Episode 4️⃣4️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad************************************Kuka kuwa wajen faridah kamar me kamar ance mata ga ranar mutuwar ta dan ko yaya ado kasa lalashin ta yayi....
Yaya ado ma ji yayi kamar yasa Abdulbaseet a gaba yayi tayi masa kuka da yasani da ya temaka masa tun sanda yake bukatar taimako da yasani bai yi masa tsanar da yayi masa ba, yayi da na sani kwarai da gaske, lale kuwa baya iya bada labarin sa ba kai tsaye abun da ciwo.Farooq da idon sa yayi jajir ya dago yace daddy wallahi bazamu kyale step mother din nan tashi ba dole sai ta gane kuranta,
Mommy aziza tace kaga farooq abun ba duka ba zagi duniya ai makaranta ce kuma tana da yaya allah ai ba azalimin bawan sa bane kuma ai yaya mata ne da ita ba yaya maza ma duniya zata yi mata bayani.Mudai yanzu Alhmdulillahi tunda bata salwanta mana rayuwar yaro ba kuma ya dawo gare mu ai sai mu gode wa allah.
Yanzu maje mu sar da inna falmata labari mai dadin gaske..
Nan alhaji sunusi ya ce Abdulbaseet ya share hawayen idon sa damuwar sa ta kare a duniya, bi izinillah ya gama sanin meye kuncin rayuwa ya kuma gama sanin meye rashin uwa da dangi a rayuwa, saboda haka ya godewa allah, allah shine abun godiya!
Alhmdulillah!!Nan aka ci aka sha, akayi hira da tuna baya akayi raha da dariya abun gwanin ban sha'awa allah mai yada yaso ya yaye maka bakin cikin ya kuma yaye maka damuwa. Allah shine abun godiya.
Nan alhaji sanusi da mommy aziza suka tafi masaukin su da yanma, su kuma samarin yaya ado da nabeel da farooq da Abdulbaseet suka tafi zaga gari dan har faridah na cewa sai ta bisu da kyar yaya ado ya lalaba ta yace ta bari su gama sabawa da yayan nata kafin su saba, sukayi dariya baki daya suka fice.
Suna fita marble hotel suka isa inda Abdulbaseet ke kwana dan yaya ado da farooq suga inda yake kwana, bayan sun gama da nan kuma suka wuce sky resort inda suke hanging out shida nabeel suka sha coffee da tea suka dan samu time dinsu sannan suka wuce sukayi salar magariba sannan yaya ado yace zai komawa matarsa dan ta ishe shi da kira, farooq kuwa ya makale shi ba inda zaije sai sunyi salar isha zai ware...
Sai da sukayi salar isha sannan suka je masaukin su daddy sannan sukayi salama yakuma yi musu alkawarin yana gama clearing abubuwa zai koma maiduguri insha allah.
Da asubar fari kuwa suka dau hanya sai garin barno.
****************************************************
Jikin gwaggo yayi tsanani dan ko tashi bata iyayi daga kan gado, gashi sai processing visar india suke yi basu samu ba domin shi kanshi likitan da yake duba ta abun yafi karfin shi, gashi abu kullun gaba yake kara yi.
Yaudai Engineer yaga bazai iya zubawa abun ido ba hakan yasa ya dauki gwaggo ya kaita UMC hospital dan sun kware sosai dan gano ciwon da suka gagara samun sauki kamar na gwaggo da ba'a san maike damun ta ba, gashi yau ta tashi da shanyewar barin jiki.
Tana kwance sai faman kiran Abdulbaseet, abdulbaseet, Abdulbaseet a hankali cikin sarkakiyar murya hawaye kawai ke zuba a cikin idon ta nuni da akira mata Abdulbaseet a waya, hadiza kuwa sai faman ce mata bata shiga take yi, gwaggo number dinsa bata shiga.
Engineer kuwa ya kara zafafa wuta wajen yan sanda na a nemo masa dansa daga yau zuwa gobe,
Gaba daya yabi ya kidime ya rude ran mahaifiyar sa a hannun allah ga kuma Abdulbaseet da take muradin gani.
Haka suka kwana a asibitin nan babu abun da gwaggo ke furtawa in ba Abdulbaseet ba dan ita kanta hadiza ta tsorata da lamarin gwaggo.......
Wayar hadiza tayi ringing ta ringing tayi sauri sa yannu a jaka ta zaro ta, tana dubawa taga naima ce,
Mommy kina ina ne sai kiranki nakeyi..??
Ina asibiti na'ima kwana mukai muna kan gwaggo ba lafiya....
Tohh allah ya kara sauki...
Amin ta fada tana shirin kashe waya...
Naima yaushe kika sa ticket din dawowar ki, munjiki shiru daddy din ku fa ya dade da turo miki da kudi...Dawowa kuma mommy, mai zan dawo nayi muku, gaskia ni bazan dawoba, ina da abubuwan yi da yawa anan, besides bazan iya tafiya in bar lucus shi kadai ba...🙄
Kinga naima ki taho da ita, ana yi wa maguna nasu process din tafiyar ai, Karfa ki manta nace miki gwaggo bata da lafiya...
Mage mummy wace irin mage kuma ni mai zanyi da mage kar fa ki manta na tsani mage ni.
Toh meye lucus di da bazaki iya tafiya ki bari ba...??
Hmm mommy kennan Lucus Eward din kike kira da mage lalle mommy...
Ke bansan shashanci ki dawo cikin satin nan kafin na hada ki da daddyn ku..
Tana kaiwa nan ta kashe wayar.
Ta koma kan sharewa gwaggo fuska da ta dan samu bacci ya dan de be ta.Engineer ne ya shigo yana haki, hadiza hadiza kina da hoton Abdulbaseet??
Abdulbaseet kuma ni mai zanyi da hoton sa kuma, duba kiga shine wannan, ta kalla fuska a tabe tace eh shine meye.....??
Alhmdulillah Alhmdulillah Alhmdulillah...???
Kai dan naka ma ka kasa ganewa uhmm abun kuya dai wallahi...
Hadiza i just wanted to make sure, yanzu inspectet ya zo mun da zance yana garin kaduna a wani hotel mai suna marble, shekarar sa guda a hotel din dama kuwa har su kansu masu hotel din suka fara suspecting din shi wanene and daga ina yake shine suma suke dan yi mini investigation akan shi, so lucky enough inspector cousin din mai marble ne and he got to knw about Abdulbaseet which is masha allah.
Gaban hadiza yayi wani darammmm kam bala'i lalle ya kamata ta kuma zage dantse, dan tayi sanyi ba shi ke nuna cewa ta hakura ba, gashi kuma yanzu Engineer yazo yana mata rawar dari akan dan sa Abdulbaseet...
Sam bazata taba sabuwa ba bindiga a ruwa.....*****************************************************
Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼
KAMU SEDANG MEMBACA
𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓
RomansaSalama, You are the first person on earth that my heart has truly shaken for. I never imagined something like this would happen to me in my life; I thought I would live a single life just like my father, Mr. Glassman. I never thought girls could be...