Lokacin da ya Auwal ya shigo tana zaune idanta nakan k'ofa amma totally hankalinta baya wajan, ta tafi wani tunanin daban, bayan fitar su, Inna da Malam danyin sallahr subhi, shi yayi tasa
Har ya rufe qofar ya tawo inda take bata jiba, sai daya tab'ata sannan ta yi firgigit ta dawo hankalinta, dariya tayi ganin shine tace Allah ya Auwal kaban tsoro nazata wani abunne
Kallonta yayi, tausayi take bashi, ganin yanda tayi wata rama kamar ba 'yar lukutar qanwar sa, indai har zuciyarsa ta fad'a masa dai dai, to ba shakka ZAHRA she's in deeply loving with Maikyau shida girman sa, baiyi irin wannan son ba, amma gashi ya kamamasa tilon qanwar sa daya keji da ita
Ada yayi tunanin cewa Mahmoud yana son ZAHRA amma ganin basu yi matching ba yasaka wa zuciyarsa Salama, kuma da lokacin yaji maganar komawarsa gida, yaga baice komai ba, akan ZAHRA yasa aransa dama had'uwar jini ce kawai, then Mahmoud yafi k'arfin villager like ZAHRA wadda batayi wani dogon karatu ba, batada ilimin da mutum kamar Mahmoud zai sota
Amma asan ransa yaso ZAHRA tayi karatu koda secondary ne, amma bashida wanga ikon akan haka, tunda k'aidar Malam ce
Yaya!Yaya! Ajiyar zuciya ya sauke ahankali ya goge hawayen fuskarsa, dan kada tagani, yace ZAHRA ya jiki?, na shigo na fad'a wani tunani na daban
Da sauqi Yaya, kafad'anta
ya kama a hankali,murya a tausashe yace ZAHRA me yake damunki kome kike so, kome baki so? Fad'a mun kinji kinsan Illar tunani kuwa, kikeyi
Ni kawai kacewa Maikyau ya dawo, nagaji da rashin ganin sa, kuma kace inata jiransa zanyi karatun, amma Baba yace aure zaimun, kuma Maikyau yace fa nayi karatu
What ZAHRA yaushe baban yace zaimiki aure, dama baba baibar wannan halin ba, baisan kai ya Waye ba, ya Ilah
a gida ya fad'i wai nan da 2 month za'ayi nida Anas d'an gidan Sharif , bayan ni banso kace ya bari plx sweet broth save me plx
Aure kamar and'aurashi ZAHRA, bana magana biyu, bazakisaka naqara irin abin kunyar danayi akan Auwal ba, kisa aranki kamar and'aura, ra'ayinane hakan tun fi'azal, kuma haka nayiwa yayunki, lafiyarki ita mukaxo ne ma yanzu ba wannan maganar ba, idan ita kikeso kyabari a koma gida
Kuka tasaka, ita wallahi batason auren, kada bari Malam yamata, ya Auwal ne yace ZAHRA kiyi shiru insha Allah I will know what to do, kamar yanda kika taimakan nasamu Aysha kema zaki samu abinda kike so
Yauwa Yaya kaga Maikyau zaice inada alk'awari tunda banyi aure ba, kuma zan koma school, kai ya kad'a mata
Ni fa Yaya, ko zanyi aure Maikyau zan aura, kaga yanada kirki kuma yanabani komai nake so, kuma ina tunanin sa
Shidai Malam yana tsaye yanajin komai suke cewa, jin Auwal yace sai yasaka anfasa auren, shine Malam yace to Idan ban auramata Anas ba, wazan aurawa, saidai idan bana raye ko ka kasheni
Dariya ya Auwal yai, yace Baba nifa wasa nake mata, dan kada tasaka komai aranta, amma aure kamar and'aura, Yaro nagari mai hankali, wasa nake ahaka akabar maganar
Magani take sha sosai, kuma ya karb'eta, ga Inna da ya Auwal da Aysha matar sa suna kwantar mata da hankali, Inna ma ta gidan Maigari taxo har sau biyu, kuma jin yadda inna tayimata bayani, yasaka itama tasha alwashin insha Allah ZAHRA bazata auri wanda bata soba
Mahmoud da maganar taji ta bakinsa, indai har ya amince zatafi kowa murna da farin ciki, itama rarrashinta tayi, da nunamata Maikyau yana tafe wajan ta
Amma Indai kinacin abinci shine zaixo, kuma indai Malam ko agida idan ankoma yayimiki maganar biki kice to kada kiqara wata maganar, to Inna
A haka suka shafe sati biyu cikin asibitin, tana samun kulawa sosai, dama ulcer da tunani yasaka jikin nata zafi, amma anan tana samun relief ga abinci akai akai datake samu, ga kuma maganar Maikyau da Inna take mata kullum
Sameer yana kula da ita, Ya kawo su Hauwa da Benaxir sun dubata, da abin arxiqin su,
Maganar kud'i ko wani abu, babu dan koda Ya Auwal yace maganar bills, take yace ai shima qanwar sace, saboda haka kyauta akayi musu komai
ZAHRA tasaba da Mrs Jawaheer, Doctor Anee ce sai a hankali, saboda anytime fuskanta ba space na fara'a shiyasa batason tazo yimata allura ko bada magani
Inna bayan ta koma gida, saidatayi ayyukanta, sannan ta janyo waya, sawa tayi aka kamomata number *Mahmoud* ringing buyi tayi yayi hanging nata
Tana katsewa ya bugo, gaisawa sukayi, yad'an tab'a barkwanci sannan Inna ta koma serious, tace *Mahmoud* na'am Inna tsohuwa mai ran qarfe nakusa samo dalma na narka rannanki dariya tai sannan taqara kiran sunan sa
Huum zaki shantakar dani bantambayi, ajiyata ba, tana dai karatun koh?
Ni bansan wata ajiyar ka ba, na bugo nafad'amaka
dama bikin mutuniyarka za'ayi, shine nace bara nafad'a maka
Wace kenan Inna, ban ganeba, *ZAHRAN BABA* mana, aiko bakasami halarta ba, ka aiko danaka guddumawar kodan zaman arxiqin da Ku kayi
Shi ruwan kansane ya tsaya ya dena circulation, me Inna ke nufi, yarinya qarama za'ayiwa aure, ko jss bataje ba, balantana akai kan university(kasan shi malam yarinya na 15 to 16 years ake mata aure, daga tagama primary) kalaman *ZAHRAN SA* suka fara dawo masa, lokacin datake bashi labari
Noooo, Inna I can't take dis, wallahi ni nakeson ZAHRA ba wani ba, kinsan son da nake mata, kin san ji da ita danake Innalillah Inna zan iya jurar komai amma banda rashin ZAHRA
Kanaji da ita katafi baka nemetaba, kanaji da ita ko sau d'aya baka tambayeta ba, kanaji da ita kuma kana sonta, bakayi magana wa manyan kaba, mu anan bama barin yara sukai wani minzali batare da anyi auren suba
Inna wallahi ina sonta, I cant imagine a future without her, she's part of me OMG Inna I have my reasons for not noticing u I love her and not saying kibata muyi magana a waya nasan Indai zanji muryanta bazan iya jurar rashin taba, zan iya tawo wane, kuma muna final exam kinga ba halin tawo wa
Amma wallahi ina kaunar ZAHRA kuma itama tasani, I'm sure ZAHRA loves me too I teach her how to love me , life without Zahra is like staying in the jail till infinity, I thought she will continue her school dats why I decide not to tell her and in my own understanding she's too young nagayamata inasonta..nabari idan tagama na fad'i mata, amma Ina sonta,(Bilkisu Bilyamun) hak'ikanin so( Asmy B Aliyu)
*Nafi kowa kaunar ta, Lafazina, Jikina, Fuskata, kallona, kyautatawa wata wa ZAHRA, ayyukana akanta, they are enough to know I love ZAHRA, I don't know what's love is, and I don't have plan for marriage soon, but for the presence of her I know what's exactly love is, kuma naji ina sha'awa aure, bakina bazai iya fad'ar d'unbin qaunata wa ZAHRAN Maikyau ba
Zahra too she can't do without Maikyau* ninasan ZAHRA kuma nasan darajarta, ki taimakan Inna plx don't let anyone to marry my beloved
Kaga *Mahmoud* indai da gaske kake ba qarya ba, sauran sati biyar zuwa shida, bikinta kazo kaida Iyayenka ba kai kad'ai ba, ni kuma insha Allah zan san yanda zanyi kasamu ZAHRA
Yauwa tnx aloot Inna, zanxo very soon, but not now ooo, coz I hv smthin right now important, nan da 3 to 4 weeks kisa ido, tsarin school d'inmu indai anfara exam to ba'a fitowa ko waye harsai an gama
Kuma final ce, nagama karatun daga wannan shiyasa Inna, kitayani da addu'a
Inayimaka kaida Bintu 'yar uwarka, agaidata, zataji, haka kowa ya ajiye wayar
Inna dai murna take, sosai *Mahmoud* nason ZAHRA kuma insha Allah tasan kamar ya samu ya gama.Who's this Maikyau?
MAHMOUD MOHAMMED AHMAD
D'ane ga Hajiya Jameela wadda ta kasance 'ya wajan Mai gari da Inna, ta kasance yarinya mai hankali batada wani kyau amma Allah yabata baiwar karatu na Qur'an, dana tauheed Tajweed fiqh, (abaya nafadamuku cewa Malam bawai a Qur'an ya tsaya ba, yayi karatun Tajweed Fiqh Tauheed kuma kaf babu Wanda baya koyawa yaransa da d'alubansa)*
Kusan a lokacin kaf cikin fad'in garin Gaya babu mai wadda tayi hadda ta Al Qur'an mai kyau kamar ita, sosai takeda hazaqa, ga bawa Al Qur'an haqqinsa wajan fitar da makharijul Huruuf, inda qalqala take bata wucewa sai tayi, ko gun Iklabi, Ikhfa'i Izhari, Idgami duk tasansu*
Daga kan fiqh, Akhabari, Ishmawi, Izziyya, duk ta iya, kitabu Tajweed Hidayatul mustafeedah ma ba'a magana, Sirah a khulasa ta tsaya saboda daga nan Malam ya tsaya wajan biyamusu*
Kaf yaran Maigari babu mai qoqarinta batada lokacin komai saina karatu, (Warsh, Hafsh) duk alhamdulillah Allah yabata wanga baiwa
A wani lokaci da ya shud'e akayi gasa tsakanin 44 local government na Kano, Gaya saita zab'i Jameela ta wakilcesu
Haka aka tafi cikin garin Kano, a Indo akayi gasar Allah yabawa Jameela sa'a tazo ta d'aya cikin local government d'in
Ba'ayi wata uku ba, akayi ta garuruwa 36 state of 9ja🇳🇬,anan ma Jameela tazo ta biyu, bawai yawan karatu ba, Muryanta da fidda Tajweed yabata, kyauta harsaida tarasa inda zata Saka, kuma harda kujjerar Makkah, Maigari tabawa shi kuma yabawa Inna
Garin na Gaya murna acikin garin su akasami wannan hafiza
Dama k'asa da k'asa aka had'a gasar to shine Nigeria🇳🇬 tafara tantancewa tsakanin garuruwansu, a Sokoto akasami ta d'aya bawata bace illa Zahra BB, sai a Kano garin Gaya akasami ta biyu
A k'aidar garin yarinya batafin shekara 15 -16 akemata aure, amma ita Jameela ba mashunshini ko da Malam yasamo mata ko Mai gari, daga anfara magana sai ta rushe, babu irin baqin cikin da basuyi ba, har suka dangana, lokacin tana da shekara 18 tunda taga haka itama bata tsaya tunani ba, tasan komai Allah keyi koda Qur'an d'in daya bata ta godemasa
Kud'in data samu, sosai akayiwa gidansu gyara duk da Maigari yanada arziqi yaran uku biyun duk maza ne, shiyasa yake San
jameela kamar yadda ZAHRAN BABA take 'yar gida agidan Baba Maigari, haka Jameela take 'yar gida agidan Malam
*Bayan wata 4*
Shahararren malamin nan wanda kowa yasanshi dake garin Kano Hafizin Qur'an *Mahiru Sharif Bala Gabari* shine ya jagoranci zuwa garin gaya dan albishir d'in cewa za'a qara gasa a tsakanin su biyun da suka zo, aciki kuma za'a zab'i ta d'aya wadda zata wakilci Nigeria🇳🇬, sosai Malam da Maigari sukayi Murna saboda wannan wata baiwa ce ta daban
Haka akayi gasa, Allah yabawa Hafsa sa'a tazo ta d'aya, anan akasaka ranar da za'ayi gasar
*OMAN* itace qasar da za'ayi gasar cikinta, kowa kagani wajan taron a nutse yake larabawa India turawa babu Wanda babu baqar fata ma haka
BHaka aka fara cikin hikima da hukunci na Allah Jameela tazo ta biyu a gasar, ada itace ta biyar, amma da kayi musu tambaya a Tajweed itace taci saikuma wajan *TAHLILI* nan ma itace taxi, da wannan abin tasamu sa'ar zuwa ta biyu
Wayyo Murna kowa wajan sai share hawaye yake, saboda yanda bahaushiya ta iya qira'a haka dabawa Qur'an haqqinsa ga murya mai dad'i kamarta *(@ut@r Hajiya, dan itama ba bayaba wajan qira'a mai sweet, ga tausassar Murya ba irinta Maman Bobo ba da Jabo, da Anker*)
A wannan taron da akayi, d'an waziril a'azam min daulatul usmaniyya ta qasar Dubai MOHAMMED AHMAD BASHA, yaga Hafsa yaji ta kwantamasa, yazo wajan saboda mahifinsa waziri bayajin dad'i kunsan dama da Dubai da Oman, kamar Nigeria🇳🇬 da NIGER ne kusa suke*
Anan fa yaji cewa lallai yasamu matar aure
Sun koma gida tareda d'unbin alkhairi, President Gen Murtala Ramat Mohd yaso su dawo garin da zama amma Maigari yace a'a
Hafsa tafito da darajar 9ja, kowa sai d'aukan PIC yake da ita, nima saida aka d'auki selfie dani dan baza'a barni abaya ba
Sosai Mohd yake son Jameela, baisha wahala ba wajan iyayensa daya fad'a musu, saima Murna da sukayi
Anan ya taho Nigeria🇳🇬, a fadar shugaban qasa aka saukeshi.