15: RASHIN SANI

5K 602 312
                                    

Rashin sani ya fi dare duhu

Kano, Nigeria

" Ya ya aka yi ki ka fada karuwanci?"

Tambayar da Almustapha ya wullo wa Rukky kenen a bazata. Tana rike da wani donut a hannunta ta sa baki ta gatsa kenen sai ta ji tambayar, tayi sauri ta hadiye tana mai kallon inda ta gatsa. Ba ta ba shi amsa ba ta ce

" A ina ka sayi donut din nan? Dadin ba magana!"

Karasowa yayi yana daura agogon hannunsa ya zauna a daidai inda take zaune kan 2 sitter. Ya kai bakinsa inda ta gatsa ya ci ya ce

" A donutfairy "

Ta ce

" Me ke nan?"

Ya kalle ta cikin mamaki ya ce

" Ba ki san donut na donutfairy ba? Kuma kina kano? Ke kuwa wata irin 'yar kauye ce? Ai duk wanda ke kano bai ci donut na donutfairy ba to kamar ya zo kano ne bai ga mota ba!"

Tayi 'yar karamar dariya. Ya sa hannu a cikin kwalin ya dauko wani mai kamar an dura abu a ciki ya kai mata baki ta gutsura.

Ta lumshe idonta tana taunawa kana ta bude suka hada ido suka kwashe da dariya

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Ta lumshe idonta tana taunawa kana ta bude suka hada ido suka kwashe da dariya. Ta ce

" Wallahi sai na ji ni kamar ba anan duniyar nake ba don dadi"

Ya bude wayarsa ya nuna mata ya ce

"Kin ga shafinsu a instagram, order ake

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

"Kin ga shafinsu a instagram, order ake. Ki zama good girl sai a sake miki order. Ko ba haka ba?"

Ta gyada kai tana dariya dama can ba mai yawan magana ba ce. Ya kara maida hankalinsa yace

"Ina tambayarki baki bani amsa ba."

Ta gane me yake nufi fara'ar fuskarta ta ragu ta ce

" Kaddara"

Ya ce

" Ba kya tunanin wataran ki daina"

Ta kalle shi da alama ranta ya fara baci ta ce

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now