4

2K 86 2
                                    


Tunda *Maikyau* yatafi ZAHRA takoma silent, abinci sai ance taci sannan taci, rawar kai da fitirita duk babu
Idan tashiga d'aki, bata fitowa, saitayi ta kuka, Inna da Amarya sun zata abune mai wucewa, amma ganin an d'auki lokaci babu canji, saisuka fara mata fad'a
Ga abu kuma yazo ya had'e mata, ciwan mara, mai azabtarwa, gaba d'aya sai ta koma wata kalar tausayi
Innan gidan Maigari, itama tayi tunanin *Mahmud* nason *ZAHRA* amma ganin yadda yatafi batare da yace komai ba yasaka ta fidda rai
Amma taso ya k'aunaci ZAHRA kodan yadda tacanja akan komai, kuma tasan bazaiyi dana sani ba
Yau gidan Maigari *ZAHRA* taje, d'akinsa tayi inda ya zauna, a kulle yake, gurin inna tayi, tace Inna ina mukullin d'akin *Maikyau*?, Bata tambayeta kome zatayi ba, cirowa tayi ta bata
Shiga tayi, komai yana nan sai jakar kayansa daya d'auka, hatta littatafanta suna nan, wasu kayan nasa ma anan ya barsu, *ZAHRA* batasan meye *SO* ba, a shekarunta, amma gashi batare da sanin taba, Allah ya aza mata son *Maikyau*
Itadai tasan kawai kullum dashi take kwana take tashi azuciyar ta, dan ko abinci take ci, yanxu zakaga ta ajiye kwanan tafara tunani
Kayansa ta janyo, rungume wa tayi, ajikinta wata nutsuwa ta saukar mata, wadda rabon data ji, harta manta
Duk abinda take, Inna na kallon ta, hawaye taji ya zubomata, tunda ta fuskanci *ZAHRA* ta fad'a tarkon *SO*, lallai datanada hali Wallahi babu abinda zaisa bata aura wa *ZAHRA Mahmoud* ba, amma batada hali, shi aure irin nasu tasan saikana SO, sannan akeyi
Amma yaxatai, saidai addu'a, itace maganin komai
Haka kullum ZAHRA take kasancewa, wani sabon tashin hankali kuma, Malam ya tsayar mata da miji, kuma wata 2 kacal akasa
Ganin tana wannan halin, yasaka ba'ayimata magana ba, amma yau zai sameta
Haka akayi, saida yabari tagama cin abinci, tana d'akin Iya Hauwa, matar malam ta uku, yashigo zama yayi akasa
Lokacin ita sallah take, saida ta, Idar tashafa addu'a sannan, tace Baba ina yini" lafiya Lou ZAHRAN Baba, yar albarka, dariya tai tace, Malam dama yanxu nake cewa zani gurin ka?
Allah yasa alkhairi?, Allah kwad'ayi nakeji, kwana biyu baka siyo mana wannan tsiren mai dad'i ba
Nasiyo kuwa, kina wa mutane kuka, ina zakisan nasiyo, tunda kinaci bara Tasi'u ya shigo saiya karb'o miki, yauwa Malam tnq, dariya sukayi dukkansu
Ganin ta ware tanata labari da dariya, yasaka Malam maida hankalinsa kanta, yace ZAHRA " na'am Baba
Yauwa, kindaisan tsarin gidana, wanda wannan tsarin inayinsane sama da shekara 30, kuma bani iya canjawa, alkawarine na d'auka kuma lokacin cika shi yayi
Tunda yafara magana hankalinta yake a tashe, ita tashiga dubu, yauwa maganar sa ta dawo da ita, ZAHRA kowacce yarinya agidan nan, bata wuce shekara goma sha biyar nake aurar da ita, kinsan haka tunda anyi bikin 'yan uwanki a gaban ki
Saboda haka, nayimiki miji ba kowa bane face, Anas d'an gidan Sharif Auwal, abokina dayake garin Kano
