7

1.7K 77 0
                                    


   Haka ya kasance yana karatun sa cikin kwanciyar hankali na jami'ar ta madina, sosai yake ziyarar d'akin Allah, (sab'anin wasu da saisu shekara basuyi ba)
Qanwarsa kusan kullum sai yayi waya, ansamata breath nata kawai zaiji, amma murna yake, yana son yara, baran dayaga suna kama, duk da waccen Bintun da Mama take kama, ita wannan da Abbee take kama
   Rayuwa tayimusu dadi, wataran d'aci wataran mad'aci, amma dai farin cikin yafi yawa, tunda sunsan daraja da qimar Kansu
Karatun sa yafara a sa'a kuma ya qare a sa'a, sai fatan amfani da abinda akaji, kuma aka karanta
Lokacin daya dawo gida, baby tayi girma, tafara rarrafe, dariya abakinta kamar gonar auduga, amma ba tayi cunkus kamar fuskar Jabo ba
    Tun da ya dawo, a gunsa take wuni, kwana ne batayi, shima saboda abincin ta, (qa'idar larabawa, baiwa za'abawa d'aki guda, itada baby, itace mai mata komai, amma ita Maman su bata yarda ba, tunda ita tasan zafin Haihuwar shiyasa ko akan Mahmoud itace tayi rainon d'an ta)
   Zuwansa gida da wata Uku, ya koma school, Jami'atul Dubai, dama yana ciki, kawai ya yanke yatafi Madina, saboda yanason qara ilimi na addini sosai, b'angaren Hadith zallah ya karanta
    Qoqrinsa yasaka, mudirul Jami'atun yaso ya tsaya, yayi karatun amma yaqi, one year kawai zai qara yakai matakin Doctor
   Shidai yafison ya dawo gida, kodan yaringa ganin 'yan uwansa, da kuma ya rabu da Taufiqa, yarinyar *Wazirul wuzara* (prime minister) na garin Bahrain wadda tare suke
    Tanuna tana sonsa, har yayunta sunsani, shi kuma baida ra'ayinta shiyasa ya matsa bazai qara zama ciki ba
   Bayan Shekara 5
Bintu angirma, lokacin tanada shekara 6, tana primary 2, idan kaji hirar ta, to da Akhee Mahmoud ne, itama taji Hausa, amma ba normal ba, tunda har yanxu bata saba ba
   D'an hutun da suka samune, a jami'atul Dubai Canidian,yasaka yace zaije ziyara Nigeria🇳🇬, tunda ya kwana biyu baije ba
   Dama Sauran sa 4 months ya qare karatun sa, a *Jamia'tu Canadian Dubai*
  Inda ya karanci,  business saboda yaci gaba da kula da Markaziyyar babansa,
  Markaz Muhammad Ahmad Kaya na mata dana maza Imratee, ita suke
  Ya kula da mahandama ciki, mahaifinsa baya duba abinda ake ciki, saboda kullum yana Daular Sultan
    Larabawa sune kan komai, kama daga kan Director, assistant director, manager, duk larabawa ne, amma baqar fata sunyi yawa,kuma da alama 'yan Nigeria🇳🇬 suna son kasarra Company, tunda sunada yawa ciki
     Shiyasa ma ya tsaya yayi karatun sa, akan business,(Hisab wa attijara) saboda ya taimaki mahaifinsa
   Yana kuma per time, a jami'atu Skyline, ita English ne zallah, so Mahmoud ya had'a komai, da ake so
    Bawai a Markaziyya suka tsaya ba, ko *Golden Dragon shop* na Abban sane, kuma shine Director na wajan
     Millonian Cargo, na sarkin garin ne, nan ma yana Shiga yaga ya aikin yake kasancewar
   Mahmoud* bashida hayaniya, ko wani hali wanda ba nagari ba, badan kada nayi qarya ba, da sai nace shi dai bashida halin da za'a qyamaceshi
    Karatun sa yasaka a gaba, yana kula school mate nashi, amma ba da sunan so ba, da Dama 'yammata suna rububinsa amma shi baya ta tasu, bawai dan wulaqanci ba, sai dan kare haqqin Allah
   Da kuma bashida ra'ayin auren yarensa, yafison baqar fata, kamar Mamansa
    Yanada abokanai sosai, yari rrika da dama, wasu ma cikin part nasa suke kwana
      Yaso tafiya da Bintu, so suna da school a time, d'in shiyasa ya shirya tafiyar shi kad'ai
   Ranar d zaitafi Bintu kuka, ita dai ya dawo, yabari su qare zangon, amma yaqi, tunda ita lokacin da take free shi kuma, yana exam lokacin
    Sallama yayiwa kowa, daga iyayensa har Sultan d'in(sarkin garin kenan), da qanwarsa datake ta kuka
Zuwansa Nigeria🇳🇬 a wannan lokacin ne, ya had'u da ZAHRAN BABA
   Akanta yasan so, yafara so, yaji so, amma ace za'a rabashi da ita, wani mai k'arfin halin ne, zai raba hanta da jini, bayan zuciyarsa da ita, tafara sabawa, babu son kowacce mace sai ita
  Baya fatan Allah ya qaddara masa, rabuwa ko da daidai da second ne da ZAHRA

    ADAWO LABARI

Ajiyar zuciya Inna ta sauke, kana ta tafi turakar Maigari, dan yimasa wannan albishir
Da sallama tashiga yana kashingid'e akan tuntu, yanajan casbaha, tashi yayi da murmushi a fiskarsa yace Innan yara ya akayi?, naga bakinki da magana

Dariya tai, tace hala yau kanajin nishad'i ne?, koh to ai Indai kina cikin farin ciki nima ina ciki
(Wai kaji tsofaffi, wai nan piran love ake)
Hakane, dama wata magana nakeson yimaka, Allah yasa banyi a qurraren lokaci ba?
Allah yasa to, fad'i
"Wato abinda muka dad'e muna zato ne, Allah yasa yazo"
Me kenan?
Maganar *Mahmoud* da Zahara mana, ashe dai da gaske suna son juna, so ba qarami ba, yakasa fad'ane saboda yana tunanin tayi qanqanta yayimata magana, anasa tunanin fa
Saida namasa waya, bakajiba harda kuka, akan meyasa za'a bawa Zahara wani bashi ba
"Kuma kasan itama ZAHRA tana sonsa, duk da batasan so ba, amma ayanda take fad'ar alamomi game da, rashin Mahmoud datayi zakasan lallai tana cikin matsanannciyar qaunar Mahmoud
Shine nace mai zaihana kayiwa Malam magana, gida bata qoshi ba, ba'a bawa dawa ba
Aganin ki kenan, Sharif Auwal ba bare bane, kuma mutumin arziqi ne
   Kinyi sake, keda jikokin naki, dan aure kamar and'aura saboda bazamu zama qananan muta ne ba
   " yasan yana sonta, yakasa fad'a?, ni da ace wani ne, zan iya Shiga na fita yasamu ZAHRA, amma wannan bazan iya ba"
  Naso yasami ZAHRA, dan har magana munyi, amma bamu sami wata amsa ba, saboda haka sai ayi hak'uri Allah yayi musu zab'i na alkhairi
    Haba malam, ai wannan ba magana bace, kanada ikon yin yanda kakeso akan yaran gidan, barantana ZAHRA, da tazama kamar yarka, ko jika
  Idan bazakayi magana ba, to gaskiya nizani gidan, bazai yuyu ace yara nason juna ba, amma ahana musu juna
    Kuma ni nasan yadda suke bawa juna kulawa, amma zakace bazaka iya ba, jikan naka cal guda amma kace haka
   Nidai zani da kaina, indai Malam yanada kirki zan gani?
    Ban yadda ki d'ara ko nan da can ba, mutuqar da sunan wannan magana kinga nagama magana, Idan rabansace Allah zai bashi, amma inyi magana akan abashi, badani ba
    Inna babu bakin magana, fita kawai tayi, dan zuciyarta wani zafi take, saboda takaici, lallai kaqi naka, kaso d'an wani
    D'aki ta koma, waya tayiwa Auwal tafad'amasa komai, har yanda sukayi da *Mahmoud* da kuma Maigari
    Inna kada kisa damuwa, insha Allah, ZAHRA batada miji sai *Mahmoud* dan shi kansa yaran da aka bata, wallahi baya son ZAHRA
    Yanada wadda yake so, abokinsa ya fad'an, dan dama munsan juna, yace shima agidan su rigimar da ake kenan
    Akan Mamansa tace abar d'anta ya auri wadda yake so, uban yaqi kuma, kinga ai nan ma, wata dama ce
    Ai kuwa, to sai mudage da addu'a
itace mafita kawai, sallama sukayi
ZAHRA jiki yana sauqi, dan yanzu bata felling komai a jikinta, sallama ma suke buqata, tunda jiki yayi normal
     Malam sai shiri ake, zaiyi auren 'ya mafi soyuwa cikin zuciyar sa, kaya ma da kansa yake siya idan yaga yayimasa
   Itadai Inna ido ne, nata ganin Malam bai canja ra'ayi ba, duk da yaji abinda Doctor yace, shiyasa ta zubamasa ido
   Ko maganar yazo mata da ita, bata saurarensa har ragowan matan, basa wani zama yayi magana da su
   Shi mamaki suke bashi, ganin   abinda suke, saikace wanda suke dominsa yasan su nayi, shi yana can yama manta da wata ZAHRA
    Amma su suna tad'insa, ko ragowan yaran sa, matan da yasaka aka kiramasa su, basu bada goyan baya akan haka ba, sukace dan dai ba yadda suka iya
      To kai Auwal daka dena mun magana, menayimaka, kan me kuma kakee so ka had'ani da matana da ragowan yara na?
Malam ni ban had'a ka, da kowa ba, kuma magana da kake, kan *Mahmoud* wallahi yaran yana sonta, kuma har Maigari yasani, lokacin da ya fad'a, kaikuma kamata miji shiyasa Maigari yace bazai iya yimaka magnae ba
    Amma tilon jikansa namiji, ace yanason d'iyarka, badan kayi magana ba, babu abinda zaisaka bazaimaka magana ba
   To kun riga kunyi alqawari, da kansa Maigari ya kirani ya fad'an, yaran kuma jarrabawa yake da tuni yazo
   Ikon Allah, yanzu Maigari baidace yamun haka ba, ai da saiya fad'an, amma ko yanzu bata b'aci ba
Zamuyi magana, lallai shiyasa kenan, Inna ta dena zuwa, shine kuwa Malam, dan tayi tunanin kai kace bazaka bawa jikanta ZAHRA ba
    Ni kuma, haba ai Maigari yafi qarfin komai awajena, zanyi magana da Malam Sharif Auwal, amma dai za'aji kunya
Babu maganar kunya Malam, kadaiyi qoqari, tashi yayi yana dariya, sai wajan Anas saurayin ZAHRA daza'abawa
    Haka Ya Auwal yatafi cikin gari, wajan Anas dan yaji ta bakinsa, akan maganar yanada wadda yake so ko kuwa babu
   Waya yayi masa, yace dan Allah ya qaraso, bakin titi yanason magana dashi
   Zuwa yayi, gaiswa sukafara sannan ya Auwal yace wato Malam Anas, naji wata magana yasaka nace lallai sainazo naji daga bakin ka, cewa maganar haka ne ko kuwa qarya ne
Wata magana ce haka, huum wato su mutane ba'a iya musu, komai kayi idansu na kai, har ankai rahotan halina
  To saime, abinda kaji hakane inada wadda nake so, take sona, kuma mailafiya ba kamar qanwar kaba
Yanxu haka, d'akin na kamawa wadda nake so, sai ya akayi, ko bazaku bawa d'an isaka qanwakuba?
   Kuma na rantse indai aka auran ita sai kunyi dana sani, tunda ni banso, arasa wadda za'a ban sai 'yar qauye, rainon koko da qosai, yayen kamun flour da farau farau
Girman noma, da almajiranci
Enough, enough stupid dama haka kake. Wallahi Malam yayi gangancin bawa ZAHRA Yaro mara tarbiyya irinka kamilar mace
Kai dama haka kake?, lallai albasa batayi halin ruwa ba, kuma ayadda kake nuna hallaiyarka wa mutane ashe qarya ne, munafuki ne kai, to wallahi karabu da ZAHRA tun wuri
  Da wanda take so, shima yake sonta, kuma mutum kamili ba irin kaba, banzaci haka kake ba, Allah nagodemaka daka nunan halin ka
Hahaha, ai magana ta wuce, dole na aure ta, muraya Sunnah sati mai zuwa, na sau muku qanwa, amma badai narabu da ita ba
   Wallahi baka isaba, kai waye, dazaka auri qanwata kuma ka sauta, indai ina raye baka isa ka aure taba
Ok, saboda kunason kubawa d'an larabawa ita, ai aure kamar anyi shi angama, sai dai ku mutu bye, haka ya bud'e murfin motar ya fita
Salati ya Auwal yasaka, yace qalu innalillahi wa inna ilaihi rajiun, masifa sabuwa daga wannan sai wanccen
    Amma Idan kasan wata bakasan wata ba, zan maka rashin mutunci
Haka yaja motarsa sai gidan sa
GAYA
    Malam ne yaje gidan Maigari, saida suka gaisa, malam ya gyara zama yace, wato Maigari, gaskiya tunda nake baka tab'a yimun abinda banji dadi ba, sai wannan karan, kuma maganar da bakason nasani nasani yanzu
   Tabbas akan ka, zaniya rashin cika alqawari, nanemi yafiyar ubangiji daga baya Ace *Mahmoud* nason ZAHRA saboda nabada ita wa wani, shine zakace kada ayi magana, ai yau basai gobe ba, zanyi maganar sizo su karb'i kayan su
   Malam, bafa za'ayi haka ba, yasan yana sonta yasa qafa ya tafi, ba tare da ya sanar damu ba?, nidai bangoyi bayan afasa wannan auren ba, kayi hakuri munemi ma musu farinciki arayuwarsu
  Haba malam, da hankalinka, bai kamata kayi haka ba, wama ya fad'a maka?
Auwal yazo yake fadan, yace kace kai bazaka iya fad'a mun ba, itama Inna saboda haka tadena zuwa kenan?
A'a ita ai hanata fita nayi, amma Malam baikamata ba, kayi alqawari ka ware, indai kamaidani wa kuma d'an uwa banyarda KA qara tada wannan maganar ba
Ka sawa abin albarka, kawai, tunda shima yaron yanada hankali, gashi mahaddaci, kaga zaikula da ZAHRA sosai, tunda yasan haqqin aure
  Haka dai Maigari yanuna ba za'ayi haka ba, ba yadda Malam ya iya, shima saiya bar maganar
A b'angaren Anas murna yake, amma fa tabbas saiya auri ZAHRA, dan yaga yarinyar tanada kyau, ai saura 2 weeks biki, kenan zaman sati zasuyi yabata takardarta
   Ya Auwal kansa, badan yaso ba, saidan d'orewar farin cikin qanwarsa, yasaka shi qara komawa wajan Anas, amma yaron yace shifa yanzu yana sonta, bazai iya sarayar da qaunar dayakemata ba, yanzu ya dena komai zai zauna da ita
    Har kud'i ya Auwal, yabashi amma ya tubure tace shifa bazai iya zuwa yace baya sonta ba, kuma dole ya aureta
Ba yanda ya iya haka, ya tafi yana mai baqin cikin wannan alamari
Shi kuma dariya, yake ganin yadda suke masa, dan har Inna ta gida data Maigari saida sukayi masa Waya akan ya haqura ya janye, amma yaqi yace lallai yana sonta
   Lokacin da sukayi wayar ZAHRA tana wajan, kuka tasaka tace lallai ita bazata aureshi ba, dama wasa suke mata sukace *Uncle Maikyau* zai zo, kuma shi zai aureta
  Ita wallahi bazata auri wani ba, au Inna garama daza'amun auren, saboda me ZAHRA?
Eh mana, tunda baizo ba, garama ayi bikin, dayana sona, ai da bindiga zaizo kawai ya harbeshi tunda naga kowa yanada bundiga a garin su
  Dariya sukayi, Iya tana wajan, itace tace ai ZAHRA zaizo yana jarrabawa ne, kuma insha Allah bazaki auri kowa ba.....
   Kai Iya, to ai *Maikyau* zan aura kyace bazan auri kowa ba, haka akeyi
Nifa banceba, haka nakeson nace bazaki auri kowa ba, indai ba *Mahmoud* ba
Tattaunawar dasu keyi kenan a kullum amma sunkasa samo mafita, ga Maigari yace bayason yaqarajin wata magana, indai akan afasa auren ne
Ga lokaci tafiya yake, yanzu haka sauran 10 dayz, shiyasa Inna ta gidan Maigari tasaka ZAHRA da wowa wajanta dan kula da ita
B'angaren *Mahmoud* angana                     Imtihanul fatratul akheera, shiyasa yake ta shirin tawowa, kowa na gidansu yasan da maganar baran Bintu komai tace, Ukhtee ZAHRA
    Iyayen sunyi farincikin jin wadda yake so, amma bayanin da sukaji ne, akan matsalan da ake, shiyasa ka, jikinsu yayi sanyi, baran Mamansa tasan Halin Abban ta
Amma itama addu'a take Allah yabawa d'anta zahi, koba komai zuri'ar Malam abin alfahari ce ga kowa, kuma babu makusa jikin ZAHRA
   Sharif mahaifin Anas, da baisan komai akaiba, sai shirunsa yake yi, haka shima Anas dan ya Dave sai ya aureta, kodan wannan shashashan wan nata, me gaya masa magana
Shiyasa shima sai d'oki yake

Dubai, garin alqusais
Iyalan waziri Muhammad Ahmad, ne dashi kansa suke ta shiri da haramar tawowa 9ja, ashirye nagan su, komai yayi ready, ga trolley wajan 3 set dana gani tare dasu
   Duk na tafiya ne, *Maikyau* shine kan gaba, saboda yana d'okin zuwa yaga Hayatee Omree tasa ZAHRA shida abokinsa Azzad d'an Sarkin garin *Ajman*
Tare sukayi karatu a Jami'atu Skyline, so halinsu d'aya shiyasa yabashi labarin ZAHRA da yanda ake
   Tare yace su tafi, kodan Idan angon yaqi suyimasa abinda zaisa dole ya haqura
   Aircraft suka tafi dan hawa jirgin dazaikaisu 9ja direct, basaisunje Ethiopia ko Egypt ba
Haka suka Shiga, komai yana clear, jirgi ya tashi a sararin samaniya sai 9ja
Lol

ZAHRAN BABA (Completed)🌹Où les histoires vivent. Découvrez maintenant