Ina mafita? A lokacin da babu mafita!
Kano, Nigeria
Washegarin rasuwar Muhammadu Hindatu ta tattara na ta ya na ta ta koma gidansu, 'Yanuwa da abokan arziki suka yi ta zuwa ma ta gaisuwa.
Ta kudurce a ranta cewar idan fa bata nemi mafita ba to da daya da daya sai ta nemi 'ya'yanta ta hange su a hannun mutuwa.To zaman gidan ma jiya i yau. Makauniyar uwarta na nan yadda take da kannenta gudu uku mata, sai ita cikon ta hudu da 'ya'yanta biyu cikon biyar da shida wanda suka samu mazauni a dan tsukakken dakin mutum biyu. Maza yanzu ba sa son zawarcin mace mai 'ya'ya in dai ba dukiya aka bar musu ba, don haka daga mutum ya zo daya, biyu sai ta ji dif.
Wani abu da ya fi daure ma ta kai da kuma ba ta haushi bai wuce gani ganin da kannen nata ke ma ta ba suna ma kallon wacce ta zo ta takura musu. Wani mugun raini ne ya shiga tsakaninsu kamar wacce kan ta aka fara zawarci. 'Ya'yanta sai suka zama ganguna sai dai ka ji tim! An kai musu duka ba gaira ba dalili.
Lokacin da tana gidan Habu tana 'yar sana'arta ba ta taba zuwa gida ba tare da ta ruko musu dan wani abu ba don haka anti sama anti kasa. Amma yanzu da suka gama gano ba ta da wata mamora sai kawai aka guntule antin aka yar a juji ake kiranta Hindatunta sak.
Ranar wata Alhamis ana kiran sallar La'asar Hindatu na alwala a bakin rijiya, kanwarta mai suna safara na zaune a bakin kofar daki tana cin taliya da manja. Can kamar an koro Abba ya shigo a guje da gare-garensa daga kofar gida. Sai ya tsaya cak a gaban Safara ya kura ma ta ido saboda yunwar da ke addabarsa . Ta kai lomarta ta hudu kenen ta ankara da shi ta ko galla ma sa harara ta ce
" Uhun..ya na ga kana kallona kamar ni na kori ubanka?"
Hindatu ta dago kai daga alwalar da take tana so ta gane abunda yayi zafi har safara ta jefi Abba da magana irin wannan. Ya kalle ta bayan yayi narai narai da ido ya ce " Anti Safara yunwa nake ji in zo in ci?" Bai karasa ba ta ce a fusace
" Ca akai maka ta ubanka ce?! Ku ji ni da tsinannen yaro" ta mika hannu ta rankwashe shi.
Hindatu kamar ta share amma sai ta tuna anyi haka ya fi a kirga. Sai ta ce" Safara kan abinci ne kike zagi har da rankwashi? Ba dan ki ba ne"
Safara tayi caraf ta ce" kut, ku ji Hinden nan. Yaro ba tarbiyya ba za a koya ma sa ba? Ko kuwa tambayar da na masa ce laifi? To karya na yi? Na ubansa ne?"
"Da sauki tunda ubansa ya taba kawowa har kin ci kin goge baki" cewar Hindatu saboda ranta ya fara baci. Cikin rashin kunya Safara ta ce
" Kin ga Hinde, ba ni na kar zomon ba ratayar ma ba a bani ba. Kan Abba ne kike nema ki gayamin magana ko ni na ce ubansa ya gudu ya bar ki ba ci ba sha? Kawai kin zo gida kin cushe mana guri ke da 'ya'yanki gayyar kwarkwata gayyar kudin cizo!"
Hindatu ta katse alwalar da take ta iso inda da Safara take ta nuna mata dan yatsa ta ce
"Kar gigin tashen balagarki ya kai ki ki zageni don kin yi kadan kin yi tsararo. Gwara ni na auru ke ki gayamin karen da ya zo ya shinshina takalminki a tsawon zamaninki!"
Toh fa! Wannan magana sai ga harzuka safara har ta dangwarar da kwanon taliyarta ta mike daidai da tsawon Hindatu ta ce
"Na rantse Hinde da aure irin na ki billahillazi gwara na mutu ba mashinshini...auren wahala..auren bakin ciki!"
Ai kafin ka ce me Hindatu ta fizgo ta an fara dambe kamar wasu dadaddun abokanen hamayya. Abba ne ya tafi da gudu ya je ya kira uwar ta fito tana dogara sandarta. Ta daidaici inda take jin rubdugun damben ta kwada sandarta ta na cewa
" Ba ku isa ku saka min hawan jini ba don ba ni kadai na tara 'ya'ya mata ba a layin nan". Suka rabu aka mayar da yanda aka yi ,budar bakin uwar sai ta ce
YOU ARE READING
Mai Tafiya
AbenteuerLabarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeri...