Abinda ke cikin zuciya ai sirri ne!
Kano, Nigeria
Iliyasou Tillaberi ke zaune a daya daka cikin kujerun ofishin Al Mustapha na I and A group of companies. Kallo daya za kai masa ka gane ya sha jinya jikinsa ya nuna matsananciyar rama. A hannunsa wata sanda ce da yake dan dogarawa irin ta masu kudi.
Al Mustapha ke zaune yana fuskantar sa. Ya riga ya sanar kar kowa ya shigo ofishin suna ganawa da mahaifinsa. Bayanai yake yi masa akan wasu kamfanoni da suke son siya su mayar da su masaka. Uban na saurarensa har ya gama ya ce
"Komi hwa yana yin kyau aikinka yana kyau. Ita dukiya ba a barinta ya wannan, juyata ake ta hayayyafa hal 'ya'ya da jikoki. Tilas idan kana so hwa ka girma kayi kasaita ka buwaya sai ka zamne na kasanka ka dakusal da su ya zamana ba a kallon kowa sai kai! Yanzun wannan da danuwanka da ran shi tare za kuyi komai. Allah kyauta makwancin shi"
Almustapha bai ce komai ba ya tabo masa abinda ke masa ciwo a zuci. Kuma bai ga dalilin da yasa zai jajanta ba bayan shi ya jawo. Wani irin abu yake ji kan uban da ya kasa fassarawa. Sai ya gwammace kawai yayi shiru.
Uban ya tsaya yana duban dan yana kallon yanayin fuskarsa ya ce
" Diba yadda cuta ke neman halakani yarona...kamata yayi ka zubal da komi ya wuce. Rayuwace fa gaba gareka ga tarin dukiya nan ubanka ya nema maka. Mi zai dame ka?"
Ya kalli uban kamar yanda zai kalli sa'ansa ya ce
" Ina gaya maka hakkin Ahmadou ba lallai ya barmu ba. A nemo yarinyar nan. Abba na roke ka a nemo yarinyar nan"
Wani irin kallo uban ke masa na tsananin mamaki. Ya rasa wannan irin bala'i da me zai ji ne wai? Shi duk 'ya'yansa maza da yake alfahari da su ba su da magana sai ta wannan yarinya?
Babu abinda ke damunsa irin mafarkan da yake da Ahmadou. Ya kan gan shi yana masa fushi yana tunkuda shi cikin wani rami. Babu ranar da zata wuce da bai yi shigen irin wannan mafarkin ba. Abinda ya hana lafiyarsa daidaita kenen. Ya sa damuwa da fargaba a ransa jinin sa sai kara hauhawa yake.
Ya tuna irin shigen ficen da yayi na jawowa Ahmadou masifu na karayar dukiya da sanadin mutuwarsa. To amma kamar Ahmadou din ya bar wata halitta da take neman fito na fito da shi. A dalilin hakan ya rasa dan sa yanzu kuma Almustapha na masa zancen banza. Ya dake irin na mazan jiya ya ce cikin nuna alamar gargadi
" Idan har kana kamnal muyi shiri da kai to ka tsaya inda nicce maka. Idan ka ce za ka shiga wannan magana kuwa..ma gamu!"
Da haka ya kokarta ya tashi, tashi irin na jikin tsufa. Almustapha ya taimaka masa. Ya raka shi zuwa waje gurin zungureriyar motarsa ya bude masa mazaunin mai zaman banza ya zauna. Ya dago ya kalle shi a tsanake ya ce
" Na tuna. Ka je gidan abokina Abbassodor Mukhtar, mun tattauna mun yi za ka je ka ga diyal wajen shi ku zanta. Ya kamata a ce yanzu wannan ka ajje mata hakanan. Kai da ka ke dulmiya kan ka cikin halkokin siyasa ya kamata ka ajje mace don a kalle ka da mutumci. Kal mutane su ga hakan a matsayin gazawa.
Duniya ita ake yiwa bauta gwamma ka moreta lokacin da kake da rai. Ranar da ka zamo babu wani ne zai maye gulbinka."
Gyada kai kawai yayi. Wasu maganganun sun shiga zuciyarsa sun zauna, ya fara hangen duniya a wani waje mai dogon zamani da zai isheka ka cika burirrikan ka. Suka yi sallama shi kuma ya dawo ofis.
Ya cigaba da juyawa akan kujerarsa tunani sun masa yawa amma akwai wani abu da ke damunsa a zuciya. Ya kasa manta fuskar wannan yarinyar da ya gani da Luba.
Shi mutum ne mai tsananin taste din yanmata. Farkon ganinsa da Luba ya ga ta masa zata cike wani gurbi a wajensa to amma kallo daya yayi wa kawar ya ji yana so ya kara kallonta. Yanayin idanuwanta ne suna masa wani irin kamanceceniya.
YOU ARE READING
Mai Tafiya
AdventureLabarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeri...