1

6.5K 208 2
                                    

Salam masoyana fatan khairan ko yaushe,  ina mai baku hakuri da cin karo da errors da spelling mistakes da zakuyi. Hakan ya samo asali ne da shi wannan littafin ba sabo bane, yanacikin tsoffin books ena, ba editing sosai fatan zaku fahimce ni. Love ❤️ u oll ana tare.

  Garin gaya, garine mai cike da tarihi, wanda yake a k'ark'ashin jihar kano, garine wanda ake kasuwanci sosai, kuma ilimi na addine shine gaba, duk da basu damu da na boko ba, amma zaka same su, cikin wayewa
Kowa yasan, Gaya ba mummuna, garine kuma, mai d'unbin tarihi, wanda Mutanen cikin garin kowa yasan mutane ne na gari, masu wadatar zuciya
K'auyene mai cike da, kyau, balantana yanayin damina, ko ina ka duba zaka sameshi garai garai ga ciyayi koraye, ga kayan gona duk sunyi, rayuwar mutanen abin sha'awa ce sosai
Malam Aminu, shine babban malami, acikin garin, kuma yakasance babban liman na fad'in garin na Gaya, yanada almajirai da yawa, saboda shahararsa hardaga k'etare na k'asa ana kamasa yara
Mutum nai mai kirki, kuma dattijon arzik'i, bafulatanine, farine tas, da farin gemun sa, Malami mai almajirai, kusan a k'asar Hausa, zaka samesu al Qur'an, kawai su keda ilminsa
Amma, Malam ilmin Qur'an, fiqh, Tauheed duka ya had'a, da safe ana karatun al'Quran, da yamma kuma sai ayi na, Fiqhu da Tauheed
Malam bashi kad'ai yake karantar dasu ba, akwai d'aliban da ya yaye, wad'anda ayanzu su suke taimaka masa, tareda manyan 'yayansa
Malam yanada Matan aure guda 4, uwar gida gwaggo Aneesa, sai ta biyu Inna Nafee, sai ta uku, Iya Hauwa, sai k"aramar cikin su Yafando Aisha
Uwar gida, tanada yara 6 Maza biyar sai mace d'aya, ta biyun tanada yara 5, Maza biyu, mata uku, sai ta uku, tanada yara biyar 5 Maza biyu itama mata uku
Sai Amarya wadda, takasance itama bafulatana ce, a yola malam ya aure ta, takasance 'yar babban liman nagarin yola
Bazawara ya aureta, tayi auren fari, Allah yayiwa mijin rasuwa, lokacin da malam yaje yola, anan ya ganta, kuma ya nuna sha'awar aurenta, Aka bashi ita
Matan malam matane nagartattu, babu wanda ya tab'a jin Kansu, kuma malam a tsaye yake akan iyalansa
Babu raini ga k'anana akan manya, kuma manya babu raini ga Matan mahaifin su, idan har bakasan 'ya'yan kowacce ba, bazaka tantance kace ga d'an wannan d'akin ba
Malam ya kasance mutum attajiri, ko almajiransa, basa bara, saboda sune suke masa aikin gona, shikuma yasakamusu da abinda zasu ci(sab'anin malaman yanxu, da almajirai suke musu komai, amma lomar abinci basa basu)
Madafar gidan malam babbar madafa ce, mace guda d'aya aka d'auka don taringa yiwa almajiran Malam abinci,
Amma, abincin gidan, yaran malam suke yi, tarbiyyar gidan, ni kaina tana burgeni
Amaryar malam saidata shafe, shekara uku gidan, malam kafin ta haihu, babu wadda tayimata gori, akan komai
