Dare daya Allah kan yi bature.
Abuja, Nigeria
Harabar cikin club din na Luoisiana babu haske idan ka cire jajaye da korayen fitilu masu kawowa da daukewa wanda aka fi sani da "disco light". Kowa harkar gabansa yake yi.
Masu rawa nayi, masu shan taba ko wiwi , masu kwankwadar giya kowa na aikatawa daidai da halayyarsa.Wasu kuma da suka daukin hakan karancin cinyewa suna zaune a VIP a wasu kalar kujeru masu hade da tebura, suna hirarrakin da ya shafesu tare da shan abunda yayi daidai da raayinsu.
A wata 'yar kusurwa kadan da babu mutane wata mace ce a zaune ita kadai. Kallo daya za kayi ma ta ka san wayayyiya ce a bariki. Ta sa wata riga mai kama da ta bebin roba iya gwiwa, gashin izgar dokinta ya ziro har kafadunta.
Ba ta cewa kowa kanzil ba wadanda suka tanka fa ma sun gaji sun tafi. Ba ta da wani aiki sai zukar taba don har ta kusa tashi da kwali daya a a tsawon zamanta.
Ta kuma jan tsaki a karo na ashirin ba daya, a rayuwarta ta tsani jira sai dai a jira ta shi ya ta ta kagu. Ta jefar da kwanson tabar da ta shanye ta janyo wani karan ta kyasta,zuka daya tayi ta ji an janye daga hannunta.
Cikin tsanannin mamakin son ganin wanda ya isa ta dago kai tayi ido biyu da wani rusheshen mutum mai uban tumbi. Ya saka wani burgujejen wando tiri kwata da wata katuwar riga, ya dora hular inyamurai a ka.
Ya zuki tabar ya fesar ma ta a fuska kana ya ce
" Baby girl sunana tobacco kin ga kuma ban miki adalci ba a ce ina raye na bar ki ke kadai kina tayar da hadari a gizagizai"
Ta dan nisa ta jingina da kujerar da take zaune ta zuba masa ido. Yana murza hannayensa ya ce
" Gaskiya ana sanyi a garin nan anya ma kina jin sanyin nan kuwa?"
Bata kula ba sai ma tace da shi
" yaya aka yi ka gane ni?"
Yayi wani guntun murmushi ya ce
" kina sanye da fuskar 'yan wasan karta"
Ta yamutsa fuska don bata gane ba ya ce
" poker face"
Ta gyada kai, ta gaji so take a wuce gurin. Shi kuma sai taga ya daga hannu ya yafito sabis na club din ya fada masa irin kalar giyar da yake so ya kawo masa aka kawo. Ta ga an rubuta blue crystal ba ta taba ganin irinta ba, ta basar wannan ba damuwarta ba ce.
Ya zuba a tambulan ya kwankwada sau daya, watakila wannan ne maganin sanyin da yake bukata. Maganar shi ce ta katse ma ta tunani da ta ji ya ce a tsaurare
"Ina sakona?"
Tayi masa kallon tsaf, sannan ta zuge jakarta ta zaro wani nadi a takarda a farar takarda. Ba ta mika ma sa ba sai ta ajiye akan tebur. Ya sa hannu a aljihu ya jawo wata siririyar ambulan ruwan kasa ya ajiye a daidai saitin da ta aje sakon nasa.
Ta sa hannu zata dauki ambulan din ya kai hannu ga danne ya ce
" not so fast..baby girl..not so fast"
A tare suka janye hannu. Sai ya dauki wannan farar takarda ya bude ya kai hancinsa kamar mai shakar hodar iblis. Ya dandana da bakinsa ya jinjina kai ya ce
" komai yayi kyau"
Ya zira a aljihu ya mike. Ya dauki kwalbar giyarsa da bai karasa ba yayi gaba abunsa ba tare da ya waiwayeta ba.
Ta dauki ambulan din. Kaurinta ya sa ta san ba kudi ne dan kadan ba. Ta jefa a jaka. Bai fi minti biyar da fita ba ta janyo waya kirar samsung ta danna wata namba, a ringin na uku aka dauka. Ta ce
YOU ARE READING
Mai Tafiya
AdventureLabarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeri...