6

1.2K 33 0
                                    


   Mohammed baisha wahala ba, tunda Jameela ta kasance sannaniya a ko ina, bayani yayi masa akan abinda yake tafe dashi
Nadaga k'aunar daya kewa Jameela, president yayi murna ba qarama ba, kasancewar d'a maigirma ya tawo takanas yanason wata daga cikin al'umar dayake mulka
    Sosai yatayashi farin ciki, a gidan ya kwana d'aki guda qayatacce aka bashi
    Da kansa president, yayimasa jagora har garin na Gaya, (kada ku manta shima mahaifinsa babbane, so dan President yamasa karramawa haka bata b'aci ba)
  Gidan Maigari akayimusu jagora, alhamdulillah, sinsami gida a gyare ko ina Maikyau, saboda dama anyi gyara agidan sosai
Malam aka kirawo, fadar da Maigari yake zama nan aka zaunar dasu, ruwan roba aka zube tareda dammamiyar fura, wadda taji had'i, daga gidan Malam aka kawo
  Shugaban qasa da kansa yayimusu bayani akan abinda ke tafe da wannan bawan Allah, kabbara Malam yayi, yace alhamdulillah bamuda abin cewa sai Godiya ga wanda ya yimu, yake saka qaunar bayinsa ako ina
    Wani jinkirin alkhairi ne, gaskiya nayi murna, amma ranka ya dad'e banqi ta takaba, shidai yaxo yaganmu kuma munganshi, amma bamusan kowa ye ba, kuma shi aure ba daka akeyinsa ba
      Yarinya zatayi mana biyayya, amma gaskiya sai munga danginsa zamu bashi zinariyar garin mu
    Tabbas haka yake, nayi murna, dama haka akeson mutum, mai hankali, nima nayi tunanin haka
Bayani akayimasa take, yaciro waya, magana yayi wa mahaifinsa take kuwa yace yana tafe yau zuwa 9ja
    Haka akayi, komawa sukai Abuja, dan jiran mahaifinsa, gari na wayewa da Waxiril a'azam Ahmad Basha suka farka, (direct flight ya biyo, baitsaya a wata qasa ba, shiyasa yaxo akan time)
  Yanada aikin yi, shiyasa yana zuwa baiyi jinkirin zama ba, suka tarkata suka tafi, komai cikin sauqi yazo atake aka saka biki wata mai kamawa
   Jameela sai kuka, abinda take so tayi koda cikin garin ga, yanxu gashi wata qasa daban ma zata
Innarta da matan gidan Maigari, sai murna, tundaga lokacin aka fara mata gyaran jiki, ciki da waje
Zaman kurame suke, dan Mohd ba Hausa ko Xo abakinsa, ita kuma ba ajal ko d'aya bakinta, saidai dariya dasuke jefawa juna
A haka lokaci ya tawo, akafara shagalin biki, 'yan uwa nesa da kusa kowa ya halarta
    Biki yayi biki, shikansa Mr president saidaya had'amata party guda, a sharaton Hotel dake garin Abuja, oh saiga larabawa a 9ja, wasu a Abuja wasu a Gaya, wai TV tazo har gida
    Abin kallo suka koma, su kuwa dayake abinda ke gabansu shi suke basu damu da kallon da ake musu ba
    A haka aka share biki, flight 2 aka kawo dan kai amarya, wai zokaga rububi na mutane daga na birni harna qauyen
  Yo anji Dubai kowa ya tawo, wasu daga wani gari ma, zuwa suke Irinsu Fido, Lubie, Ybk, Anee Asea, Mrs Omar daga katsina, suma haka na gansu, sai Anker, Leemcy ZAHRA Bukar, Maryam G, daga sokoto da Zamfara, Billy giro Munay daga kebbi, Sahaf, Aunty Sady jegal su Mrs Jawaheer, Miss Hafcy duk haka na gansu
  Duk wanda yazo, ansaka sunansa atafiya, wad'anda aka sani da wad'anda ba'asani ba
Su Inna ana kan gaba, ta gidan Malam, itace wadda ke riqe da amarya, kaita akayi wajan iyayenta maza nasiha suka mata, da nunamata matsayin aure, da darajarsa da qimarsa wajan matar data kasance cikin inuwar aure
    A haka aka tafi Kano ta dabo, dan zuwa airport, motoci nagidan governor su aka kawo, dan d'iban wad'anda za'ayi tafiya dasu
Haka aka tafi, sai airport, sauke mutane aka yi, motocin suka jiya
Ko wacce nagani,tana raba ido za'a Dubai a kyauta, ba da kud'i ba, su Fido Sodangi sai zare ido take, a airport bata tab'a shiga jirgiba, haka nagan su duk sunyi tsuru suna jiran suga ta ina zasu fara hawa
   Dariya nayi, ganin wata acikinsu tasaki fitsari, dubawar da zanyi sai ganin Miss Hussein nayi(Meimi bee) tana rufe jikinta, saboda ganin yanda step na jirgi yake sauka qasa
   Haka aka fara bin layi, wajan Shiga saida Sahaf tayi abin kunya, daga ta fara hawa saita dawo, Lubie ce tace kinga idan bazaki iya hawa ba, to ki koma Maiduguri, amma bazakisaka ace mu koma ba, dariya nasaka
Miss Hafcy ce takama hannunta, ahaka aka gama shiga, jirgi ya d'aga, ko cikin jirgi naci dariya yanda 'yan naga writers na wara ido kamar za'a yankasu
Munay ce, tace kash wallahi naso tawowa da biro na, ko na samu abin rubutawa makaranta, amma na manta, Kut lallai Munay muna hanyar ko mu mutu komu tsira zakiyi maganar wani readers, kiyi fatan kada jirgi ya gaji da surutunmu ya tsaya
    Haka sukayi ta abin dariya, a Egypt jirgin ya sauka, nan ma saida aka saida hali, dan ita Meimi tace lallai saitaje wajan da aka binne fur'auna sukuma suka hanata, da qyar ta hanu, amma ansha selfie kodan a d'ora a dp
Two hours akayi, jirgi ya qara tashi, sai Dubai emirate
Haka aka kai Amarya, Sama Dubai, gida na gani na fad'a, kusa da gidan mahaifinsa akayi masa gidan, komai yatafi cikin tsari yadda ake so, Illa 'yan groups na writers da suke qauyenci, ko 'yan garin Gayan basuyi qauyanci kamar yadda Hapsat Rano da Feedoh sukayi ba
   Koni da banje Dubai ba, naja class amma su karkuso kuga yanda suke baza idanu, Sahaf harda cewa wallahi tunda nazo Dubai sainaje Bur Dubai, wai mai Maryam G zatayi dani idan ba dariya ba, jin zata qara fad'a yasa nace Sahaf idan kikaji ancewa waje Bur to ana nufin kamar unguwar daza'a tsalleka da ship, itace Bur da larabci, ko guru kusa daku, Maiduguri zaki iya cewa Bur guru
   Dariya akasaka jin yanda nayi magana, ita kuwa saitakama fushi, ahaka muka shafe 2 weeks daga anyi maganar komawa gida, Anee zata fara, wai da ace ankoma school da mun tafi amma yanxu, ba'a yi resuming ba
   Ita kuwa Munay bata cewa komai, saboda ansamu kayan fruits abanza, kullum dashi take breakfast
Amarya dai batada tacewa sai godiya ga sarki Allah, saboda inda yayi mata kyakyawan sakamako, ya kawota inda ko a mafarki bata tab'a tunanin zuwa ba
Yakata inda ko a k'auyensu bata tab'a jin an ambaci sunan qasar ba, tayimata zab'i miji wanda ko a television bata tab'a cin karo dashi ba, yabata d'an asali, d'an dangi, mai muqami mai mulki
Hawaye ta share, tace Allah na godemaka, dakayimun abinda bakayiwa wasu ba, bawai dan nafisu agun kaba, Allah kayiwa nabaya Ameen
3 weeks sukayi, sannan aka maidasu gida Nigeria🇳🇬, bawai dan sun soba, a'a saidan ba yadda suka iya, Meimi bee kuwa harda tsarabar Seed na Apple wai zata shuka a Maiduguri, hhhh ko ta ina garin Maiduguri zata d'auka, haka kowa yafara mata dariya
     Zaman su zama ne na gaskiya da mitunta juna, da girma, danginsa kaf suna sonta, basa nunamata kyara ko d'aya, sun rungumeta sosai, run bata jin larabci harta dawo tanaji
Batayi wata uku cikakkeba, yamaidata makaranta, kuma idan ta dawo yana zama su qara biyawa, batayi zurfi akaratunta tafara laulayi, mai zafi, tundaga lokacin karatun ya tsaya
  Bayan wata takwas
Alhamdulillah, Allah ya sauketa lafiya, tasami d'a namiji, mai kyawun gaske, komai na mahaifinsa ya d'auko, bai d'akko mamansa a komai ba, Yaro yaci sunan Mahmoud
   Agarin akayi suna, daga nan ta tawo gida Nigeria🇳🇬, sosai danginta sukayi murna da ganinta gaba d'aya ta canja kamar ba Hafsan da aka sani ba, ta goge ta waye tazama wata big madam
Wata biyu tayi, mijinta yazo suka tafi, tareda abin arxiqin dayazo musu dashi, bayan wanda ta kamusu
  Bata sami komawa makaranta ba, saboda yace ai karatun ba dole bane, ta zauna tayi rainon d'an ta
*Mahmoud* yataso cikin gata da kulawa, ko ina ya shiga sai anyi rububin d'aukansa
Tun tasowarsa, mahaifiyarsa batayimasa wani yare daban, bayan Hausa, haka mahaifinsa baya masa wani yare illa larabci, shiyasa ya bud'i baki da Hausa, a gida indai da Mamansa zaiyi magana to Hausa zatayimasa sai fullanci
Yanada sheakara bakwai, akayimasa qanwa Bintu, yanson qanwarsa sosai, tun tana baby tasaba dashi, ko school yaje to da abinda zai siyomata, itama tasan dangin Maman ta tunda duk bayan 6 months suke zuwa, Nigeria🇳🇬, garin Gaya kuma
Shiyasa yasaba da danginsa, baran Inna, hargidan Malam yana zuwa, yanason qauyen kodan basuda qazanta ga hankali kamar cikin birni, baya kyamar komai nasu
  Bintu tanada shekara goma, shi kuma yanada 17 to 18 Allah yayi mata rasuwa, sanadiyyar wani wahalenllan Zazzabi datayi, yaji mutuwar qanwarsa sosai, dan yafi 6 months baidawo normal ba
Saidai akaringa rubutu da addu'a sannan ya sakko, tundaga lokacin gaba d'aya yadena wani sakewa ko a gida
Mahmoud* yanada hankali, rayuwarsa abin sha'awa kuma abin kwatance, bai d'auko kansa komai ba, Sarki yana qaunar sa sosai, yana jansa ajiki, yawanci idan ba school to zaka same shi a Janahi Sultan Imran Ahmad, wane ga kaknsa, shi Allah bai bashi d'a ko d'aya ba, shiyasa shima yaji mutuwar Bintu, kakansa yana sonsa sosai, bayan mutuwar Bintu ne, aka bawa Mahaifinsa muqamin waxiri na qasar Dubai amadadin rasuwar da kakansa yayi, gida aka basu na saurata, kusa da gidan sarki, dama kakansa bashida mata, kasancewar duk sun mutu, shiyasa aka gyara musu gidan, ga bayi rututu, part nasa daban shima damasu yimasa hidima, amma *Mahmoud* idan ka ganshi yanda yake da mutane bazakace d'an Waziri bane, saboda bai d'auki rayuwa akomai ba
   6years latter
A wannan lokacin ne, Allah ya bawa Mamansa ciki, lallai yayi farin ciki, sosai, kusan shine mai wa Mamansa komai, ko abinci ne yafara Mama kinadai so ko?, bayan shi mai zaki ce, saidai tayi dariya kawai tasanyamasa albarka
Mace aka qara samu, wadda taci Sunan Bintu, lokacin da akayi Haihuwar baya gida, yatafi Al azhar Madina, dan yin wani course na 8 month amma dai yaga pics sosai

ZAHRAN BABA (Completed)🌹Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz