2: KANTAFI

10.7K 683 338
                                    

Ina aka je? Ina za a dawo?

Saudi Arabia

"Hajiyya goro"? Balaraben ya tambayi wata mata da ke fitowa daga harabar "airport" din Jidda a cikin gurbatacciyar hausarsa. Matar ta girgiza kai tayi gaba cike da takaicin goronta da aka kwace a wajen screening . Ranta ya cigaba da raya ma ta dama a gida Najeriya ne, ta bada cin hanci ta wuce da shi ta ci kazamar riba.

Wannan abun da ya faru akan idon Lubabatu wacce ta sha bakar abaya da nikabi baka hango komai sai fararen idanuwanta. Can ta hango wata mata lukuta ta fito da sassarfa tana tafiya da kyar kamar kwai ya fashe ma ta a ciki. Luba tayi sauri ta mike ta cafki hannun matar ta ce

"Salam ya ukhti..Hajiyya barka da zuwa barka da zuwa na ga alama akwai goro ko?"

Hajiyar ta kalli Luba da mamakin yadda ta gane yayin da takari maza da mata suka yanyame ta da rokon ta siyar musu. Amma sai ta ki, ta tsayar da Luba akan dalilin ita ta fara taryo ta. Suka sauke goron ta na mai bawa Luba labari

" Ai duk cikin 'yanuwana ni kadai na samu na ketaro da shi yau sa'ar a kaina take. Abokanan tafiyata an kwace musu har da masu kwarya goma! Amma kin ganni nan sai da na haye da kwarya takwas!"

Luba tace " Mashallah mashallah"

Sa'annan ta daga baki ta kwalawa Hajiya 'yar Sakkwato kira ita kuma tayi ma ta alama da hannu cewar ta na zuwa. Suka yi ciniki ta biya ta kwashi goronta tayi gaba suka hade da Hajiya 'yar Sakkwato tana murmushin mugunta ta ce

" ai halin na ma ta ,na ga sabuwar hajiya ce ko kan lisafin riyal din ba ta sani ba"
Suka kwashe da dariya. Hajiya Yar Sakkwato ta ce

"Kwanda da kin kai ma ta haka. Duka nawa an ka saida huhun goro ga kano? Amma dan Allah ya bisshe su ga sa'a sunka hawo da shi ,sai su lumka mishi kuddi su saida shi da tsada bayan mu abun kai baka kawai munka bida" .

Luba ta gyara nikab dinta tayi murmushi ta ce

" Kin ko samu kin sayi man bilicin din kin san fa kwanan nan shi ke kawo kudi."
Hajiyar ta saka hannu a ledar hannunta ta nuna ma ta ta kara da cewa

" har atanhwa ta jikka bibbiyu ni ssiya sai mu siyarta ga uwani mai tuwo na ji tana bida"

Suka rankaya za su fita Luba tayi sauri ta ce " au ki tsaya mu duba ko an kawo maggi star kin san fa yanzu zuwan 'yan umara ne, su in ba su ji maggin nan zai! a abinci ba babu magana". Da kayan da suka siya daga hannun matafiya 'yan Najeriya suka koma Makkah. Nan da nan fa sai kasuwa ta bude, suka raba goron nan bari bari suna siyarwa larabawan nan mayun goro su kuma suna rububi.

Idan da mai karatu zai ga inda su Luba ke kwana a unguwar Sharu mansur da Sharu sittin sai abun ya bashi mamaki. Anan za ka ga mai siyar da tuwo, waina, shinkafa har da danginsu gyada da aya. Dakin kwanansu Luba wani tsukakken daki ne a can saman bene su goma sha uku ne a dakin kowa akan 'yar yaloluwar katifarsa. Daukacin jama'ar wannan daki ba sa dauke da takardar shaidar zama ta dan kasa igama, a takaice dai bakin haure ne.
Luba da Hajiya kan yi tuwo,suna kuma sayar da kayan sare saren da suka samo daga 'yan Najeriya. Sa'annan Luba kan dauki kayan yara da dan kananan siturunsu masu saukin kudi ta kulle a zani ta kai bakin "Harem" .Duk inda suka ga askar to fa sai su fyalla a guje ita da ire irenta , don idan aka kama ka yanzun nan ka sha zaman" sijjin"daga nan sai kasarka ta gado.

Idan lokacin Ummara da Hajji ya wuce sukan yi aiki a gidajen larabawa kamar su wanke wanke, shara, raino da sauransu. Wadannan aiyukan da bakaken fata kan yiwa larabawa shi ke sawa suke musu kallon kaskanci a ganinsu kowani bakar fata matsiyaci ne, boyi boyi ne. Don haka kyara ta dalilin banbancin launin fata (racism) yayi yawa yayin da aka samu rangwame na rashin sanin darajar kai a wajen bakaken.

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now