Aisha ta kasance kyakyaawar gaske, duk da Matan malam ba mummuna aciki, amma Aysha ta daban ce, tana sana'ar kayan k'amshi, kama daga humrah, turaren jiki, turaren kaya, gishirin wankaTuraren wuta, shiyasa gidan malam kullum zaka jishi cikin gidan malam
Yaran malam maza, daga secondary suke gamawa, mata kuma daga primary, iyalan malam dai sai san barka
Lokacin data fuskanci tanada ciki, bak'aramar murna tayi ba, gidan baki d'aya saida suka kasance cikin murna
Malam ya aurar da yara uku mata, kuma masha Allah suna zaune lafiya gidan maxajensu, dan kowacce gidan rufin asiri take
K'aidar Malam shine yake zab'arwa yaransa Mazaje, suma Mazan shine yake musu zab'i, harda almajiran sa, da suka isa aure
Malam cikin, iyalansa yanada sakewa, amma kuma ana shakkarsa, duk wasansa da kai, indai wajan karatune to zai dokeka kamar jaki, shiyasa yaran malam da d'alibansa, suke daban koda cikin wata jihar ne daban
Yafendo Aysha, amaryar Malam, Allah ya sauketa lafiya inda Allah ya azurtata da samun d'iya mace, wadda ta kasance hasken gidan malam
Babu wanda baiyi murna da samun k'aruwar ba, balantana daya kasance duk ba yara agidan, duk sunzama yammata, shiyasa kowa yake murna
Malam kansa, idan kaga bakinsa baya rufuwa, saboda murna, yarinya tuntana jaririya kowa saiya fad'i kyanta, ga gashi kamar ba'yar Fulani ba
Yarinya taci sunan ZAHRA, malam da kansa yasamata suna, Dan bashi yake sawa yaransa suna ba, Amininsane Mai gari, shine yake rad'awa yaran malam suna
Amma wannan karan, Malam da kansa, yasawa 'yarsa suna, duk haihuwar da ake gidan malam, yara basa liyafa, amma saboda murnar haihuwar ZAHRA, malam da kansa yabada kud'in liyafa
Yarinya ta taso, cikin gata, harara Malam bai bari ayimata, wanka idan bataso to kuwa baza'ayi ba, tunda ta iya magana, take cewa Malam BABA, sunan sa shi tafara iyawa kafin na kowa
Tun tasowarta, ta taso da rigima ga tsiwa, amma malam bai bari adaketa, wataran yakance yarinta ce, zata dena
A k'aidar Malam, yaro tunyana shan mama, ake fita dashi makaranta, amma gashi ZAHRA hartayi shekara biyar bata fara zuwa ba, indai taje, to dan kanta taje amma badai a tafi da ita ba
Sosai Yafendo bata son sangartar da ake mata agidan amma yata iya, haka ta hk'ura ta zuba ido
Wataran agidan, girkin Inna ne, angama dafa abinci, sauran miya itama angama ansauke, ZAHRA tana zuwa, muciya tasaka tayita tura tukunyar miyar harta kife, aikuwa tasha duka wajan Mamanta
Dalilin dayasaka ta koma d'akin Inna da zama
Babban d'an Malam, ya Auwal shi kad'ai take tsoro, shikuma Allah cikin ikonsa bayan k'are secondary school nasa, wani abokin malam yasamarmasa makaranta a kano, FCE anan yayi NCE d'insa, har degree a BUK
Bayan k'arewarsa, yasamamasa aiki, a banki, yanxu haka yana zaune a kano, amatsayin cooperation Manager na GT Bank, tunyana matsayin Marketer, har yakai matsayin dashi kebada ATM, gashi yanzu yakai stage d'in co-operation manager
Indai kaji ZAHRA tayi shiru agida, ya Auwal na nan, ko motsi batayi indai yana wajan, shikuma yana mata Hakane d'anta gyaru, amma a ganinsa ba wanda ya kaishi k'aunar 'yar uwarsa yana sonta sosai
Duk da ZAHRA kamanin Mamanta tayi, amma daga KA ganta kaga Malam, kuma kaga ya Auwal, kowa na mamakin kamanin ta, tayi kama da babanta tayi kama da Mamanta
Yanzu kusan rabin gidan, sundaina cewa Malam, Malam, sai Baba, shiyasa ake karanta da ZAHRAN BABA, tunda ita takawo canji
   Tafi tafi, gashi ZAHRA tanada shekara bakwai a yanxu, idan kaganta bakace 'yar k'auye bace, saboda kaya daidai gwargwado malam nayi wa iyalansa, balantana kuma ZAHRAN shi
Yanzu su ya Sani, sune agida, babu mai tab'ata, shiyasa ba'ajin Kansu, amma indai akace Ya Auwal yazo gari, to karinga jin maganar malam kenan, su 'yan gida dariya ce tasu
ZAHRA batason makaranta, duk da yanxu tana PRI 2 amma, duk dahaka, wataran sai ance ga ya Auwal sannan zata tafi
Makarantar Malam kuwa, saita ga dama, amma wani ikon Allah idan kaji yadda take fidda karatu, kuma da k'ira'a mai dad'i, bazaka ce wannan ZAHRA'N bace, na boko ma, haka take yi, amma fa sai ita kad'ai koda malam xakaji karatunta, indai wanine batayi
'Yan gidan sukance malam yajik'a yabawa 'yarsa, tunda gashi bata zuwa, amma karatu wajanta komai zuwa albarka, shi dariya suke bashi, saidai yace ai indai kunason kuga magajina, to ZAHRA ce, dan babu inda tabarni
Makarantar boko, ba dama, idan taso babu wanda yake jiranta, idan taje kuma, sai inda tazab'a zata zauna, malamai sun Santa,wajan rigimarta, shiyasa ko yara basa zamar ta awaje, ba duka sai cizo
Dan idan tacijeka dole wajan yayi jini, suku ma, 'yan garin basa iya kai k'ara saboda ganin girman malam
Mama, dan Allah kisamun kayan da Yaya Auwalu ya siyamun, kinji? naki, ai d'azu nace kitafi makaranta kika k'i, bazansa ba
Dan Allah Inna, wallahi zani, kuma zan kaiki kano wajan ya Auwal, kuma zan nunamiki gidan matarsa
Au harmata yakeda ita?, eh mana, ran nan yabani muka gaisa, wai tace sunanta Aisha, nida yaya Rabi yabamu fa, (yar wajan gwago ce, k'anwarsa wadda suke uwa d'aya)
Lallai kice harbaku yayi?, eh mana, kinga idan ki kasan to zan kaiki wajanta, ba yadda ta iya haka tasamata kayan
Fita tayi, bata zarce ko ina ba, sai gidan maigari, wajan matarsa, Inna fito gida nima zanzama 'yar gayu, ya Auwal ya siyamun, kuma ance tayimun kyau, idan kema kince tayi, to saikiban alewar da wannan 'yar gayun take baki, idan tazo
Wayyo ZAHRAN Baba, irin wannan magana haka ba tsayawa, aisai ki kashen kunne
Ni, kuma Allah ko kiyashi ban kashewa, nifa ko kunama nagani ban kasheta, bare kunnanki, nasan dan kada kiban alewar ne?, bara naje gun baba mai gari
Kamo hannunta tayi, tace haba jikalle, ragowar hanjin Malam, ni na isa nahana dariyar Malam alewa?( malam baidariya sosai, amma tun Bayan haihuwar ZAHRA, yazama kamar mai tallan Maclean, wajan dariya) shiyasa take cewa dariyar Malam
Zunb'uro baki tayi tace, Allah ni wajan baba zani, amma idan kinban wayar ki sai na zauna? Huum yana iya
Haka tayi zamanta gidan mai gari, ba taje makarantar ba
Bikin Yaya Rabi da Amina, xa'ayi wad'anda sune dama ragowar yaran malam wad'anda ba'aiwa aure ba, saikuma Aliya, ita bikinta sai wani ranin
Ya Auwal shine yasiyo komai, a kano na bikin, kayan kitchen dubu Saba'in malam yabayarwa ko wacce, bajinta da halin girma dai za'a nuna
Su ZAHRA, sai rawar kai, za'ayi biki, itada Zainab yar gidan 'yar Inna, jikar gidan kenan, itace k'awar ta, sai khadeeja, ita khadeeja jikace, agidan mai gari
Duk inda zaka gansu tare, fitinar su d'aya, abinda suka fita shine, rashin kunya da fad'a, dan batada fad'a indai ba'an tab'o taba, tanada girmama nagaba da ita, zagi shima bata iyaba, dan gidansu ba'ayi kuma tasan halin malam idan yaji kana zagi
Allah ya isa ta tab'a yiwa, wani almajirin Malam, ai aranar da kyar aka kwaceta shiyasa kwata kwata bata zagi
Barta da tsiwa, da mirgud'a baki, sai kuma rashin zuwa makaranta
Biki yazo, shagulgula aka sha, ba kad'an ba, idan kaga ZAHRA alokacin kamar wata babbar budurwa saboda, yanda take kwainane, da shiga cikin manya
K'auyensu mai kyaune, dan yaune za'ayi bikin girbe kwanya, ma'ana, zasu girbe kowacce kwanya acikin sa'a guda, wanda ya girbe shine jarumin shekara
Dan haka, tunsafe samari na cikin garin, kowa kagani cikin shiri yake, saboda manyan gari, kaya kud'i Shanu, haka ake had'awa kowa, kuma acikin wani biki a garin, aciki ne, ake samawa budurwa saurayi
Idan anbata shi, saiwata shekara ayi biki, dan haka, 'yammata da samari ko wacce tayi shirin ta, ZAHRA ana sawun gaba
Dan yau shigar fulani kowa, yake, kuma kowacce da kwarya cikinta Nono ne, ana gasa, kukuma kunasha
Saboda tsawan lokacin da ake d'auka a wajan
Ya Auwal yazo, tare dashi malam yace za'ayi, hankali sa atashe yake, saboda shi akwai wadda yake so, kuma itama tana son sa
Dan haka, gurin Amarya malam yaje, Allah Annabi ta taimakeshi Malam yabar wannan gasar dashi, acireshi, da wadda yake so
Malam tasamu tayiwa magana, amma yak'i, yace kamar yadda akayiwa sauran shima haka, za'ayi masa
Sosai yaringa bin matan gidan, amma ko wacce saitace bazata iya zuwa ba, hankalinsa duk yabi ya tashi, yarasa yadda zaiyi haka shima yashirya yaje wajan
Fadawan mai gari, suke kiran samarin gasa, haka aka fara kiran na farko, na biyu na ukuuuuu, Au....
To shin ya Auwal ne ko wanine daban
:ZAHRAN BABA
®NWA
©Zainab Y Hussain
Dedicated to Queen Meemi nd Baby Huda
page 5-6
Audu sunan da aka kira kenan, Ya Auwal kansane ya kwance azuciyarsa yace, kenan yanzu mutum hud'u ake gasar, Malam ka kasheni, bansan yazanyiwa Aisha, tabbas yaudara zatace nazo da ita, ya ilah
Jin anyi shiru da kiran 'yan gasa, yasa ka Ya Auwal juyawa, yaga Malam bai gurin, dama baya zuwa, Amma mai gari shine yake fidda gwani ma
Hagunsa ya duba, da dama baiga idon kowa akansa ba, me hakan ke nufi?
Ko anyi mantuwa ne, amma kuma Malam ai indai yace abu, baya canjawa, ko yaji maganar Amarya?, amma ai yace bazai canja ba
Daman sa ya duba, babu kowa wanda yadanganci Matan malam wajan, tun asali basa zuwa, shifa yashiga shock
Hannunsa yaji amkama, dubawa yayi, sai ganin ZAHRAN Baba, yayi tana dariya, tace Yaya u ar shock koh? da sauri yace ZAHRA said again wht u said, k'ara fad'a tayi, Huum,who teach u hw to speak eng? my teacher, u think I'm nor undstnd Eng bah?, shi gaba d'aya ZAHRA ta d'auremasa kai, jin yadda take pronunciation na Eng good
Yaya, naji lokacin da kakewa inna magana, tace wa Baba wai kada yasaka a masu gasar, danaji tace bazata ba, shine naje
Nace Baba, dan Allah kacire Yaya amasu gasar, tunda yace baya so, kuma shi yanada mata, nace kabani mun gaisa
Shine yace wai kaine ka aikoni?, nace a'a naga dai kamar bakada lafiya, shine yace indai yace bakai, zanyi murna? Nace eh
Da safe, da kansa yace naje nakiramasa Audu, nagidan sarkin noma, bansan maganar da sukayi ba, nagaidai yafito yana murna
Shine fa, bakaji sunan kaba, da tuni nasan Marka ta gidan malam mai qula quzai za'a baka, bakinta ya murd'e yace, bak'in fata ba kyau
Da confidence nasa, ya zauna a wajan, yana kallon yanda suke ta girbewa, wai yanzu da ina cikin uwar ranar nan, Allah ya rufan asiri
Haka akayi gasa, aka gama, Audu wanda yazo daga baya shi yaci, sosai guri ya d'auki sowa
Ansha shagalin biki, anan garin dai, amaren suka tare, kowacce gidanta mai kyau, kamar cikin birni
Amarya yau zata yola, gidan iyayen ta, shiyasa tunda asubah dasuka tashi, basu koma ba, tare da ZAHRA za'a, shiyasa taketa d'okin, zataje wajan Feenat k'awarta
Malam da kansa, ya rakasu tasha, tareda rakiyar Ya Salisu wanda, ya kasance yana aiki a jigawa, a k'aramar hukumar kafin Hausa, yana aiki acikin secteria, matsayin PA na ES
Yanada Mota, shine ya d'auko su zuwa cikin tashar garin
ZAHRA kamar ta koma, itadai Malam ya tawo su tafi, da kyar ta hak'ura, mota taja, sai Adamawa Yola
Tafiyar nine hours cikakkiya, ta kaisu garin na yola, daga nan mota suka tara zuwa, cikin unguwarsu
Dangi sunyi murna da zuwan ta, saboda Aisha macece mai kirki, duk da ba mahaifiyarta agidan amma bata tab'a yimusu wani abu na rashin kyautawa ba
ZAHRA anga gari, sai yawo daga nan sai can, lokacin makaranta haka kowa zai tafi, ita tana zaune, sanin halunta yasaka bawanda yake mata magana, indai kace ZAHRA makaranta, to yini zatayi tana kuka, shiyasa ba'ayimata magana
Amma Indai yaran suka dawo, to tabbas indai har sunyi karatu taji, shi kenan ya zauna
Feenat budurwa ce sosai, amma dayake tana ririta ZAHRA kuma tana biyemata, shiyasa take d'aukanta k'awarta
Lokacin dasuka zo, bata nan, yanxu kuma ta dawo, itace kad'ai mai sata taje makaranta, ita d'inma sai in a ajinsu zata zauna
Kwanan su goma sha biyu yau, shiyasa suke shiri tun yau, kafin jibi tayi sukama hanya
Feenat ce, ta d'auketa sukaje makaranta, kowa da al Qur'an ninsa, wasu ne su uku kawai basu dashi, kuma kowa karatu ake yake biyawa one by one
Ana zuwa kan ta farko, malamin yace ina Qur'an naki? K'asa tayi da kanta tace, Malam bana d'auka, haka kayi tayi harkan ta ukun, gani tayi baicemusu komai ba, amma ya akai wasu da Qur'an a hannun su, aka dakesu
