18: DUHU

5.9K 619 409
                                    

Haske shi ne maganin duhu...amma yaushe hasken zai zo? Yaushe zai bayyana?

Kano, Nigeria

Kwance yake akan wani katafaren gado da aka lullube da wani lallausan zanin gado. Ji yake kamar yana bacci kamar idonsa biyu. Irin baccin nan da ka kan yi idan damuwa ta yi maka yawa, gabanka na faduwa fat fat.

Kafin wani lokaci ya ji kamar yana kasa numfashi. Sai a lokacin ya lura ashe wuta ke cin dakin.

Wani abun ban al'ajabi uku ne ya sa shi cikin dimuwa.

Na farko baya ganin hasken hutar illa tsananin zafin da yake ji. Na biyu wani DUHU ne ya mamaye shi ba ya ko iya ganin tafin hannayensa. Na uku ya kasa tashi ya gudu daga wannan duhun da ke mamayarsa.

Wannan wani irin al'amari ne?

Kamar babu iska...
Kamar ba ya numfashi...
Kamar baya gani..

Sai gata ta bayyana a cikin duhun, siffarta ce kawai kuma don ita ma bata tare da haske. Ta mika hannu kamar zata taimake shi. Amma sai duhun ya mamaye da ita!

Shin yaushe haske zai bayyana? Abinda yake tambayar zuciyarsa kenen.

Almustapha ya tashi firgigit daga wannan mummunan mafarki ya jike da zufa sharkaf! Har yanzu ya kasa daina jin zafin nan, duhun nan ya matukar ba shi tsoro. Me ke faruwa wai?

Wacce ya gani a duhu tare da shi, ko a mafarki sai ya gane surarta RUKKY ce!To me ya kawo ta irin halin da yake ciki?

Watakila hakan na da dalili na yarda ya sa ta a rai a 'yan kwanakin nan. Ya wayi gari yana matsananciyar kaunarta! Kaunar da bai taba zaton ana yiwa karuwa ba!

Yarinyar ta shigar masa rai ta zauna daram dam. Har yakan ji son kamar wani abu ne da aka halicce shi da shi. Ya lura ita ma ta kamu da son sa da kuma tsananin kishinsa.

Dalilin kenen da ko da wasa bai bari zancen aurensa na sirri da Rebecca ya kai gurinta ba. Zata haukace ne kawai a idonta yake kallon kishinsa da take.

To wai a haka za su kare rayuwa? Wai yaushe zai 'yanta kan shi daga irin wannan rayuwar ta rashin tabbas? Lokaci yayi da zai san abinda yake ciki, shekaru ja suke, kwanaki tafiya suke. Da ya tuna mutuwa sai tsikar jikinsa ta tashi yarr.

Shin ba sharri mahaifinsa ya kulla ba har ya sa yanzu ya fada wannan rayuwar. Shi ba matacce ba shi ba rayayye ba? Kowa ya guje shi harta matansa. Idan ba don shi Almustapha ba yana ga da yanzu ya rube ya lalace sabida wari da rashin kula.

Wani abu ke daure masa kai shi ne, a kullum ya je wajensa a cikin sarkakken harshensa ya kan ce da shi

" Al..mus...tapha...duhu! Duhu shi..mmamaye ni!"

Kamar baya gani amma idanuwansa a bude suke. Haske ya kaurace masa duniya ta juya masa baya. Shin ko shi ne duhun?

Da sauri ya tashi ya dauro alwala ya fara jero sallolin nafilar da ya manta rabonsa da su. Ya san laifuffukansa dayawa, ga shi nan kullum sai tsunduma kan sa yake cikin sabuwar matsala.

Ko da ya je ofis a ranar tunanin bai bar zuciyarsa ba. Al'amarin Rebecca ya daure masa kai. Ya tuna ranar da yayi ido biyu da dansa, sai da ya ji kwalla ta tarar masa. Kamar an tsaga kara.

Shin wannan bai zame masa izina ba? A ce duk zamansa da tsohuwar matarsa khairiyya bai taba samun da ba sai akan karuwa? Wai shin ana yiwa Allah wayo?

Sai ya ji yana so ya kaunaci yaron amma idan ya tuna wai shi ya haifi shege sai gabadaya ransa ya dagule. Kiri kiri ta hana a taho da shi aka bar shi ahannun mai kula da shi acan kadunan wai ita takamar kar ya cutar da shi. Shi ma dai ya ga fa'idar barinsa don hakan ma ba karamin taimakawa zai yi ba wajen adana sirrinsa.

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now