Duniya budurwar wawa...kowa ya daka ta tata ya sha kuka!
Kano, Nigeria
Ahayye..yau ana shagalin duniya a gidan nan" cewar 'yar Modu " gaskiya ku din nan an yi 'yan kwal uba! Kamar lokacin da uwarku take da cikinku ta zagi ubanta! Wannan balbalcewa haka.
Ko da yake zaman duniya ai ta gaji haka..in dai da ranka ai dole sai kayi motsi. Rayuwa idan ba ka daga 'yar kwalbar nan kana dan zuke zuken nan ya kwakwalwarka za tayi kiliya? Ai sai dai bakin cikin duniya ya yasarka a gindin kwalbati irin yadda ya yada uwata da tayo cikina a kwararo. Billahillazi bata mike ba sai da ta sankato ni! Ahayye Allah raba mu da takaicin duniya...cas!
Rukky ce ta kalle shi tana dariya
" Dama 'yar maduwaye kai shege ne? Katakatan uba! Haba dole tambadewar tayi yawa ka ce tsotso kayi a nono..hahaha" ta kwashe da dariyar ban haushi
Yayi sakaka da baki
" Yo ke uwar taki da tayi cikinki ta hanyar halas alfahari tayi da ke? Ku ji ni da karamar 'yar iska. Me kika fasa?kwanan gida ko sane? Ko kuwa idan kun hallara a gaban Allah ana gobe kiyama za ta nuna ki a cikinmu ta hada ubangiji ya jefa ki jahannama? A billahillazi Rukky yanda na san zan mutu haka na san sai mun dandani wuta! Duniya gidan dadi! Allah kar ka kashe mu bamu tuba ba...ahayye nanaye! Gargadi na karshe kar ki kara sani a jinsin da ba nawa ba..To kin ji!"
Hindu tayi caraf ta ce
" Amma 'yar moduwaye an yi dan tselan uwa Rukky ka ke cewa za ta shiga jahannama? To kai gida Allah zai gina maka a aljanna? Akwai abunda ma ya kai daudu zunubi?"
Maimakon ya kula ta sai ya dauko karan tabarsa ya kunna ya fara zuka ya ce
" ke Hindu shi zunubi yana da kankani yana da mai yawa ne? Yo Allah na tuba ko da sata a ka bar ku ai sai dai ku hango mu a karshen siradi mun tsallaka mun bar ku. Ai wuyarta kan ka mutu kayi taubatan nasuha cikakkiyar tuba kenen. Ka kuma shaidawa Allah ba zaka koma i zuwa wannan aikin zunubin ba. Yo ke 'yar nan ba ki je islamiyya ba? Dan ahalarin nan ma ba ki haddace ba?"
Hindu ta zuba masa ido da mamaki ta ce
" Ta ce wai kai anan din nan har islamiyya ka je? Amma a bige da daudu? Wanda ya sani ya take shi Allah ya fi hukuntawa!"
Ya kalleta yayi sakkaka da baki karan taba na reto a lebensa ya ce
" Allah jikar Alaramma wacce aka yi cikinta aka haife akan dandamalin masallaci! Aka yiwa uwarta wankan jego da ruwan alwala! To duk yadda aka kai ga tofe ki da kul'a'u zai idan ba ki shuka khairan ba ba ki tadda shi gaba! Ehe kin ji na gaya miki.
To 'yar ni din nan da kika raina izifina 20 cif! Hadda kuwa tun daga alhamdu abunda yayi izza sama'u zuwa kulu hiya babu wacce ban iya ba! Kin ga kuwa ina da na sallah wacce muke dan jejjefa ta haka kar abun yayi mana yawa. Babun badiluhu..mu ba tsinana abun arziki ba mu ba mu zauna a musuliluncin ba. Kin ganni nan Alquran Hajiya nike don bara biyu da ta wuce na je aikin hajji na sauke farali..ai aljanna ta mai rabo ce! Ahayye...cas!"
Hindu ta karkace kai ta rangada guda 'yar Modu ya bata hannu suka kashe. Ran su tas suna ganin duniya ba a bakin komai ba.
Duk wannan shagalin da ake a Gidan Hajiya Kububuwa ne a wani tangamemen falo kuma ba su kadai ba ne a ciki. A can gefe kowa shagalinsa yake..yawa yawansu wasan karta suke. Wasu suna gefe suna shaye shaye.
In da su Hindu ke zaune su hudu ne. Hindu, Rukky , Luba sai 'yar Modu. Duk wannan hirar da suke ita Luba bata sa baki ba. Ba ta da wani aiki sai zukar wiwi dama gwanace amma tana saurarensu tsaf. A lokacin ne ta ga Rukky jikinta yayi sanyi da maganar da 'yar Modu ya dankara ma ta. Kawai sai ta tashi ta nufi inda take ta cusa ma ta tabar wiwi a baki ta ce
YOU ARE READING
Mai Tafiya
AdventureLabarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeri...