9

2.3K 94 0
                                    


  Ya Auwal ne yafara magana, Malam Anas masoyin ZAHRA koh?, kai ya kad'a yace tabbas ko kana shakka, Idan ma kanayi ko bakayi, zaka tantance ranar da aka kaimun ita
   Murmushi yayi, yace nazo na had'aka da Allah nakuma yimaka last warning  kafita hanyar qanwata ZAHRA, karabu da ita, kaje can kasami dai dai da kai
Wannan da kake gani shine ya keson ta yasan darajarta, yake mata qauna ta fisabilillah ba wai jikinta yake so ba, kai banda abinka mai zaka tsinta jikin yarinyar da ko qirgan dangi baigama fitowa jikin taba?
Abinda yake bid'a wajanta shina ke so, kuma koda ma ace yarinyace shekara 9 tunda za'a d'auran ina ruwan ka
"ZAHRA tawa ce, Idan kuma kuka cikan ciki, wallahi bazan sake taba, zan zauna da itane tasan rayuwa, banda abinka kai jar fata, me ye naka na rikicewa sai ita?
ga yammata nan, da yawa, a garinku kaje ka samu mana ka aura, ko dole sai ZAHRA, da kake gani kullum, nibanma yadda da kaiba da ita, anyama?
Koma itace kake so nayi maka lamuni zan baka ita bayan one week, kafin na kawota gida ma, sai munje asibiti, anyi mata wankin ciki, kaga ko aranar zaka iya auranta
Duk wannan maganar Anas tsagera keyi musu
*Mahmoud* da ransa yagama 6aci sosai, baisan lokacin daya fara bashi mari ba, saidaya masa 5, kafin akaci galaba ya iya cika shi
Wani irin tururi had'e da madarar wuta na baqin ki shine yake cinsa, lallai ZAHRAN sa za'ayiwa wannan cin mutuncin?
Kenan shi bama son Allah yake mata ba, rayuwarta zai lalata, sannan ya saketa
To da batada Wanda take so, yake sonta, da qaramar bazawara zai maidata, lallai yayi kuskure
Ya Salees ne yace, Anas mun had'a ka, da Allah cikin sauqi karabu da ZAHRA, kaqi, amma wallahi akan haka, ko wadda kake so, saita gujeka, muje zuwa
Gurin zama cikin unguwarku saika rasa, shashasha, wanda baigaji daraja da qima ba
Azzad, Ya Auwal ku tawo, Idan yasan wata baisan wata ba?
Haka suka ja *Mahmoud* da qyar wanda har hawaye masu rad'ad'i saida suka zuba, jin tanadin tsiyar da akayi wa 'yar gidan sa
  A can Gaya*
  Maigari da qyar ya sasanta da habeebatyn sa, dan Inna ko kallon inda yake batayi, saida ya had'a, da Maman su Mahmoud, sannan aka shirya
   Su Ya Salees basu zame ko inaba, sai Asibinti wajan Dct Sameer, kunsan sun zama abokanai dalilin matan su, da kuma zaman da su kayi, so shima yasan matsalan dasuke forcing
Tunda Doc, ne kuma shiya bada, shawara akan ayimata abinda take so
  Gaya masa komai sukai, murmushi yayi yace, lallai zaikuwa ji kunya, wallahi saiya gagara fitowa, badai shi d'an iska ba, ni kuma zan had'a masa abinda koda gaskiya ta fito zaiji kunya, kuyi qoqari kuce akawo su, ayi test daga shi har ZAHRAN
Idan akayi haka, zamuyi finding out na solution namu, simple, ai HIV zansa masa, kunga Idan Maigari yaji haka, ai dole ya haqura
   Haka akayi, gida suka koma, nan fa Ya Salees yayiwa Malam fanfo akan lallai sai aje ayi test, tunda ya hallata ma, wani baisan yanada itaba, Idan akayi katari da yayi using da wani qarfe wanda mai ita yayi amfani dashi
   Haka yayita d'ora shi, har ya yadda, tunda Salees ne, da Auwal ne, zaice makirci ya had'a, duk da yaga tadena masa magana
   Washe gari sai gasu, shida kansa Anas yazo ya d'auke ta, za'ayi magana, Malam yace abari sutafi su 2, tunda sauran 3 dayz a daura aure, kuma ai yaran yanada hankali
  Anas d'an qarya, maimakon yatafi, Nasarawa Hspt, ko Murtala, a'a sai yatafi cikin sauqi inda za'a kasheshi, wato Haubenz hspt, inda Sameer yake ciki
Suna shiga, da taqama ya tamvaya cewa yanason za'ayumusu HIV test, wannan itace matar da zai aura, Doct Stylich ce, su Anee basa nan, so ZAHRA batasan taba
File suka bud'e da komai da komai, sannan tace yajira Doc yazo
*(Ya Auwal shi ya fad'awa zahra, yace ko sunje wani asibitin tace ita bata Shiga, Idan taqi dole ya kira waya, kinga sainace aka woki nasu Sameer, to sai akaci sa'a nan ma ya tawo)*
     Hira yake mata, kafin likitan yazo, amma ita ko kallo bai ishetaba, azuciyarsa yace lallai yarinya kin kusa shigowa hannu, zaki yi bayani
    Come in, akace musu, lab, suka shiga anan aka d'iba, aka gama, a lokacin sukebada result amma sai akace musu, sai nan da 2 dayz, saboda wani machine nasu yasamu prblm
   Haka ya tarkata suka dawo, a hanya ko pure water bai siyamata ba. Itama bata roqaba
   Wow, mutumin ka iya, kai su Ya Auwal ne, kenan suna binsu abaya, lallai
    Ai Ku bari, sai ranar d'aurin Aure za'a nuna, Idan aka nuna yanzu, komai zai iya faruwa, zaice bashida ita, kuma kunsan qara zuwa wani asibitin za'ayi, agano
Amma Idan aka bada ranar, hankalin su, tashi zaiyi, kaga basaso jin kunya sun tara mutane ba ,kuma babu lokacin da za'a qara wani test d'in
  Kaga anan sai, Inna tayi aikin ta, na cewa to abaka, hhhhhoooooo, amma dai kanada brain, nayi tunanin yau za'a bayar
Azzad ne yace, ai bazamu barshi haka ba
   Sai mun, qara da sashi rubutun dole, kuma yayi sign da komai, akan shi baya sonta, dole aka masa, saboda haka bazai iya zama da itaba, ko an d'aura to shi ya saketa 3, nan ma dariya suka saka
    Jin komai yazo cikin sauqi, kai Alhamdulillah, Allah nagode maka, *Maikyau* yake fad'a
ZAHRA koda ta koma, gida tacedai ga abinda sukayi, kuma ance result sai bayan kwana 2, babu laifi, ai yaran dayanada wani abu, bazai bari aje ba

♥♦♥♦♥♥♦
    BIKI BUDURI
Yau ake yin kamu, kuma kamu na 'Yar maishi na wadda akeji da ita, yar dangi
A wani qaton waje akayi, canopies aka zuba da fararen kujeru, anzagayesu da decoration, milk and blue, wajan da aka tanada dan Amarya shima sai d'aukan ido yake, kai bakace a Gaya ake wannan shagalin ba
Aikin Aunty Aysha ne, ta kirawo masu Decoration d'in tundaga Kano, da wadda zatayi wa Amarya kwalliya (Munnuvia make over)
Sosai gurin ya qayatu, yasha kyau
"Wajan qarfe 3, agidan Maigari d'akin Inna mai kwalliya ce take yiwa ZAHRA, make up, bayan qunshin da akayi mata, wanda ita kuma yagana ce tayi, 'yar chadi, mai had'e da sirrin qamshi ciki
   Doguwan riga k'irar Bahrain ita tasaka, *Maman Maikyau* ta bata, komai dai yatafi cikin tsari, haka aka fito da ita zuwa wajan
Lokacin da Maikyau yaganta kamar ya saceta ya gudu, ganinta yayi kamar wata flower girl, dama ZAHRA ga gashi tubarkallah
    Aunty Aysha ta fito da ita sosai, itama lokacin da taganshi mantawa tayi ita amaryace da gudu taje wajan sa
*Maikyau* kalla kaga nayi kyau?, ga qunshin ma, duba tana magana tana nuna masa, wow yayi kyau habeebty, kwalliyan tayi kyau kamar ba *ZAHRAN BABA* ba, u look look so gorgeous nd busty baby na, dariya tayi
  To ai bakamana selfie ba?, ohp na manta, tawo a dubban jama'a haka suka ringa shan pictures nasu, tare da Bintu dasu Azzad aka ringa d'auka
BbSaida Inna tace to ya isa sannan suka bari, shi kuma ya tafi
Kamu akayi, had'e da wasannin su na al'ada, da aka sabayi indai ana biki
   Kid'a aka sha, sosai suka raqashe, ana magareeb aka tashi, dangi dai kowa saiyaba kyan Amarya yake, kaf tarihin *Garin na Gaya* ba'a tab'a biki wanda yayi kyau haka ba
Anas anata bidiri za'a angwance da ZAHRA, harwani jiji da kai yake, suma gidansu taro ake, dan harda mace za'a aurar
Lokacin da suka koma, sai gashi wai yazo yaganta, aikuwa sai ya qara rud'ewa, Ji yake kamar ya janyo jibi, ayi ad'aura auren, koya huta da idon wanccen mayen wai *Mahmoud* tunda lokacin dayazo agbansa akace taje, hartace bazata ba, Maikyau yace ta fita
Ba maganar arziqi saima magana da ya yab'a mata, wai me take yi acikin gidan, bayan ga nasu gidan, kunsan ZAHRA da rashin kunya dan ma tayi laushi
*Karkace kai tayi, tace kai asuwa kare agudun layya, faqara'au alal larurati, dan kaga ana kulaka shine zaka wani d'ebo dirty mouth naka kace zaka gayan magana, talaka kawai, bazai yuyuba na aureka kai atafe ni atafe, naci saikace quda, taurinkai kamar kafuran farko, ko jinjirin jaki, to ahir d'in ka, da gayan magana, kogaywa Maikyau baqa, da baki kamar kacar jirgi, fuska uwa anwatsawa biri tawadda*
*Dazakana cemun villager, uwar wani a kantagora aka aurota, ko kazata bansani ba, kuma kalleni kaga dani da kai a nemi d'an qauye, gaba d'aya kan sane ya kwance, lallai wato dama batada kunya?, zaki shigo hannu, wallahi saikin kasa moruwa*
*Kaine dai bakada ita, kuma indai ka ganni cikin gidan ka, kasani a turu kayita jibga, ni ZAHRA nafi qarfin ka, na wuce ajinka, majnuuni kawai, yawu ta tofamasa tayi wucewarta*
   Abayansa yaji ana dariya, ana tafi, Anas ya kaga, wallahi nayi imanin ko and'aura maka ZAHRA, bazaka iyawa halin taba, ita one ta isheka, bare kuma bazaka aureta ba
   Bashida bakin magana, illa wani abu mai d'aci daya had'iye, lallai kuwa zasuga tsiya (nace Anas kaidai zaka gani)
   Washe gari akayi, gasa, na samari nan ma sunsha kallo, shi Azzad video yafara komai bashi sha'awa yake, baran gad'ar da akayi a dandali yaga yara amma su a tunanin su yammata ne
Da wasan tseran gudu, sosai akayi shagali na ban mamaki, kuma kowacce rana lemo na kwali da abinci mai rai da lafiya ake rabawa
  Anas dai yatanadi rashin kirkin da zaiyi, dan tunda yake ba'ata6a yimasa rashin arziqi irin haka ba
*"Baqar fuska, baqin Ido baqar zuciya, mai hancin botorami* shi yayi masa ciwo, yanda yake da hanci Maikyau ace masa mai hancin botorami
Lallai zasuyi kuka da idonsu
Wayarsa ce tayi qara cewar , ana kira, kamr bazai d'aga ba, sai ya d'auka
"assalamu alaika, wa alaika sakam" kana magana da Dr Sameer, oh Dct ya gida? Lafiya Lou, dama sakamakon Ku, ya fito, shine nace Idan bakada uzuri saikazo Ka karb'a
"Ba matsala insha Allah, amma gaskiya yanzu bana gida, kuma gobe d'aurin aure, kaga da safe ba lokaci amma dai ko jibi ne saina zo
Ok, haka yayi, sai anjima

ZAHRAN BABA (Completed)🌹Donde viven las historias. Descúbrelo ahora