Mahaifinsa ya ganki, yace yana barar indai ban miki miji ba, to yana son d'ansa zai shiga ciki, kinsan shi sosai, yaran mai hankali ne, da mutunci malamin makaranta ne, a ( Sheikh Tijjani usman Zangon bare bari) da karatun sa, bawai d'an jagaliya bane
Nayi farin cikin kasancewarki cikin zuri'ar Sharif Auwal, dan mutane ne malamai, garin kano bawanda bai san suba, wajan tarbiyya da ilimi
Saboda haka zaizo, zaku gana, ita Innar taki zata koyamiki Komai
Ita dai ZAHRA jin abin tayi kamar almara, kenan Idan akayimata biki zata dena ganin *Maikyau* kuma Idan yazo bata nan, bayan haka itafa *Maikyau* yace kada ta kula kowa, kuma tayi karatu, she tak prms, kenan ita bazata cigaba da karatu ba
Wani irin abu taji ya tsayama ta a makoshi, tayi tayi ta had'iye dan amsawa Malam amma takasa
Basuyi auneba, sai ganin ta sukayi a qasa a yashe, babu alamar numfashi tare da ita
Kuka Iya tasaka tafara neman agaji, ruwa Malam ya d'ebo zubamata yayi, amma shiru haka yayita yimata tofi amma ko motsi
Innar gidan Maigari, kafin kace me duk sunzo, anrasa gane kome, ahaka Ya Auwal yazo, baiyi wata wata ba, ya sunkuceta sai *General hospital Gaya*
Gudu yakeyi cikin motarsa sai General hospital dake garin na gaya, parking yayi d'aukanta yayi a hannu, hankalinsa a tashe, jin ko motsi ZAHRA batayi, gawani nauyi datayi, Inna ma gaba d'aya ita takasa sarrafa hawayenta, zuba duke ba qaqautawa
Reception ya shiga Doctor Lubie suka gani, da sauri yace plx sister help ma sis I don't wnn loss her plx, gaba d'aya shima kansa a kwance yake, da sauri aka kawo gado aka sakata
Checking nata ta fara, amma bataga alamun xata farko ba, gadai alamar tanada rai, amma he can't do anything dazata farka, kota ga ta inda abin yak faru
Sosai taduba, ganin ba hali, saita sakamata drip, fitowa tayi tace, am Malam gaskiya aganina best solution kawai kutafi AKTH saboda anan za'a duba ko menene yake going nan ni gaskiya nayi iya yina, inda problem yake ban gane ba
Baijira amsarta ba, yatafi cikin d'akin, da gudu ta bishi nasamata drip da kabari ya qare? Noo zan d'auketa na, kawai
Haka ya ciremata suka kamo hanyar Kano, a wudil suka tsaya sallah saboda anyi magreeb da Isha kuma basuyi ba, shiyasa ya tsaya
Matar sa ce tamasa waya, lokacin harsun idar yana shirin Shiga cikin mota
[05/10 2:16 pm] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻🇳🇬: "Hello"
Aysha ya gida?, lafiya lou kaje lafiya?, huum lafiya lou, amma ganima na kusa cikin gari ma
"Me ya faru?, wallahi ZAHRAN Baba ce ba lafiya, munje amma sun turamu AKTH, shine muka tawo, wai Allah yabata lafiya amma kuma da zakuje *HAUBEN Hospital* wallahi dayafi dan likitocin asibitin kansu India ne, wasu ma daga *Miami* aka kasu, nawani matashi ne, wallahi asibitin badai kyau ba
OK yana daga ina, naji ana fadarsa kuwa?, ta ina yake?, yauwa ai kasan Kano capital? eh nasani, yauwa to idan kayi baya kad'an ai akwai unguwa *MATAN FADA*? Good nasani to anan yake babu wuya zakaga symbol nasu daga kaje, Allah yabata lafiya Ameen
Haka yacigaba da driving, har suka k'arasa, sosai gurin yaganeshi baisha wahala ba, shiga sukai da gudu Sister Ummu Haneepa ta k'araso, kafin su d'auko komai Ya Auwal ya sunkuceta yana tambayar inane room en
Bin bayansa tayi, Maman haneep suka qarasa, Allah yasa Doctor SMS(zabin wa zanbi) yana cikin asibitin, da gaggawa aka kafa checking nata, hrt break, innalillah
Sosai Doctor Sameer shida Doctor Anee suka hau kanta, check up akayi mata sosai dan saida sukai at least 3 hours akanta sannan suka gano akan abin, saboda drip d'in da doctor Lubie tasaka bai kamata ace ansawa baby kamarta ba
Abinda yayi tunani before, shine saidai baiyi nisa ba, fatansa kada Allah yasa ka abin yayi worst, amma abin mamaki yarinyar dabatafi 15 years ba ace tana tunani har haka, kuma har yakai yana barazana da lafiyarta, how comes
Wata zuciyar ce tace ikon Allah, shidai abin ya bashi mamaki ganin inda jininta ya hau har yakai 170, kuma ga Ulcer data kamata sosai yaji tausayin yarinyar ganinta very simple nd Innocent amma tanada matsala irin haka
Kamata ace irin budurwanan ce take cikin wanga Conditions d'in(kamar Anker) amma ba baby irin haka ba, amma wannan yarinyar tunanin mai zatayi, da zaikaita ga shiga hali irin haka?
Allurai Doctor Anee tayimata tareda taimakon Dr Mrs Jawaheer, sannan suka samata drip wanda yayi containing food ciki, tunda zata iya kaiwa 10 to 11 hours bata farkaba
Ganin komai yayi normal, yasaka Doctor Sameer fitowa wajan wad'anda suka kata
Suna zaune a reception sunyi jugum, Malam dai casbaha yake ja, Inna kuma kanta a qasa yake da alama kuka take
Ya Auwal ne dai yake ta zagaye awajan ganin fitowarsa yasaka yai saurin zuwa wajansa, Doctor ..., kafin yace wani abu, Sameer yace biyoni, haka ya bishi abaya
Kujera ya nunamasa, hav a seat, zama yayi, musabaha sukai, suka d'an gaisa, kirr wayan Ya Auwal tayi ringing, excuse plx ma wife, noo pick it
D'auka yayi, Aysha ce, gaisheshi tayi, tayimasa yame jiki, da sauqi Aysha kin dawo gida?, dan bazan samu chance ba zuwa d'aukanki ba
Bandawo ba, yanzu dai nake shiri, nace bara naji ko zaka dawo gida, huum kinjiki abinda ko ina gari indai kikaje gidan qawayenki bakison komawa gida
Dariya tayi tace, haba wallahi ba haka ba, kasan Jabo nada ciki, shiyasa nad'an kamata wani abun, Bena bata nan ta tafi Abuja gida, kuma kasan sunada kirki, nima suna zuwa hardare suke kaiwa
Huum, ainasan yanzu zaki shigarwa qawarki Jabo komai akayi Jabo Adda, to ai sunada kirki kuma mutane ne na qwarai ba hayaniya bare kace nace
To naji, saina dawo, kitayamu da addu'a, ZAHRA nacikin matsala har muka tawo daga gida muka kata, bata motsi
Sosai ta jajan tamasa, haka sukayi sallama ya mayar da wayar aljihu
Juyowa yayi, ya fuskanci Doctor, d'an kallonsa Doctor Sameer yayi, yace hala da matarka kake waya, kai ya kad'a yace eh, mata tace
OK "naji kamar kana magana kace Jabo da Benaxir?, eh qawayen mata nane, sunada kirki yanxu haka tana gidan, narasa irinta indai taje kamar bazata dawo ba
[08/10 6:52 pm] @ut@r h@jiy@💅🏻✍Dariya yayi, yace indai ba suna yazo d'aya ba, da nace mata nane, haba?, wallahi kuwa kai ya sunan matar taka?, Aysha Chuchu
Wallahi itace, ai qawarsuce sosai, yanxu dana fito nabarta gidan, kasan mai d'akin nawa bata jin dad'i, ayya haka tace mun yanxu ma Ayshan, d'an hira suka tab'a sannan Sameer yace let back to our business yallab'ai
Tambayarsa yafara, ya yakeda mara lafiyan, sister nace Auwal yace, ok gaskiya tana cikin had'ari, indai bawai Allah ya d'oramata ba, to tana tunanin wani abu, then ga ulcer data kamata, at her age baici ace tanada wannan matsalanta
Idan wani abu take so, best solution abata, idan kuma wani abune bataso to gaskiya abari, idan ba haka ba, to da matsala, yarinyace matsalanta zaiyi saurin kaucewa Idan har anyimata abinda take so
Abun baiyi worst ba, amma idan ba ayimata abinda take so, gaskiya zaiyi iya shafar xuciyar ta, ada nayi tunanin ciwan zuciyane ganin yadda abin yake, saidanayi checking sosai nagane bashi bane, amma adaure ayinata yanda take so
Idan alewa aka hanata to abata, ko kuma Shiga ruwa wasa ko ma menene adaure asamo mafita, xata dena wataran
Ajiyar xuciya ya Auwal ya sauke yace masifa sabuwa, ana wata ga wata, me ZAHRAN BABA ke so, kome ke damunta har take tunani haka?, bashida answer ko d'aya shiyasa yayi shiru
Ganin kamar hankalinsa ya tashi, yasaka Doctor dafa shoulder nasa, yace Calm down ma friend ix not serious abu fa, indai anmata abinta take bid'a, no more ciwo, adai daure, haka yayi ta bashi baki har ya sauko
Inna da Malam suna zaune, akan kujera, suna bid'ar fitowar Auwal
Suna ganin fitowarsa, suka miqe Auwal yayah? bai iya fad'amusu abinda ke damunta ba, yace dai Ulcer tayimata kamu sosai, sai d'an rashin bacci dayake damunta
Inna harda qarawa miya maggi, wallahi hakane dan tunda *Mahmoud* yatafi yarinyar nan, aka rasa gane kanta, abinci tamasa qaura, sai d'an banzan tunani, haka sukayita maganganu har wajan asubah
Sai wajan asubah ta farka, 4 da sunan *Maikyau* abinta, tana cewa kada yabari Malam yamata auren dabatasan mutum ba, bud'e Idanta tayi, sai ganin Baba tayi shida Inna a tsaye, komawa tayi ta kwanta
Matsawa Malam yayi kusa da ita, ya kama hannunta yace ZAHRAN BABA me yake damunki, ko me kike so, ko abincin da akene baki so?, kin d'agamun hankali eye ZAHRA?
Hawaye tafara tace Malam nima bansani ba, kawai jinake bansan cin komai, ko naji yinwa idan nazubo saina kasa, kuma sai nan ta nuna qirjinta tace saiyayitamun ciwo da zafi, kaina kuma saiya kama ciwo
Komai akayi sainajishi cikin kaina, ga bacci da banyi, kona kwanta
Innalillah " yaushe ZAHRA tadena fad'an damuwarta, ko Innar ku ai saiki fad'awa, tun yaushe rabon da kiyi bacci?
Tun randa *Uncle Maikyau* ya tafi, nadena kuma sainayi ta jinasa nan, xuciyarta ta nuna,kuma sai yayita zuwa mun a bacci
Dan Allah Baba kada kace zakamun aure da wani Anas, *Uncle Maikyau* yace nayi karatu kuma kada na kula samari, Ilimi garkuwar d'an Adam, kuma ilimin mace kamar duniya keda shi
Naji ZAHRA, zakiyi karatu, fatana kiringa cin abinci, tunda ance gyambon ciki ke damunki, kuma ki ringa bacci, tunda kince da ciwan kai, ki dena tunani, idan kindena kan zaidena ciwo kinji Dariyar Malam
Tom tace, haka sukayi ta hira da nishad'i harta ware akafara da ita
By
@ut@r h@jiy@

ZAHRAN BABA (Completed)🌹Onde histórias criam vida. Descubra agora