1: KUMBAR SUSA

10.7K 883 399
                                    

Kudi kumbar susa, idan ba ka da su sai ya zamto ba ka da murya, ko ka yi magana ba za a ji ba!

Kano, Nigeria

Wai me ya sa mutane ba sa son talaka ne? Har bahaushe ma kan ce wai "talaka ba aboki ba, ko kun shirya ranar biki kwa bata" Irin tunane tunanen da Hindatu ke yi kenen a wata safiyar Laraba. Ta san an ce wai Laraba ranar sa'a ce, to amma sai ta yi wa wannan Larabar taken ranar bakin ciki, ranar ban haushi.

Matsalarta a yanzu bata wuce biyu ba;ta tashi ba ta maganin komai sai naira hamsin! kuma ta wayi gari jinjirinta wanda yayi kwana 40 a duniya yana fama da zazzabi da mura, ciwon da ya kamata ta kai shi asibiti. 'Ya'yanta biyu Abba da Asiya su suka tsira mata ido suna ma ta kallon gasasshen balangu don yunwar da ke azalzalarsu.
Abba dan shekara shida shi ne mai wayo cikinsu ya ce

"Mama, in yi gudu in je in siyo kosan"?

ta yi sauri ta kawar da idon ta daga kan sa, tausayi yake ba ta. Hamsin din dai ita ta ci wa buri tayi kudin mota ta kai jinjirinta asibitin Murtala tunda ba a biyan kudin kati, idan ya so in aka rubuta magani ta karba a wajen Danladi mai kemis na unguwarsu baga baya ta biya shi a hankali. To amma ya za ayi ta bar yara da yunwa?

Da wannan tunanin da zaro kudin ta ba shi ta ce "yi maza ka je wajen karama ka siyo kosan ashirin ka ce ma ta in ji ni..kar fa ka tsaya wasa" ya fice a guje kafin ta karasa. Ya dawo ya bata canjin suka hau kan dan tsurut din kosan suka cinye har da lashe lashen takarda. Ba ta bi ta kan su ba ta saba jinjirinta a baya agogon bango ya nuna karfe takwas na safe cif.

Ta dauki jinjirin da ta sawa suna muhammadu ba don ta yanka ma sa ragon suna ba ta saba a baya,jikinsa zafi rau! ta tarkato ragowar yaran suka yiwo waje. Ta rufo kofar gami da saqalo ta da wani kara ba don tsoron kar barawo ya shiga ya ma ta sata ba sai don cika ala'da. Ta zunkuda goyon bayanta da ke mutsu mutsu ta ce da Abba ta na nuna makotansu

" ku shiga gidan malam wajen Iyami ku ce nace ku zauna a wurinta zan je asibiti na dawo" ba ta bar gurin ba sai da ta ga shigar su.

Ta fara kissawa ranta irin tazarar da ke tsakanin unguwarsu hausawa da asibitin Murtala, sai ta yanke wata shawara. Za ta sabi tafiyar kafa zuwa dangi daga nan ta roki dan acaba ya dauketa zuwa asibiti a naira talatin, a dawowa kuma ta biya gidan mahaifiyarta da ke Kofar Wambai ta samu kudin mota. Da wannan shawarar ta fara tafiya. Gari ne na damina dan haka tsilli tsilin mutane ne akan titi saboda ruwan da aka maka da daddare. A cikin wannan tafiyar ne ta tafi dogon tunani.
*************************
Ita yar asalin haifaffiyar kano ce a wata unguwa da ake kira Kofar Wambai. Mahaifinta ya rasu tun tana karama inda mahifiyarta Hajiya Uwani mai zuciyar nema ta cigaba da kula da su har zuwa lokacin da hindatun ta kamala diplomarta a Health Technology da ke kano. Abubuwa sun fara cabewa ne lokacin da mahaifiyar ta su ta gamu da cutar ciwon ido ta "glaucoma" har ya zamana ta daina gani.

Fadi nan tashi nan Hindatu ta fara neman aiki da dan kwalin diplomarta amma abu ya ci tura. To bata san wani a sama ba,ba ta kuma san wani wanda ya san wani ba don haka maganar neman aiki ta rushe.
Abubakar wanda aka fi sani da Habu yana cikin masu neman aurenta kuma shi ya fi kwanta mata a rai. Soyayya aka yi irinta bugawa a jarida wacce in ba kai ba sai rijiya.

Habu ba mai kudi ba ne,rufin asiri gare shi yana aiki a wani kamfanin robobi da ke sharada a matsayin mataimakin manaja kuma yakan taimakawa su Hindatu. Aka yi biki aka kare aka kai amarya dakinta. Wani abu da ya fara daure ma ta kai bai wuce yanda zamantakewar ta da Habu take neman sauya zani ba. Shi din da ta sani a samartaka mai wasa da dariya sai ya zamana idan ta ji dariyarsa to kallon ball yake inda yan club din su suka yi sa'ar buga kwallo cikin ragar abokanan hamayyarsu.

Auren bai fi wata shida ba gabadaya zaman ya isheta. Dan taimakawa mahaifiyarta da yake ma duk ya watsar suka koma gidan jiya. Dama shi iyayena sun rasu a wajen kawunsa ya tashi,to su ma nan sai ya dade kafin ya je.

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now