Ko Feenat k'awarta, itama tanada Qur'an amma aka daketa, aukuwa saita kama murna lallai idan kace baka d'auka babu mai dukanka
Take sai ta tuno, ya Rabi, wataran batada Qur'an, Malam bai doketa ba, amma ya daki Ya Habee
Har aka tashi tana tuna wannan abin
Masha Allah tafiya tayi kyau, dan gashi, har sun dawo gida, suna hutawa
Yanzu ZAHRA tana aji biyar, kuma a yanxu take cikin shekara Goma sha hud'u, babu abinda ya sauya daga abinda take
Matar mai gari ma, sangarta ta take, kamar me, yanxu wataran ma agidan take kwana, zumunci mai k'arfine tsakanin iyalan Baba Malam da gidan maigari
Kowa ka gani, cikin garin, sabgarsa yake, yara cike agidan ko wanne, saboda yajin aikin da aka tafi, natsawan wata shida, shiyasa yara sukayi yawa
ZAHRA! ina wannan wanda muka gani, a photo gidan Baba Maigari? eh ZAHRA tace, yauwa shine yazo awata jibgegiyar Mota, wallahi irin na kallon da muke, ja dashi, dan yafi tumaturin Baba jaa, kinsan me,? Kinga yimun shiru, haka kawai ina karatu zaki daman, kince kinganshi, amma bakice da jaka kika ganshi ba, ya za'ayi na kulaki
Heeey, wallahi jakunkuna sunfi goma naganshi da ita, Fadawan mai gari su suka ida shigarwa, babbar jakar ma alewa ce cikinta, har zubewa tayi aka fara wawaso
Kinga wadda na samo, wai ZAHRA najin alewa, ai bata k'ara minti d'aya ba, tayi gaba
Da gudunta, ta shiga gidan, tana Inna wai kinyi bak'o?, mairo tace har alewa ya zubar aka d'iba, ni baki kirani ba?
Dariyar Malam, nima bansan da zuwan saba, kuma bansan ya zubar da alewa ba
Shigo wa tayi, ai da gudu ta koma bayan Inna, wai inna ashe ana ganin aljani, afili, wallahi ina shigowa aljani nagani, dashi nafara cin karo, waih, tab Allah yasoni, dana shiga garari
Duk maganar da take yi, idonta arufe yake kuma batabar jikin Inna ba, dariya inna tayi, tace ZAHRA shi aljani ai ba'a ganinsa, kum......wallahi Inna nagani, Fari fah, Allah nadena zama akan kujerar ki, akanta yake
Bud'e Idanta tayi, aikuwa idansa fes akanta, Ihuu tasaka, wallahi Inna yana nan, kallona yake idansa kamar mage, kuka tafara sosai
Juyo da ita Inna tayi, tace kinga ZAHRA bud'e Idanki, babu komai, tashi ki nunan aljanin, haka ta tashi amma jikinta bai bar, mazari ba, a hankali take takawa har taje inda yake
Tab'a fuskarsa tayi da hannunta, tace Inna wallahi gashi har fuskarsa na tab'a, laushi tafada sai dariya, sosai Inna ta dara tace, jikanane aljani koh ZAHRA?
To bazai baki alewar ba, tunda kince masa aljani
Da sauri ta bud'a Idanta tace, Inna da gaske wannan jikankine, amma irinsu ake nunawa a TV wallahi, kuma Gwagwo tace wai turawa aljanune, shiyasa nace aljani
Gurin sa taje a hankali, ta tab'a hannun sa, saita koma baya, ahaka batasan lokacin data zauna a kusa dashi ba
Kanajin Hausa tace? Kai ya kad'a mata, alamar eh
Dariya yayi mata, sai kuwa taga wani had'add'an dimple a gefen fuskar sa
Da gudu ta kwasa, tamanta maganar alewa, sai waje, jama'a jama'a kiransu tafara, kafin kace me, saiga mutane
Jama'a naga jikan Inna, kuma wallahi har dariya yamun, fuskarsa ta lob'a, watace tace kema ai fuskarki tana lob'awa
Labari tafara basu, ganin motar ya Auwal tasaka tai saurin tafiya zuwa gidan su
Tasan halin sa, bayason yaganta a waje, ko tana wasa
@ut@r h@jiy@

ZAHRAN BABA (Completed)🌹Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang