Almustapha gwani....makwafin gwani!
( ina so mai karatu ya gane cewa momodou na cikin labarin rokaiyatou ya mutu! Wanda ya mutu kuma, baya dawowa. Almustapha danuwan Momodou ne, babansu daya. Ku duba babi na 6 don karin bayani. Kalamai da ake amfani da su mararsa kyau a labarin an yi haka ne dan nuna ainihin yadda alamarin yake, ba don a habbaka su ba. Ayi hakuri da hakan)
Kano, Nigeria
Sau dayawa a rayuwar dan adam mutane kan aikata laifuffuka da suke gani ba a bakin komai ba. Zamani ya zo mana da wasu halaye da suka zama ruwan dare. Zinace zinace, shaye shaye, tsubbu da sauransu.
Ka dauka cewa a rayuwarka kai matafiyi ne duk tsawon tafiyarka akwai inda zaka kare. Za kuma a tambayeka abubuwan da ka aikata a hanyarka ta zuwa wannan guri. Wani tanadi ka yi? Ka tabbata lokacin da aka nuna maka tafiyarka cikin majigi za kayi alfahari da kan ka?
Ga duk wanda bai san Almustapha Iliyasou Tillaberi ba to a anan ya gama cutarsa. Yana da fuskar kamala da za kayi zaton mutum ne mai tsantseni wajan aikata zunubi. To sai dai me? Sau dayawa mutane na sanyawa jikinsu wata riga mai badda kama. Akuya da fatar kura!
Da ne ga Hajiya Hadiza da iliyasou Tillaberi. Ya taso cikin gata da tsananin soyayyar uwa da take ganinsa da daya tilo.
Almustapha da Momodou 'yanuwan juna ne kuma aminan juna. Sun yi zumunci ba tare da iyayensu sun damu da suyi hakan ba. Momodou ba shi da wani abokin shawara sai Almustapha musamman akan soyayyar shi da Rokaiyatou. Almustapha ya ba shi goyon baya dari bisa dari abinda ya rasa a duk cikin yanuwansa.
Almustapha yayi wa Rokaiyatou ne sani tun tana zanin goyo don haka har yau ba zai iya tantance ta ba a cikin mutane. Momodou ya sha masa mitar ya zo su gana abinda ya sa ya ce zai zo Niamey kenen. Zuwan da aiki ya rike shi suka yi da momodou zai taho shi kuma momodou din ya wuce Tillaberi a daura musu aure sai su hadu a Niamey. Daga nan zasu taho da shi, momodou, Rokaiyatou da Momma. Yana taya danuwansa murna yana taya sa samun abinda yake so. Sai a lokacin shi ma ya fara tunanin aure.
Momodou da Almustapha sun riga sun gane halin mahaifinsu sun kuma rantse ba za su goya masa baya ba. Suka yi ajandar cewa amarya da angon zasu karasa shiri a Nigeria su wuce nairobi inda momodou ya samu aiki. Shi kuma Almustapha ya cigaba da kula da harkokin biznes din su da zasu bude babbar hedkwata a kano.
A wannan shirin na shi na zuwa Niamey ne ya ji wayarsa tayi kara. Yana duba ya ga momodou ne dariya ta subuce masa ya san ba zai wuce zancen aure ba, inshallahu su ke da nasara. Daga jin alama Momodou din akan hanya yake don yana jin karar iskar mota. Ya ce
" Hello..Frere"
Network ke yanke maganar sai ya ji baya jin sa. Ya kara cewa
" Heloooo..."
Muryar momodou kawai ya ji yana cewa
" An damra..Mustapha an damra.... amrena da Rokaiyatou" sai ya ji wayar ta dauke.
Dariya ya kama yi, ya ji abunda yace sai yake ta kara kokarin kira. Wayar ta ki shiga. Sai ya hakura ya fara shirye shiryen wucewarsa Niamey. Ya san dole ya je don wannan fadan da suka tarko da mahaifinsu ba mai karewa ba ne. Shi dai yana bayan danuwansa ko ana ha maza ha mata bai ga dalilin da zai sa a hana masa abunda yake so ba!
Abu daya ne ya sa bai je da wuri ba, daga Abuja ya hau jirgi za shi Niamey sai yayi missing flight. Har a lokacin yana gwada nambar momodou bai samu ba. Sai ya fara wani tunani kar ya tafi niamey shi kuma momodou da Rokaiyatou sun taho nigeria a samu sabani. Sai yayi tunanin bari ya kwana in ya so washegari sai suyi waya su tsara yadda abun zai kasance. Ya riga ya kira wani abokinsa a immigration ofgice da zai yiwa Rokaiyatou fasfo a kwana 2 daga nan sai ya shigar musu da biza. Da wannan ya kwana a rai.
YOU ARE READING
Mai Tafiya
AdventureLabarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeri...