Inna ta gidan Maigari itace ta karb'i yimata wankan
Kullum akaje sai anyi fad'a tarunga cewa Inna mugunta take mata, ta ringa samata towel da zafi kuma taringa cewa d'aga nan
Maikyau kam cewa yake Inna gaskiya ki dena, naga alama so kike ki qonamun mata, saboda tafi sona akan ki yanzu
Wataran sai ya lallab'ata take yadda ayi wankan, Inna kam saida tace yarinya gata nake miki, Idan ba haka ba duk qaunar daya ke miki indai yajiki ba daidai ba saiya canja
Dariya ake musu, tuwo yau Inna da kanta ta tuqa tace lallai shi zataci
Wallahi Inna banci ko a gida bana ci, bare agidan mijina Maikyau
Kudai kuci, aikam saikinci shizaisa kiyi kwari, Lallai to Inna sauran da basu ci ba fa?, kenan basuda kwari
Banceba amma gyaraki nake yi, wataran sai kinso dama ina kusa, haba aibazan soba, takuramin kike
Ni dai ZAHRA kidena yiwa uwata haka, kiyiwa mijin ki mana sai Inna ban yadda banima
Hhhh Ummi Inna tafiya takura shi kuma Maikyau ba ruwan sa, haka suke ayiwasa da dariya
Anzaga dasu Inna gurare da dama, sun kashe kwarkwatar Idan su, Iya da Gwago har selfie suka saka aka musu a *Golden Dragon* kai Dubai dai kowa yasan ta had'u burin d'an Kano Dubai
To ga Inna da su Iya dai sunje anbar su Aunty Sady a Jegal itada ZAHRA BUKAR a 9jaYau sauran kwana 2 suna, kuma ayau dangin su, zasu zo na *Gaya da Yola* da dangin Malam na *Gombe*, Sultan shi yabada kujera 100 abisa murna da kyauta da aka yi masa
Wai kowa ribubin Zuwa yake *Fulani Munay miss Zozo Feedoh yar ficika exam take amma ta barta aka tawo suna, Nafee Anker tana Zamfara amma saigata a Kano wai itama zata suna, Autar Hajiya qawar tace kuma itace ke bada labarin dan haka zuwa dole*
*Aunty Jamcy da su princess Hassy duk sunzo suma aje dasu, Leemcy itada Mrs Jawaheer a fiffiken jirgi suka zauna saboda cika, 'yan excellent, NAGARTA, WWA duk suna cikin jirgin, 'yan Dandalin Auta 1&2 da Dandalin Queen MEEMI, da Musha karatu ga Taskar Lubie kai gana Stylich da Pharty BB ga gayyar Duniyar makaranta duk a malegi nagan su asaman jirgi iska duk sai karkad'a su take*
Amma dole sai anje, *Jabo itada Aunty Bena da Lubie sai Ummul fadeela da Maman Haneep su a first class suke harna juya naga Maman twince itada Kwaiseh sai Asea Bashir Lallai kace writers sunyi kara SAHAF ma satin ne na bikinta amma saidana ganta*
Aunty YBK ita sai sunje Ethiopia zasu d'auke ta, tunda ta can jirgin zaibi kuma zai tsaya
Taro taro wai Idan bakayi bani guri, wani naya sai amale Idan ka raina taro ba naka bane, kamar ba za'a mutu ba, Gaskiya anyi taro wanda nikaina ban tab'a gani ba
Abinci abin sha odor akayi daga Hayat Hotel da Sammako, sai 'yan Ethiopia da sukayi nasu girkin (sunada yawa a Dubai), Hausawa na can suma kwangila aka basu na abincin 9ja
Allah yabawa marashi, shi, kud'i yai aiki, komai na bajinta akayi da Isa da girma da sarauta
Duk mutum guda sai da aka bashi Riga doguwa da mayafi da takalmi Toms ga Jakar chocolates da aka bawa kowa
Koni sunan ZAHRA da Little ZAHRA yamun anyi komai lafiya angama lafiya, anci an sha anyi hani'an, ancika ciki
Anyi guxurin wani kuma, dan 'yan excellent su, ZAHRA dai anyo guzuri duk da ba aranar zasu taho ba
OHW mazan duka sunje kai anyimun kara naga masoya har maqiya nagani saidai ba halin magana, Ya Aysha itace akan komai
ZAHRA tasamu kaya, Azzad kansa set ya kamata na Akwatu ga sarqan d'anyan Gold, abokan Maikyau sunmasa kara da nuna zaman aminci suke da shi Samar dashi akayi komai
ZAHRA tayi shigan larabawa data Hausawa komai tasaka ya amsheta
Anyi suna lafiya, kowa ya koma gidansa lafiya, writers sai baccin gajiya
Su Inna suma suntafi Iya aka bari da zata taimakamata dayimata wanka, kafin ayi arba'in su tawo 9ja da ita
Zaman su suke cikin aminci, da kwanciyar hankali, Iya na kula da ita sosai
Mahmoud dai sai raragefe yake saboda gaskiya amatse yake, ga Iya tasaka ido ko gurin sa bata bari taje. Saidai ita da kanta take kai masa Babyn
Yayi kamun qafa har wajan Bintu amma abin ba sauqi, har gashi yanzu suna shirin tafiya 9ja
Bintu ta fad'awa su Hanan da Hanadi har su za'a tafi Bintu anyi candy, itama maganarta ake da Azzad
Hanadi da Hanan suma visa aka buga musu, ita kuwa Bintu sai da akayi mata new passport cox her own ranar suna *STYLICH* ta yagamata shi, batasan passport bane ta yage ta bawa *Ya Hajja* number wayan *Pharty BB* lokacin da suka fita itama tanason zaga gari so batada number shine *Stylich* taganshi cikin jaka amma ta kama yagawa
Su dama suna garin, wasu guraren dai take son zuwa
Yau Iya anfita shan iska da zaga gidan, tana tare da wata tsohuwa 'yar Ethiopia ce taji hausa kullum nan zata zo susha hira yau ita ma saitace zataje b'arin su
Ummi na qasa, itama kome zata d'auko sai ta hau upstairs
Maikyau ne ya shigo ganin ba kowa a parlour yasashi kutsa kai d'akin ganin ta yai tana feeding Little ZAHRA
Gashinta yasha gyara taimasa kyau ahakan datake bawa Little Mamma, gashi ta ciko kallon Babyn take fuskanta a sake
Yana tsaye yana kallon ta, saidaga can yaqarasa ciki, kan bed d'in ya qarasa, ta bayanta ya rungumeta yasaka kansa a shoulder nata
Tsit kakejinsu atare suka saki ajiyar zuciya yaushe rabon da jikin su ya had'u waje guda?, tun tana labour
Habeebty ya kike ya Little?, lafiya lou, hankali tayi maganar
ZAHRA shine kike guduna koh?, bayan kinsan mijin kine ni kin biyewa Iya da Ummi kuna azabtar dani, ko rashin ganinki aka barni da shi aina wahala bare jikin ki
Ajiye Little tai dayake tayi bacci, kansa ta kwantar a cinyanta tana shafa sumarsa, Habeeby wallahi nima nayi rashinka Iya dasu Inna sukace kada na yadda da kai, wai zaka lalatan baby, kuma .... bata qarasa ba saboda bakinsa da yakai kan nata
Wow soyayya da dad'i Idan kayi dace, bata hanashi ba, saboda itama tayi missing, saida suka mitsikka juna sannan ya cikata dan kansa
Habeeby nayi kewarka da yawa, nima haka yana magana hannunsa na wata jiha daban
Kai ! ZAHRA kinga hannunsa ya nuna mata, kama hannun tai Habeeby banga komai ba, wani abune?
Gani nayi banji komai ba, kinyi wanka kenan?
Eh tun last two weeks fa, Na fad'a wa Iya ban ganin komai, tace nayi wanka kuma bai mun wasa ba ya d'auke duka
Wani kallo yamata tasan sauran bashiri ta miqe tace kaga yi nan hanya ta nuna masa
Miqewa yai ganin yana matsawa kusa da ita yasata saurin matsawa, ba yanda yai haka ya tafi yana had'iyar miyau, yai haquri tun kafin ta haihu ya jima rabon ta dashi
Ko da Iya ta dawo bata ga alama ta komai ba, duk da lokacin su Bintu sun dawo, anata shiri gobe ne tafiyar
Siyayya sukai sosai Bintu zata rabawa yaran garin, sai Mahmoud da ya bata ta siyowa Family na ZAHRA dana Inna
Tun safe kowa ya tashi sunyi shirin su da komai, Ummi da Abee rakiya sukai airport
Sultan dayaji labarin tafiyarta har gida ya kamata Mohd yace taje dashi dangi su ganshi
Qi tayi tace ai banata bane Babyn, nasane tabashi halak malak ko nan gaba ba itace Maman saba
Haka suka tafi, ya qara jinjina hankali na ZAHRA, Mahmoud tafiyar badashi akayi niyya ba, amma saigani akayi shima yana shiga wajan screening anzaci rakiya yai
Ummi murmushi tai, azuciyar ta tace Mahmoud na ZAHRA basu iya rabuwa da juna
Cikin jirgi babyn sa na hannunsa ZAHRA na kusa dashi Iya na gefen hannun damansa
Ba wani hira sukai ba, saboda Idon Iya, shi baisan Iya nada matsi ba haka, gara Inna ma akan ta
Hanadi Bintu Hanan sudai hiran su suke, kowa Na maganar saurayin ta
A haka har suka dira a Egypt, anan suka huta direct sai 9ja
11:30am jirginsu ya sauka a Kano, already ya Auwal da ya Sani suna jiran su
ZAHRA anzo gida murna kamar me, qin yadda Iya tai aje gidan Auwal dole daga nan suka d'unguma sai Gaya
Lokacin da suka qarasa murna murna farin ciki, su suka cikawa ZAHRA ciki, dan ji tayi kamar tayi shekara 2 bata gida
Gidan Maigari ya Auwal ya tsayar da motar, Maikyau ne yace a'a mufara zuwa wajan Malam
Haka akayi sosai Malam yai farin ciki da karramawar da aka yi masa
ZAHRA anzo gida harwani shagwaba take, Su Inna murna , haka ta ,zauna har wajan la'asar, su Bintu sunje gidan Maigari suda Baby daga baya aka dawo da Little tareda kwad'on zogale aka wa ZAHRA
Sosai taci tayi missing kayan ganye, kunu aka dama mata na kanwa sha'awarsa tai bawa idan babu ruwan nono wadatacce ba
Ana sallar la'asar ta tafi gidan Inna gidan Maigari, Inna inataka saka ina taka ajiye, Su Bintu dariya sukai Inna ZAHRA cefa nan da dare kunyi fad'a, amma kike wani lallab'ata
Ina ruwan ku, ai ZAHRA bamai had'a ni da ita ko Mahmoud dan miji ne shi, amma nasan ZAHRA tafi sona akan sa
Wa yace aini nafison Maikyau akan kowa, shi komai nawane banda kamarsa, Malam da ke kuma aiko ban fad'a ba kunada matsayin da ko Amarya wallahi batadashi azuciyata (Maman ta kenan)
Yauwa fad'a musu, dai haka suka zauna akasha hira har dare
Maikyau bai zauna ba, tare da ya Auwal suka fita, bashi ya dawo ba, sai da akayi sallar Isha'i
Tare aka ci abinci akacigaba da hira, d'akin Inna bata kunna AC yau tun daga parlour har bedroom saida aka kunna
Tare da Inna suke kwana, kullum, kuma haka tacigaba da gasa mata jiki, ga abubuwa datake tsuguno dana sha na gyaran jiki datake bata, bayan wanda Iya da Ummi tabata acan
ZAHRA Yar gata, Babyn ta kowa yana sonta, Malam kullum cikin yimata addu'a yake, ya ringa tofemata al'aurarta da manyan ayoyi
Saida sukayi Sati,Inna tace yakamata kuma tafara zaga dangi daga nan kuma saitaje Gombe da Yola
Amma dai tafara da zaga dangi na kusa da gidan makota da kansa tare da Bintu da Hanan suke yawon dangin Inna na cikin Gayan da Wudil, sannan sukaje Kano gidan Ya Auwal da na Ya Sadees dagidan Doctor Sameer an musu tarba ta mutunci
Jabo da Bena sun musu kirki, Doctor da kansa yadawo da maganar na gwagwarmayar da aka sha kafin biki
Sosai aka ringa dariya, baran da sukaji twins aka haifa, nan aka qara tabbatar da hukuncin ubangiji wani baya haifar d'an wani
Basu kwana ba saboda Inna hanawa tayi, taga take takensa shiyasa yanzu atare suke kwana da ita
Yau Yola za'a tafi dukkansu zasu tafi Su Hanan 9ja ta musu kyau, dan sunyi zagaye sosai anje Minjibir park, Yankari national park, Gidan Zoo kai sosai 9ja ta musu kyau
Amma duk yawon da suke ba ZAHRA ake yin sa, tareda wasu abokanan Maikyau na Abuja da Lagos suke zuwa suma nan Gayan suka zo
A jirgi suka tafi Yola tare da Bintu akaje su kad'ai, shi kuma ranar da Inna tace ana I gobe ZAHRA zasu tafi Yola, aranar shi kuma yace Lagos zaitafi murna Inna tai saboda tana tsoran Mahmoud, shiyasa ma batasaka wani ya bisu ba
Inna manyan gari, kafin Su su isa Yola shi ya isa Hotel yakama yajirayi zuwansu
Hazihi nihayatu qissatu ZAHRAN BABA wa ZAUJIHA MAHMOUD MAIKYAU
*5:56pm*
Dai dai suka isa Yola, a airport qanin Ummanta ya zo ya same su, shi ya d'auke su sai babban gida
A nan dangi kowa yazo yaganta da Babyn ta wanda suka samu zuwa can Dubai d'in da wad'anda basu sami damar zuwa ba
Dangi rahma, wanda bashi da su yai kuka, dan dai dangi indai sunasonka zakaga gata, bare ZAHRA ta kowa da kowa
Feenat qawarta yaranta 3, itama tazo ta ganta, haka suka shafe awowi suna hira, itama Feenat sai da tabawa ZAHRA d'an sirrikan Su na Fulani
D'akin Yafendo ta sauka kakarta, katifa da pillow aka saka musu cikin d'aki guda, ga fanka ga freeing aciki Komai da zasu buqata da akwai ciki
Nono da fura d'an shila gasashe haka aka zube musu, ga Madarar shanu ta usul da aka dafata sukasa tayi sanyi
Hanan taji dadin garin, ganin yanda duk inda sukaje ana karammasu, ga babu qazanta ba sauro, suma masu kud'i ne
Babyn ta batada rigima kamar yadda tazata, kowa saiya fad'i kamarta da ZAHRA, baran yanzu data girma taqara qiba kamarta da Mamanta nadad'a fitowa
Suna zaune qirr wayan ZAHRA qirar iPhone XR tayi qara, ringtone nasa daban ne, da sauri ta d'aga tasan shine
Fita tai saboda hayaniyar da suke
"Hello Habeebty"
'Aiwa habeeby" ya kake ya Lagos da kad'aici?
Dariya yai yace duka fine, amma kad'aici nakusa barin sa, tunda inada mata kusa dani nasan zata d'eban kewa
Maikyau muryanta na rawa tace bangane ba, kana nufin abinda bakayi kana saurayi ba shi zakayi da girman ka, me ye Wanda bana maka har kake tunanin wata daban, dama dan kaje ka had'u da wata kake yawan zuwa Lagos sai kuka
OMG!, ZAHRA I dnt mean dat fah, is u I talk about, kada kimun fassara daban I'm urs nd me too u ar so fell free
Ni bansan jin komai dan nace kayi haquri naqara some months nan gaba shine zaka mun haka?
Hayatee wallahi ba haka nake nufi ba, koda abinda nakeji akanki zai kasheni, Idan baki ban kanki ba I swear bazani gun wata ba
U know i tak smtimes without u before ma ki haihu, nayi haquri so kike nayi cuta kome?, ni nufi na ina Yola ba wani guri ba
Danace miki gani ga wata, ai ke nake nufi, naga kamar bakiyi farin ciki da zuwa naba gara na tafi bye ashafan kan Little
Tsit ya katse wayan yasan zata kira shi, shiyasa yai mata haka
Aikam bai rife baki ba, sai ga kiranta, da qyar ya sakko aka daidaita, sai gasu harda wasa da dariya
Tambayar ta yai ina zasu had'u?, dan yai kewarta, shiru tai, kodai zakizo inda nake sai kisaka yaran gidan su fita dasu Bintu kinga kema saiki zo koh habeebaty?
Huum ya ta iya? ahaka suka bar shawarar gobe yazo yatsaya daga baya sai tazo, dama already yasan gidan
Haka akai, yaran gidan tun safe suka fita dasu Hanan, itama suna fita tasa kai tace zata gidan Feenat da wata qawarta da suka had'u a Oman
Waya taimasa gata zata fito, Huum nayi 10 minutes da zuwa fah I'm waiting 4 u ki ce kingama
Sallama tai musu ta tafi, Motar Hotel en da ita yazo bayan d'unbin kud'in daya zubemusu, aikam ba wata wata tashiga sai Yola new Hotel Maikyau sabone kwana ma kawai 50k ne shiya kama
Parking yai shi ya karb'i Little suka haura sai room en daya kama
Sosai d'akin babba komai akwai, fresh milk da Gashin kaza ta Hausa ya siyamata yaga tanason gashin, ci tayi sosai ta ware suka ringa hira
Basu sukabar wajan ba, sai 4pm, dan kada a nemeta, kamar kada Su rabu, dama haka mata ke komawa Idan suka Haihu ikon Allah kamar yau ya ba're ZAHRAN SA a Leda, gaskiya yai dace
Itama kanta tasan tayi missing gwarzon namiji irin Mahmoud, sosai sika farantawa junan su, albarka tashata har saidata rufemasa baki
A baya ya dureta bayan yacikata da kayan kwalama yasan ZAHRA da cin kayan zak'i
Allah ya taimaketa su basu dawo ba sai wajan 6, haka suka fara bata labarin yawon da sukaje, sun zaga gari
Aifa ansamu abinyi kullum haka zatasaka su fita itama tace taje wajan Feenat ko gidan wasu 'yan uwanta, basu gane komai ba, itama tana kula da takatsantsan da Bintu dan wannan karan anbata amana
Maikyau yau ya tarkata ya tafi, amma dai saida aka Shiga kwaryar manya kafin ya tafi
Tafiyar sa da kwana biyu suma suka fara shirin koma gida
Rakiya akayimusu suma, anmusu abin arziqi su Hanadi anyi Freinds yaran governor da ministers da Senates, sunsha yawo kuma ansha selfie dan har gurin kiwo aka kaisu na wasu kai sunga karramawa
Inna tayi murna da dawowar Su, shima Mahmoud shekaran jiya ya dawo haka tace, ana maganar ya shigo zama yai kusa Inna sannu ya gida Little ya hanya?
Lafiya Lou, Littly tasha hanya k'asa qasa take dariya ganin yadda yake magana kansa a qasa yana basarwa
Alhamdulillah rayuwa taiwa kowa dad'i, Iyayen su na farin ciki da yadda basuda damuwa ko d'aya, dai dai gwagwado kowa na cikin rufin asiri bayada damuwa, rayuwa ta inganta
Maikyau barin su yai, yatafi saboda wani aiki or gently daya taso
*Bayan wata biyu*
ZAHRA ce taketa kwara amai, duk abinda taci saiya fito, wajan kwana 3 kenan tana fama, ga babynta rigima take mata
Tayi fari ta d'ashe abin tausayi, abinci baya zama cikinta
Iya ce data shigo ta ganta a haka, ke 'yan nan saikace mai yaron ciki irin wannan rama haka?
Wallahi maganar danake kenan, ni badan haihuwa tai ba kace qaramin ciki gareta
Ko shawara take damunta, ko malaria dan itace mai saka amai
Yo aisai a kaita Asibiti, dan bazata zauna ahaka ba, bari Auwal yazo saiya kaita, naga yarinyar rigima take ma
Safiya nayi Ya Auwal yazo Asibiti ya kaita gwajin farko CIKI ya tabbata, wata biyu cif
Kuka tasaka ya,za'ayi ace ciki ga 'yarta ko wata 5 bata yi ba, Lallai sai a cire cikin ita bata so Inna zatace ita taje bayan shi ya bisu Yola
Shikansa ya tausayamata, ganin yarinya qarama ace har anyi wani CIKI
Waya yaiwa Mahmoud bayani yamasa, shi murna yafara yace ya jikin nata?
Huum kaga ita tace sai anxubar bazata je gida da ciki ba, kuma ga yarinyar ta qarama kaganta kuka take
Bata wayar Ya Auwal hello kuka tasa, ita wallahi bazatai irinta da ba, saboda haka dole a zubar
Rarrashi ba irin wanda baiyi ba, amma taqi yadda ko ba'a cire anan ba, saina cire da kaina abinda Inna da Iya suka gujemun kenan gashi banji ta suba nayi abin kunya
Fusata yafara yace wallahi Idan taciremasa ciki shida itane, saboda rainin hankali wani nema yake Allah baibashi ba, ke ya baki zakiyi masa butulci
Kakata 'yarta d'aya, ni kuma mu 2 ne, qannen baba na daga mai 3 saimai 4, bamuda yawa amma ke Allah yabaki shine zakice zaki zubar sai kace d'an Shege?, da uban sa fad'a sosai
Huum kagama abinka saina cire, bismillah ki cire ki gani
Ya Auwal ne ya amshi wayan, kagane ta zauna a wajen ka insha Allah ina tawowa nan da jibi ko gobe nasami jirgi zaka ganni ka taimakan plx
Ba komai insha Allah zanyi qoqari, baice komai ba Illa karb'an Little da yai, anan aka ce zata ita ci gaba da feeding nata kafin nan da 5 months
Gidan sa ya tafi da ita, lallab ata yai akan zai taimakamata acire tunda baiso, drip aka sakamata a gidan, Ya Aysha ta tausayamata amma baki take bata akan tayi haquri
Can kuma yaiwa Bintu waya akan ta shirya gobe zaizo zasu tafi kuma a goben, Su Hanan ankoma school, bashiri suka fara shiri
Maikyau ya sami jirgi na rana ma, Allah ya taimakeshi direct ne, wajan 10 ya dira
Idonta biyu, lokacin daya je ai sai fad'a, bari yai tagama sannan yace mata zuwa yai akan suzo Idan akaje Dubai acire acan yaimata fada ne akan Idan ta cire anan Su Iya zasu gani
Amma tasha kuruminta kamar an cire shi, murna tai saiyau tai bacci mai dad'i, kodan ya lafa mata yau oho
Sungama had'a kayansu, acan Safiya nayi Ya Auwal ya d'auko su sai gaya, anan suka tarar da Bintu sin shirya
Shiga yai aka gaisa, basu zauna ba suka dunguma sai gidan Malam sunyi sallama yaimusu abin arziqi sosai haka akayimusu rakiya saboda qiman su da mutunta mutane da suke dashi
Inna koda ta tambaya me likita yace akan ZAHRA cewa akai malaria ce, kuma daga sunje zasuga Doctor, yaqara duba ta
Kowa baiso tafiyar ZAHRA ba, ga little Maikyau kowa saiya sha'awan Babyn
ZAHRA mai farin jini a koina Cikin Ikon Allah suka tafi cikin sa'a suka sauka asa'a, ko cikin jirgi bata kula saba ba wanda taiwa magana abincin bata ciba saboda tsoranta daya kada tayi amai
Azzad da Samar su sukazo tarbon Su, Su Bintu aka d'iba sukuma Iranian Hospital sukai, anan akayi mata check up sosai, magana sukai da Doctor yabashi hint akan abin da zaice mata, ita a k'age take azo acire
Am Madam zauna mana, yanzu zamu miki abinda kike so, amma da sharad'i gaskiya mahaifarki Idan akayi aborting baby, nan gaba bazaki haihu ba, saboda rashin qwarinta Idan kin amince fine muna iyamiki yanzu
Cak tunanin ta ya tsaya, to Idan akace bazata qara haihuwa ba, ya kenan?
Kallon Mahmoud tai, ido ya d'aga mata, kin yadda?, kaga Doctor yimata ina sauri Idan kuma cikin inji zatashiga sai ka sakata
Anya kuwa ai shi inji gaskiya ad'ayan biyu ne amutu ko ayi rai, amma Idan shi take so sai ayi bismillah Shiga mu gani
Batayi magana ba, ta miqe bani 'yata dama sokake na mutu to baka isaba ciki zama daram kuma kazo mutafi gida
Sosai yaji dadin plans ensa ya hau. Doctor magani yabata narage aman da kuma wanda za tasha kwana 8, Daga nan zata iya cigaba da shayara da baby har sai ta haihu
Murna tai, ganin babyn ta ance bazatayi komai ba. Ko da yaimata magana, shiru tai
Suna zuwa Ummi tasamu tafadawa komai wai yace acire cikin har Asibiti ya kaita, nan fa Ummi takama fad'a dama haka yake yanaganin Su basuda d'a amma shi Allah yabashi zaiyi butulci ko yara 100 Allah yabaka inaso Idan kai baka so
Ganin ana masa fad'a kuma har Abee ma daya shigo yasaka baki, sai murna ladan fad'an daya mata
Part nasu tai, anan ya zauna yagayamusu komai, dariya sukai Ummi tace haba naga tana dariya Allah ya inganta
Batayi fushi ba, tunda anmasa fad'a agabanta, itama kuma taji tana son babyn nata, haka suka ci gaba da rainon cikin su cikin kwanciyar hankali
Sultan yana kula da Mohd dashi ake zuwa fada, kusan kadarorinsa yanzu duk yasaka Mohd, matarsa batayi baqin ciki ba, itama haka take bud'e masa share, Yaro dai yaje inda ake sonsa, kuma ana kashi wajan Maman sa dan itace ma take nuna basai an kawo shi ba
Ya Auwal ne yagaya musu yanda akayi, suma dariya sukai Iya tace wallahi nayi tunanin haka, kenan binsu Yola yai Lallai Allah ya shirya yaran zamani
Yanzu dai ahaka da cikin yafara nemar mata admition na Secondary school Al Taufeeq Dubai, kuma ahakan daya fito tafara zuwa
Laulayin kad'an take yi, Little tana samun kulawa Ummi aka bawa ita, itakuma take kula da kanta
Burinsa ya cika, ya Auri ZAHRA, yabawa ZAHRA farin ciki Yasaka ZAHRA a school, yabawa ZAHRA soyayyar dayake fatan bata
Bintu angama komai na maganarta da Azzad saifatan jiran lokaci
ZAHRA kwance akan bed itada Maikyau ga cikin ta agaba, bunch na grapes ne agaban ta take sha, vest ce iyakarya cibiyanta sai wando qarami gashin anyi kitso qanana hira suke akan school nasu, da maganar Madam Ameeru qawarta itama ciki ne da ita na biyu, sin had'u wajan awo
Janyota jikin sa yai, yana qaunar ZAHRA har baisan adadi ba, burinsa yaga ZAHRA na farin ciki, burinsa yaga fuskan ZAHRA da fara'a gashi yana gani
Mafarkinsa shida yaran dayake gani ya tabbata gashi ZAHRA zataqara bashi hasken Idaniya
Soyayyarsa da ZAHRA daga indallah ce, badan tana da wani cikar hallita ba alokacin yaso ta, yaso tane saboda Allah
Allah kabani ikon kyauta tawa ZAHRA har qarshen rayuwa ta
Our lov was so beautiful love story, wch everyone wanted to live bcox it started wth trust, learning then marriage nd by d wll of our God would be everlasting in d enternal bless
I love u ZAHRA, I love Ana bihibak waqif janby aka kulli halin, la takseer Hayatee ana mani ishq bi dunik ya Hayatee Omree
Inti Hayatee, Najwatee, Omree, Lahmee, Damee, Qalbee, Aynee, zaujatul azeeza, jamalu nurul ain, nuru ainee, Inti Waheed minnee, inti Sultanatee wa Ameeratee wa maulatee, Ummul umaratee
Hawaye take zubarwa jin wannan kirari dayake mata, gaba d'aya saita kasa dannewa rungumeshi tai tasaka wani irin kuka, wannan SO har ina gaskiya Maikyau yana qaunar ta
Mirgino da ita yai, ahaka yasaka bakinsa cikin nata suka lula duniyar da banje ba
Anker Jabo Stylich Pharty BB Sahaf duk bamu jebaSai fatan Allah ya sauki ZAHRAN MAIKYAU lafiya
Alhamdulillah da Allah ya nunan wannan rana ta gama Littafin ZAHRAN BABA, Ina Godiya gareka mai iyawa mai bayarwa mai wadatawa mai azirtawa mai kare mumini daga sharrin maqiya
![](https://img.wattpad.com/cover/170777851-288-k976773.jpg)
VOUS LISEZ
ZAHRAN BABA (Completed)🌹
Fiction généraleStory of beautiful villager called zahra.....❤️❤️❤️