Episode 1️⃣5️⃣
‼️Abdulbaseet‼️
Na: Bintnagz( Hasna mansur nagoda)
Make sure to check out @bintnags on wattpad*************************************
Cikin mamaki yaya ado ke kallon Abdulbaseet dan bai gane mai yake nifi ba, anya kuwa har yanzu ba a bige yake ba tun da ance shaye shaye yakeyi.
Ama meye dalilin ka na cewa bazaka koma ba, gidan kune fa, iyayen ka da kannen ka.
Yayi murmushi da kyar yace wannan gidan ba gida bane mutanen cikin gidan ba mutane bane monsters ne.....
Kaga dakata ya sunan ka.....
Abdulbaseet ya fada masa....
Abdulbaseet ka kuwa san mai kake cewa....❓
Suna cikin haka salama suka shigo ita da sabeeha, rike da flask din ruwan zafi da kayan shayi a basket.
Nan suka gaishe shi sukayi masa ya jiki sabeeha ta sami guri ta zauna
Ita kuma salama ta fara kokarin hada masa shayi,yaya Ado dai na zaune yana nazari kala kala dan gane da wannan mutun.....
Sabeeha kuwa sai satar kallon sa takeyi, anya kuwa wannan bahaushe ne, kalle shi fa, ji jikinsa kamar kana latsawa jini ya fito, ji kansa kamar na yan korea, yau ita dai taga halitar ubangiji. Duk farin salama wannan yafita fari dan yau sai taga salama takoma baka akanshi. Tana cikin wannan tunanin taji salama tana cewa eh kawatace sunnan ta sabeeha, dayake tambayar ta yayi. Ta kali yaya ado kuma tace wannan kuma brother nane.
Yayi murmushi yace ai naga alama kuna kama sosai,sukayi dariya.
*****************************************************
Kiran da salama tayi wa hajar yasa ta watsake daga baccin, ta kira takira kuma taji wayarta a kashe, bata kawo komai a ranta aba ta tashi ya fara sabgogin gaban ta. Sai wajen azahar ta tuna da yayan ta hakan yasa ta tafi wajen sa da dan fara'ar ta....
Tana shiga taji wayam ba kowa sai ta zata ya fita....Bata duba komai ba ta fito daga dakin dan ganin motarsa ma bata nan.
Nan ta yi ta jiran dawo warsa har wajen magariba ama shiru bai dawo ba, ta dauki waya ta kira shi, ama wayar sa akashe, haka dai ta hakura bata sanar da kowa ba har taga dare yana tayi ama yayanta bai dawo ba, toh wa zata fada wa ma, ama kafin ta yanke wani abu bara ta kara jira ta gani dai.Chan kuwa asibiti gurin Abdulbaseet, masu jinya sunyi jungun jungun kamar wanda akayiwa mutuwa, can salama da sabeeha suka ce zasu wuce makaranta nan suka yi masa sallama suka fita suka barshi shi da yaya Ado.......
Yaya ado kuwa ba zaman komai yake ba sai jin labarin Abdulbaseet......
Yanzu da gske kake nima in tashi in tafi in barka kai kadai anan..?
Ba damuwa wllh nagode kwarai da gske wlh nagode....Ama dan allah ina so kafin ka tafi ka sama mun hotel din da zan zauna idan an salame ni da sunan ka ko kuma wani suna dai da ba nawa ba.....cikin harshen turanci.
Cikin bacin rai Ado ya juyo ya kale shi
Wai mai ke damun ka ne, ka fada mun matsalar da take tatare da kai, mai yasa ka ke nisanta kanka da dangin ka da iyayen kane, mun dako ka cikin maye mun kawo ka asibiti, atleast ko ba komai ya kamata ka sanar da mu halin da kake ciki, idan kuma baza fada ba toh wlh am not ready to help you, tashi yayi a fusace ya fice.Dayake yaya ado yana hada masa da turanci da kuma hausa hakan yasa ya gane abun da yake fadi, yayi ajiyar zuciya ya gyara kwanciyar sa ya kwanta.
******
Su kuwa su salama tun da suka fita sabeeha take mata zancen sa na ya hadu yayi wace tsiya yayi wace tsiya duk tabi ta rikice tana santin kyaunsa... ita kuwa salama kasa cewa komai tayi jikin ta duk yayi sanyi kamar ita ce bata da lafiyar, har sun shiga makaranta salama taji bazata iya zaman makarantar ba,kawai tasa kai ta fice ta koma asibitin.
Jin motsin shigowar mutun yayi saurin dagowa hada ido sukayi da tayi saurin sunkuyar da kai...
SALAMA ya fada cikin mamakin ganin ta....Duk kurin salama, ashe na banza ne ko daga ido ta kalle shi kasa yi tayi, ji tayi kamar ta koma dan a bakin kofa ta tsaya.
come in please......
Shiru bata ce komai ba bata kuma matsa daga inda take ba....
Shima shiru yayi ya bita da kallo kawai,
Do you want me to come and pick u up?
Ganin yana kokarin tashi daga kan gadon da kyar yasa tayi saurin karasowa inda yake....
Garin kokarin tashi ashe ya tuje abun karin ruwan nasa jini sai diga yake....ganin jinin yasa tayi saurin cewa jini 😳 hannun sa ta kamo a rikice ta rike tana dane masa wajen zubar jinin.Sun fi sakan 30 a haka ganin smiling din da yayi yasa ta farga da abun da tayi,tayi saurin sakin hannun tare da fadin bari naje na kira likita.... dayan hannunta ya kamo tare da girgiza mata kai alamar ba sai taje ba.
Tsayawa tayi tana kallon shi sai kuma yace baki iya first Aid ba ai an koya miki ma makaranta ko??
Ta gyada masa kai a hankali, sannan yace toh apply your skills
Dayan hannun sa yasa ya miko mata flaster da kuma tissue da cotton ya bata.
Ba bu ko gargada ta cire masa allurar daga cikin jikinsa sannan ta sa cotton da flaster ta mane wajen...shi kuwa ba abun da yake yi sai faman kallonta sai kara burge shi take yi....Guri ya nuna mata kan gadon gefen kafarsa data zauna, ita kuma ta kasa zama sai kujera ya janyo ta zauna tana kallonsa, tana wasa da yan yatsun ta.
Da kyar ta samu bakin ta ta furta
Meyasa da kaji baka da lafiya kazo gidan mu mai makon ka tafi asibiti??
Murmushi ya dan gyara fuska sannan yace..... because you are all i have left.............Toh masu karatu anan muka kawo karshen wannan episode din.....
mu kasance cikin episode na gaba domin jin yanda zata kaya tsakanin Abdulbaseet da kuma salama*********************Mai yi muku fatan alheri akoda yaushe
Bintnags( Hasna mansur nagoda)Make sure to drop your
Comments
Likes
Vote 🗳
Much love and Stay Blessed 🙏🏼
VOCÊ ESTÁ LENDO
𝐀𝐁𝐃𝐔𝐋𝐁𝐀𝐒𝐄𝐄𝐓
RomanceSalama, You are the first person on earth that my heart has truly shaken for. I never imagined something like this would happen to me in my life; I thought I would live a single life just like my father, Mr. Glassman. I never thought girls could be...