Haske maganin duhu. Haske ya bayyana, duhu ya yaye.
( last chapter)
Kano, Nigeria
Shekaru dayawa sun ja dauke da abubuwa daban daban.
Tsaye suke a gaban sasshen SS wali na Asibitin AKTH inda ya danganci kula da masu cuta mai karya garkuwar jiki.
Abba ne da mahaifiyarsa Hindatu, hannusa rike da ledar magunguna. Shi ne ya kawo ta kamar yadda ya saba, suka doshi wata jaramar mota kirar starlet. Fuskarsu kadaran kadahan suka shige suka fice daga asibitin.
Abban ne ke cewa
" Ai mama, idan na samu na ajiyeki. Yanzu yanzun lodi zan yi na je Dutse na dawo kafin la'asar. Sai ki ga wasu 'yan kwabbai sun shigo hannuna."
Wani irin kallo Hindatu ke masa tana son yin dariya tana kunshewa. Cikin mamaki ta ce tana mai nuna masa dan yatsa
" Anya Abba! Anya kuwa nan kurkusa akwai mai son jarabar neman kudi irinka? A kofar gida ka kafa tireda, kana kanikanci, kana koyarwa a islamiyya, yanzu juma ka tsiri lodi zuwa jigawa. Dazu dazu aka kira ka wai interview din da kuka yi ka ci, an dauke ku aiki. Wannan neman kudi da me yayi kama?"
Wata irin dariya ya kwashe da ita har da buga sitiyari ya ce
" Ka ji mama! Na san babu wani abu da ya fi ba ki haushi irin tiredar nan. Mama kin raina tiredar nan. To jiya jiyan nan da aka siyo miki zabuwa kika sashe baki da kudin tireda ne!"
Dariya take, ta kama baki ta ce
" tiredar?!
Ya ce
" Ahaf mama! Ai ku ne kuka raina sanaa. Mutane sun fi so su jira aikin gwamnati to ina aikin gwamnati yake? Yanzu wannan tiredar da kudin bautar kasata na kafata. Da a ce mutane za su dauki hanyar rashin dogaro ga aikin gwamnati su kafa kan su da kansu ba tare da sun sa girman kai ba, to da an yaki talauci. Yanzu da kudin wannan tiredar sai ki ga an dallo miki suruka!"
Ware hannayenta tayi guda biyu ta masa dakuwa ta na cewa
" uwaka! Ka ga marar kunya, ni kake wa maganar suruka. Ka mai da ni kakar ka ko"
Suka kwashe da dariya
Ran Hindatu wani farin ciki ne jin ya ambaci aure. Tana fatan ta ga auren Abbanta. Ko za ta kai?
Ya ce
" Ba ga shi ba yanzu aikin ya samu daga Allah. Kafin ya samu fa ai da sai mu zauna mu nade hannu muyi maula? Allah ya ce tashi in taimake ka. Babu maraya sai rago mama!"
Shiru tayi tana nutsar da maganganun Abba. Ya lura zata fada tunani ya ce
" Ehem..ehem"
Ta ce" ya dai?"
Ya fara shafa keyarsa yana cewa
" Yau ma fa na ga mutumin naki a kofar gida kafin mu taho. Allah Mama yana wahala"
Take annurin fuskarta ya gushe, ta san maganar mahaifinsa yake. Mutumin da ba shi da wajen ziyara sai kofar gidansu idan ya bushi iska, duk wai don ta yafe masa.
Ya lura da daurewar fuskarta ya ce
"Mamah..."
Ta dakatar da shi da sauri idanunta fal kwalla
" Abdulhakeem!....ka da ka ce Allah ya ce na yafewa mahaifinka! Dan Allah kar ka ce!"
Ya ga yadda hankalinta yake neman tashi ya dafa kafadarta ya ce
" To shikenen. Ka da ki damu. Yafiya abun so ce amma ba tilas ba ce. Allah ya ce ayi koyi da hakan amma ba dole ba ne. Ita wata aba ce da kan zo daga zuciya. Idan har bata zo miki zuciya ba sai a hakura."
YOU ARE READING
Mai Tafiya
AdventureLabarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeri...