11

2K 84 0
                                    


  A'a Inna ai maganar nan, bazata fita ba, ayi dai shiru, tunda tafaru ta qare
Inna ai abin farin ciki ne, kuma naga kema kina zuwa turaka bare yara masu jini a jika, kyalesu
Kyalkyalkyal sai dariya ake sha, Inna ce tace haba takwara har dake?
Eh mana, naji ana wai arufe maganar ciki bayan kowa yasan da mijinta
Hum, sai kiyi nidai ankuyatani kuma lallai saina rama, hhhh Inna dame zaki rama?
Nayadda zaki iya ramawa, saidai Idan zakina kwana damu kibar d'an tsoho, kuma sai in bazakiyi bacci ba, Amma Idan kinyi tabbas sai na turata
Yauwa 'yar gari, inji Inna ta gidan Malam
Kwasar Inna sukaringayi tintana fushi harta ware, juyawa Iya tai tace toke ZAHRA cikin wata nawane?
Yo Iya nima ganin sa nayi, sai yauma nasani daya gayan, amma bansan inada wani ciki ba
Salallami suka fara, kiji shashanci, bara yazo saiya kaiki, amma ace mutum da abu a jikinsa, har ya kai wani lokaci amma bai gane ba?
"Assalamu alaikum"
"Wa alaika salam, yauwa zancenka muke, yakamata asan wataannin cikin, ba'ace an zauna haka ba,
Haka ne Iya, nima yanzu nai tunanin haka, gobe Insha Allah zamuje yanxu ma dan dare yayi
Yauwa sai a hanzarta, muji sauran yaushe kishiya ko miji suzo
Dariya sukai, itadai Inna sai yaqe dan bataso haka ba, amma tayi murna sosai
Haka suka zauna har Isha lokacin mazajen suka shigo, Malam dai dayaji abin albishir murna yai sosai, yarasa Inna zaisa kansa
Kasa zama yai, saidaya dangana da Zaharan, 'Yar Malam, ZAHI BABA kuma, tazama babba, takusa ajiyewa Malam jika
Ya jikin badai inda ke miki ciwo koh?
Babu Malam, yauwa haka nakeson Ji, ZAHRA Allah yara baku lafiya, yasa yazama mai amfani wa duniya
Ameen Baba, yanzu me zakici?, bana jin yunwa, saidai anjima
To ko anjiman me kike so?
Taiba da miyan alayyahu sai asa manja ciki
Yauwa sai me kuma?, shikenan
Kowa dai farin Ciki murna, annashuwa shiyake baran daya kasance bata laulayi sai abin yazo da dad'i
Safiya nayi, Inna da kanta ta had'amata komai na wanka, saboda asibitin da zasu, itama ta ajiye makaman yaqin nata, taga kowa murna yake
Ummin su Mahmoud kanta, waya tamata tana dariya da murna, ta kusa samun jika, Godiya ga sarki jalla wa azza, mai rayawa da kashe wa, mai talautarwa da azurtawa(Allah kabawa marasa 'ya'ya, 'Yaya nagari masu albarka)
*NAGARTA Hsptl* sukaje anan kwararrun Doctors suke, dan Dct Sa'adatu YBK itane ta duba ta, check up sosai akayi mata, sannan tafara basu advice na yanda zasu kula da kansu da baby
Lafiyanta lou da baby, kuma gata da wadataccen jini ajiki, bataga wata matsala da zata Iya affecting wani abu a jikin ta ba
Cikin ya kusan shiga 4 month, amma bai kai ba, dan haka tace wani month tazo afara awo
Murmushi yayi, yace ai jibi zamu koma gida, *Al qusais* dan Ba zamuyi rainon Babyn mu a 9ja ba, koh watermelon?
Kai ta kad'a
Abbansa kasa zama yai shida Ummi, saida suka zo, suma dai farin ciki sukai, anan suka fara shirin komawa gida, Bintu ma ankoma school

   ZAHRA wai bazaki bar wannan yawan ba, haka akace miki yanzu ake wasa jini?, inna kyaleni wallahi dadin hakan nakeji, to ai saikiyi har wani tsalle kike, bara Mahmoud ya shigo, nafadamasa ai
Inna dai anji kanta da 'yarta yau, Ummi ce ta fad'a
      Ummi ai ni yanzu kowa yagama jin kanmu, tunda tayi miji shikenan, Idan ina magana har shigar masa take, zata zo ina zaune
Dariya Zahra tai, to Inna ai miji irin nawa ba abin yarwa bane, Maikyau yanada kirki, yana mun duk abinda nake so
    Nidabanayi shiyasa kike share ni, ba haka bane Innarmu, kece kinfiya sa ido ne
Ni kuma, dariya akaringa yi, ganin Zahara nata tarewa Mahmoud
Assalamu alaikum", yauwa gaka nan, tun d'azu wai langa take na ce tabari wai tafijin dad'i a haka, gata nan
My ZAHRA wai haka ne?, Habeebe kawai fa d'an tsale nayi d'aya biyu, shikenan, kaga irin haka nayi, nan tayi wani tsalle tadire tana dariya
Keh! bakida hankali kike tsalle haka, bayan kinsan bake d'aya bace, shashasha, kuma ba ruwana dake
Maikyau aina dena data fad'an, kawai example namaka kagani, banajin komai, amma kayi haquri, tunda baka so, dama Inna so take muyi fad'a, dan nace bazan bika ba, haka taje cewa na zauna, sorry habeebe, nibazan haqura ba, so kike kimun asarar baby, Ummi kina ganinta kuma?, ni nadena kulaki, bazan qara miki magana ba kuka tasamasa, tashige d'aki
Huum aikin jangab'o aiki Inna, yau sai Allah, aikuwa dai
Shiga yai, kan kujera take tanata kuka, kusa da ita yaje, my Zahra daga magana sai kuka?
To yi shiru kiyi haquri bazan kuma ba, amma kinga aikece da laifi, kinji da kunnanki Doctor tace Idan kin kiyaye zaki haihu lafiya ba ciwo,
Then Idan kina tsalle haka, baby zaki haifa ba handsome ba, kinga sai ana cewa ZAHRA ta haifi baby mara kyau
Kinason ace haka, ashagwab'e tace ni bana so, ni kyakyawa zan Haifa mai irin wannan abin, dimple nasa ta nuna, kuma mai kama da kai
Yauwa to kidena tsalle ko ki kwanta ruf da ciki, Idan kika kiyaye bazamu ringa fad'a ba kinji Tawan?
Naji, amma ai baka sona yanzu, kafison Babyn ka, kamar zaka dukeni fa, kaiyita zagina harda Malam ka zaga
Lailah ZAHRA, banda sharri yaushe nazageki?, rungumeshi tai, tana dariya tace amma dai ka kusa dukana
Rufan asiri na daki rayuwata, to Idan kanaso na haqura yimun goyo, ido ya zaro ZAHRA aikinyi nauyi, ku 2 ne yanzu fa, Allah ni ko kamun ko Idan malam yazo nace ka zageshi
Bayanda yai haka ya duqa ta hau, wayyo Allah zaki karyani bayana, waih dariya tai tace narama nima
To naji,
"Huum Inna ta bakin ki, indai kashiga fad'an su kaizakaji kunya, ji yadda suke dariya
Yo tin yaushe nasan haka, ai yanzu tafi sonsa akaina ma.
Bintu ce tace to Sitti ai mijinta ne, kema kinfison naki mijin akan mu
Uwaki Bintu, kin rainani, amma zan rama wataran
Sosai Idan kaga wannan family en, zasu baka sha'awa, rayuwan su simple, komai cikin ilimi na addini da wayewa ta addini suke
*Bayan kwana 1*
Kusan rabin garin na Gaya Idan ka duba sun fito, badan komai ba, saidan rakiya da ban kwana da ZAHRA
Ba yanda Inna batayiba akan a kyaleta zata kula da ita, amma daga Mahmoud har ZAHRA qi sukayi
Shi Malam ma da tantashine da tuni sun tafi, amma lokaci gashi yau ,azu d'aga zuwa qasar su
ZAHRA ji tayi kamar kada ta bisu, ko Bintu da wannan shine zuwan da tayi wanda ta dad'e itama jitayi kamar kada ta tafi
Kuka suke, qawayenta na tayata, Malam kansa rabuwa da ZAHRA ba sauqi, amma ba yanda zaiyi, aure tayi, kuma dama ya gaji haka
Inna ta gidan su dasu Iya gwago duk kuka suke saikace wadda bazata dawo ba, Amarya ita a gida take bata fito ba. Amma itama taji rashin dad'i dan tanason ZAHRA sosai
Haka dai kowa yagama koke kokensa, akayi masu addu'a sannan mota taja sai Kano ta dabo
Anan suka hau flight daga kano, zuwa Lagos tunda anan zasu hau jirgin
A airport ZAHRA kuka take, ganin dai da gaske ta rabu da Malam da Inna, sai kuka
Lallashinta yake, ajikinsa yasaka ta, har akafa announcement na kiran suna, kaf tare dasu aka kira, ZAHRA tsoranta kad'an ne, tunda ya tab'a zuwa Lagos tare da ita, har Abuja sunje a flight, amma duk da haka ,ZAHRA qamqame Mahmoud tai, kamar wadda zata shige ciki, ahaka suka fara hawa step sannu a hankali har suka cikin jirgin
Su Ummi suna fist class shi a third yake shida Bintu, zama sukai yana riqe da hannunta idonta a rufe ta qanqame hannunsa har jirgin yagama guguwar tashin sa, ya saitu a sararin samaniya
4:30 ya sauka a Lagos, hutun 30 minutes akayi, aka qara fara Shiga, saida ya siyamata abinci taci sannan suka shiga

ZAHRAN BABA (Completed)🌹Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon