannan Kyau na salama......
Yana cikin wannan tunanin Hajar ta iso rike da hula a hannun ta .....
toh yaya ga mahadi shigar ka nan kaga yanda kayi kyau kamar ba kai ba nace maka dama ka dena sa bakaken kayen nan ka ki ,yanzu dan allah kai baka ga kayi kyau ba....... i never knew u were this handsome😉
Hajar keep quiet idan zaki shiga muje ki shiga na gaji da shegen surutun ki.....
Sukayi smiling su biyu, ya daga kai yakalli salama yaga smiling dinta....
A zuciyarsa yace she has a killer smile.
Hajar ta shiga gaba ita kuma ta zauna owners conner, kallon sa kawai salama keyi ta gefe a nutse cikin yanayin burgewa, hakikanin gskia ya burge ta da gani ba ruwan shi ga shi yana da nutsuwa saidai da yayi magana sai taji kamar ta taba jin voice din ama ta kasa tuna ina ta taba jin muryar....side view din shima looks familiar ama shiru ta kasa tunawa.

Suna tafe suna yar hira jefi jefi da salama
Shima a tasa zuciyar tuno encounter din shi da salama yayi tayi, yana jin muryar ta yana she has a cool voice.

Sun tsaya wajen kennan yazo zai yi reverse domin ya samu yayi parking daidai, ya sa hannun sa jikin sit din har abun Hannun sa ya buga, hannun rigar sa kuma ya dan daga.

Karaf a kunnen salama sautin da bazata taba mantawa dashi sautin da ko ina ta jishi zata banban tashi da kowanee irin sauti, sautin da bata taba jinshi ba sai a wajen Abdulbaseet.
Gabanta ya fadi jiki a sanyayi ta daga ido ta kalli abun hannun nasa, ta kalli fuskar shi nan take ta tuno fuskar shi da ta gani a sahad. Nan da nan yana yinta ya chanza, dama yayan Hajar ne mamalakin wannan sautin shine wanda ya kade ta, shine wanda ya kaita asibiti , shine kuma mai sa bakaken kayen nan ashe shi yasa hajar tayi masa zancen bakaken kaya dazu, ashe shiyasa jikin ta yake bata kamar ta sanshi.

Tana cikin wannan tunanin taji Hajar na cewa yaya wannan karar abun hannun naka wallahi tsoro yake bani wllh daukar hankalin mutane zai dunga yi dan allah ka cire shi...... sauka Hajar na kawo ku ai so get out kar ki kira ni kuma sai nan da 2hrs i have others things to do, allah ya huci zuciyar ka sai ka dawo ta fada yayin da take bude kofa suka fita.
Ajiyar zuciya yayi yace da allama yarinyar nan bata gane ni ba thank God dama haka nake so sannan ya ja motar sa yayi gaba.

Shagali yayi shagali ama salama yarda ta fito daga gida ba haka ta iso wajen ba dan duk jikinta a sanyaye yake tunanin ta da hankalin ta Abdulbaseet ya tafi dasu, dan har sai da kawaye nasu suka lura akwai abun da ke damun ta ama ta wayence da babu abin da ke damunta.

Karfe 8 daidai Abdulbaseet yazo daukan su yana kiran su suka fito sai da sukazao bakin gate sannan salama tace ai ita daga nan zata wuce gida bazata tafi tare da suba.
Hajar tayi ta rokonta ama taki kememe sai da ta fada wa Abdulbaseet, shima har zaice a barta ta tafi ya tuna da halin da ya barta ranar nan na rashi kudin mota hakan yasa yace..... what sort of nonsense is this ta shigo su tafi yanda suka kawo ta haka zasu dauke ta su maida ta gida..... ganin gogon naka ya hade girar sama da ta kasa yasa ta amince tace toh sannan ta shiga mota suka tafi badan tana so ba.

To be continued ..........
Mai muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnagz (Hasna mansur nagoda)

Make sure to drop ur comments
               Likes and votes 🗳
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin