2

2.4K 107 0
                                    


   Da saurin ta, ta k'arasa gida, maimakon tashiga gidan, saita b'uya bayan k'ofa, lokacin daya shigo harya wuce cikin gida, saiya ji kamar numfashi, itakuma lokacin take fitowa danta koma, yayi daidai da k'arasowarsa
Taku uku yayi, ya cafkota, saboda harta d'aga k'afa zata arce, shine ya cafkota
Kunnenta ya kama, yace waike meyasa bakyaji, bakisan kin fara girma ba, amma kike abu irin na yara, baki ta zob'aro tace, Yaya shekara sha hud'u shine na girma?, kuma ai tunda ba yara agidan dole naringa ganina yarinya
Kuma ai Malam yace, ni yarinyace adena dukana
Dariya tabashi, jin wai ita ta tubure yarinyace
Kuma wai kada adaketa, gintse dariyar sa yayi, yace wayace kifita kuma me kike fad'awa mutanen, ahaka zakice ke yarinya ce, kina rashin ji, kunnen ya murd'e sosai
Hawaye tafara, amma baisaketa ba, kuma ya hana tayi ihu, jin motsin malam datayi, yasaka takurma ihu, wayyo *Baban ZAHRA* kazo kataimakeni, kaceceni wani yazo har zauren gidan mu, yana dukana, wayyo nashiga uku, Inna Gwago, Amarya kufito
Kafin kace me?, har soron ya cika, Malam harda sanda
Wayene, wani mara imanin ne, yarinya k'arama yake jibgarta haka
Ya Auwal shi gaba d'aya kasa komai yayi, kansane ya rik'e, lallai yarinyar nan, dama 'yar sharri CE
Malam daya k'araso, sakin baki yayi, yace lallai wato Kaine, banhanaka dukan taba, da darabon kaciremata kunne, ko ka kashe mata ido
Kwaceta yayi daga hannunsa, yana duba kunnan, ita Amarya takaici yakamata bashiri ta koma gida
Dama gwago da Inna suma 'yan abi yarima ne, suma dai fad'a suka kama masa, tana jikin malam saita dawo jikin Inna
Inna itama harda lailaya mata kunne
Had'a Ido, sukayi da ita, wata harara ya sakarmata
bashiri ta juya
Sosai yarinyar tabashi mamaki da dariya, abinda kad'an ya kama kunnan
Haka suka shiga gida, Malam nata sababi, shida gwago
Ranar dai, bata fita ba, tana gida, kuma bata bari sun had'u ba
Dan koda ya shigo, da gudu tayi d'aki, yana kula da ita, lokacin da suka gama hira da Inna, zai fita Malam ya shigo kiran Inna yayi
Suna fita, yashiga d'akin, ganinta yayi kudundune kan gado, sad'af ya cafko hannunta
Wana kama?, ni tanuna kanta, dariya ya kwashe da ita, yace me yasa kikayimun sharri d'azu?
Wallahi banice ba, bakina ne, kuma ai kaga ban tab'a yimaka ba?,
Kai ya kad'a, amma kinsan idan na k'ara ganinki kinfita wajan magreeba, saina cire bakin ki
Na yadda, tace, kafin me sai hira, nan tafara bashi labarin *Mai kyau* jikan Inna, harda dimples nasa, da Idan mage datace yanada shi
Bata gama bashi labari ba, tajiyo sallamar Mai gari, lek'awa tayi, Idu hud'u sukayi da *Mai kyau*
Da sauri ta k'arasa, tace lah *mai kyau* dama zakazo?, namanta bankarab'i alewa taba, katawomun ita?
A'a, yace, kallonsa tayi tace, kai komai a'a, baka iya Hausa ba, kuma kace ka iya, nidai kaban kaji, Inna bata fad'a maka tana bani ba, wadda wata 'yar gayu idan tazo take bata?
Dariya yayi yace, inajin Hausa like u, nama fiki iyawa, d'azu ina kiranki kika tafi
Tsayawa tayi kallonsa, yanda yake fidda harshen Hausa
   Da gaske, yake ashe ya iya, amma Waya koya masa?, Mamana ita ta koyan, abinda taji yace, au Ashe a fili nayi magana
Ya Auwal ne ya matso suka gaisa, yace tana nan tanabaka wahala da magana koh? murmushi yayi yace, Nooo I like her attitudes, she's nice girl
Sosai suka fara, hira, har Maigari yakira *mai kyau* su gaisa da Malam
Itadai ZAHRA so take yafito yabata alewar ta, tunda yace yana da ita
Ko kafin sufito hartayi bacci rumfar Inna, shima saidaya tambayeta, Inna tace kaganta tayi bacci, ai tayi jiranka, baka fito ba, bacci kuma ya kwasheta
Sallama yayi musu, ya tafi, ya Auwal har kusan rabin gida ya raka su
Koda safiya tayi, dashi ta farka, a bakinta, tana Inna *Mai kyau* bai baki alewa kin ajiye mun ba? bai bani ba
Bata k'ara magana ba, tafito sai gidan Maigari
Tana shiga sallama tayi, Inna ta tarar a bakin k'ofa da mutane 'yan aikin gidan
Hannunta taja, tace Inna jiya *Mai kyau* jiya sai gashi a gidan mu, amma bai tafi da alewa taba, ko mantawa yayi? Itadai Inna dariya tai tace mantawa yayi, amma yaban na ajiye miki
Yauwa, d'akko min, dama wallahi har mafarki nayi, nasha buttermin, Allah yasa wadda tafita dad'i zaki ban
Nidai bansaniba, haka inna ta d'auko mata chocolate masu yawa, harda sabuwar yayi, *Kamara* sosai alewar takeda yawa, babu sallama ta tafi, tunda sweet take so, kuma an bata
Xaman *Maikyau* agarin yamasa dad'i, especially saboda ZAHRA, yarinyar da abin dariya take
Gata da tsokana, duk da ba cikin city suke ba, amma yarinyar akwai wayewa, kuma tanada hankali
Yanzuma sallama tayi, cikin gidan Inna tagani da wata k'anwarta, hira suke gaishesu tayi, bata tsaya ba, tabi hanyar shiga d'akin *mai kyau* Inna ce tace, wato ZAHRA kin mana yaji koh?, ai zai tafi ne, nikuma lokacin zan rama
Dariya tai, tace Inna ai idan zaitafi tare zamu, kuma aiyace ba inda zashi, nan zai zauna
Idanma ya tafi, ai zai dawo, tare zamu zauna, yace mun
Koh, to Allah yasaka, K'anwar Inna ce, tace wallahi yarinyar nan tana ban sha'awa, gata tsaf tsaf, wallahi kuwa, ai duk gidan ko nace garin nan, babu mai kyawawan halayenta gata dai yar ficika da ita
Sallamu alaikum *mai kyau* yana nan, ko bo baya nan?, baya nan, indai ba ZAHRAN BABA ke neman saba, shiga tayi, zama tayi tace, jiya shine katafi baka fad'an ba?, kasan ina jiranka koh
Sorry, baby na, mantawa nayi, lalala wace baby?, Ya Auwal yace na girma, kuma ai yara ake cewa baby
Hum, nidai baby zan riga cewa, haka suka sha hirar su, harda labarin garinsu ya bata, to *Maikyau* agarinku, duka irinsu d'aya damasu wannan ramin a kumatu?(dimples taje nufi),
Hhhh, kowa kamar sa daban, ZAHRA kuma dimples ake cewa, ba rami ba, kema aikinadashi, yafi nawa kyau ma
Allah ni bandashi, kaga niba *maikyau* kuma nan k'auyene ba irin garin kuba, yaza'ayi wani abu nawa yafi naka kyau?
Lallai ZAHRA, ke ai kinada kyau, gaki da wushirya, mai kyau, idan kin zama babba zakifi haka kyau ma, sannan kin gama karatu
Lah, ai Baba baya bari a cigaba, aure yakeyi wa yara,
Yauwa dama inason tambayar ki, naga bakya zuwa makaranta, me yasa, kusan yaran garin ma basa zuwa?
Munyi commen, shiyasa kaga bana zuwa, ok ai naga anyi resuming schools, meyasa bakya tafiya?, ai antafi strike kuma bamusan ranar dawowa ba
Too, tunyaushe aka tafi?, wajan wata biyu fah yanxu, kai amma ba'ayi magana ba, zansami Baba Maigari idan ya amince, yaran ki fad'a musu, kowa tasiyo littafi da pencil zan runvae yimuku lesson, amma zaman haka ba amfani
Yauwa, *Mai kyau* Allah yayimaka albarka, yanzu inason karatu, tunda kace yanada amfani, kuma zan fad'a musu, amma dai bazaka ringa duka ba?
Eh idan mutum ya iya, baxanyi ba, Amma idan ka iya, baruwana da du kanka, haka suka yi ta hirarsu
sannan yafara koyamata karatu, sai wajan magreeb sannan tace zata ta koma gida Tom, ZAHRA sai gobe, koh idan kin fad'a musu
Tashi tayi, shima mik'ewa yayi dan yin alwala, harzata fita saita dawo, tace yauba sweet?
Dariya yai,yace ZAHRA kullum saikinsha sweet, yara ne sukesha, ainima yarinyace, ohoo! amma d'azu kikace kin girma?, eh ai idan gurin shan alewa ne, to yarinya ce ni
Amma, idan ba anan ba, to I'm big girl lyk Adda Bena, dariya yai sosai yadda take juyi wai ita budurwa
*Kamara* ya d'auko mata, da *Galaxy* yabata, b'arewa tayi, tafara sha wow so sweet, shanta tayi harta gama, tana d'ago Idanta taga gaba d'aya yabada attention nasa kanta, kallonsa take, amma baisan tagama ba
Wani irin feeling da baisan irinsa ba, yakeji akan ZAHRAN Baba,
D'ankwalinta ta cire da jefamasa tace, irin wannan kallo haka, dawani idan ka, kada ka cinyeni
D'ankwalin data jefamasa, maimakon yaji warin gashi, sai wani k'amshi ne ya buge shi, mai dad'i, (kunsan dama Amarya tana siyar da turare, harna kai) shiyasa ZAHRA bata rabo da k'amshi
Rik'e d'ankwalin yayi, ya kalleta yace ZAHRA nikoh? zan rama dariya tamasa ta tafi
Koda Inna ta tambayeta ina fatalarta, sai cewa tayi aida hijabi tazo, itama bankwana sukayi ta tafi
*Maikyau* baisan lokacin da ya bud'e akwatunsa ba, ya jefa d'ankwalin, harda bashi sumba guda, fuskarsa sake, yana son ZAHRA
@ut@r h@jiy@

ZAHRAN BABA (Completed)🌹Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang