Ranar wanka ba a boye cibi
Kano, Nigeria
Hindatu ce ke zaune a gaban mudubi tana kwalliya, tayi da wani maneminta zasu hadu karfe hudu na yamma daidai. A wayarta ta saka wata wakar sa'adu bori da take so tana bi da baki
Lale hadiza lale lale hadiza yar malummai ka ga hadiza ta birgeni
Ina cikin yawona ka ga hadiza ta birgeni
Yara suna kiranta amare manya suna kiranta amare
Zama da kishiya tilas ne ba don uwargida na so ba!
Kai! Duniya tana kaunar Saadou Bori Allah dai ya jikan sa. Anya idan ta tashi aure da Alhaji Awaisu ba za ta kira yaron saadou bori ya wake su ba? Irin arzikin Alhaji Awaisu ai sai da haka yanda za ta fantama a cikin kawayenta.
Ita yanzu duk yanda za a yi bata iya auren wanda bai tara dukiya ba, wanda ba zai gina mata tamfatsetsen gida ba da motoci na alfarma suna harabar pakin. Ya bata ko da miliyan goma ne ta hado lefe na kece raini, Allah ta tuba ina tsiya tsiya ina miliyan goma a wajen Alhaji Awaisu! Ai wuce nan.
A cikin akwatin ajiyarta ta banki ma jiya miliyan 2 ya sa mata duk da ta ji dan sa ya kira shi daga zaria inda yake makaranta kan cewa lokaci yayi na biyan kudi kuma yace baya da. A wayarsa uwargidansa ta dau nambarta ta kira tayi mata zagin uwa da uba. Har da cewa wai
" Halin da kika sani ni da 'ya'yana da sannu sai kin fada! Inshallahu sai kin yi kuka da idanunki!"
Ji wani mugun fata! Yo ita ta aike shi? Ita ta sa Alhaji Awaisu yawon ta zubar har da za a kafa mata kahon zuka? Tun kan a haifeta yake yawon bariki amma kawai kawai dan an rainata sai a aza mata jakar tsaba? Bai zai yiwu ba fa.
Don haka ta dau aniyar auren Alhaji Awaisu ko don ta nuna wa uwargidansa ita ba komai ba ce. Da sannu zata gane wa ta zaga da sannu zata koya mata hankali.
Da wannan tunanin ta kammala kwalliyarta. Wani jan leshi ta daura ta dau komai fari ta saka. Dama bata yafa mayafi don ba zata iya ba. Ta dau jakarta kenen wayarta tayi kara. Kallo daya ta yiwa wayar ta ja tsaki, safara ce kanwarta.
Ta san ba zai wuce roke roke ba abunda ta tsana. Ko korafe korafe wanda ita ba zata iya saurare ba kar ta makara. Ita fa tunda ta dauke yaranta ba sosai take lekawa ba, ina za ta iya? Ka je ayi ta maka dogon wa'azi kamar kai ka yiwa shedan ungozoma.
Sai ta ki dauka. Kara kiran da aka yi ne ta dauka a fusace tace
" Safara wai menene wannan irin kira haka kamar na dau kayan wani"
A zafafe ita ma safara din ta ce
" Mai da wukar, Hajiyarmu tun jiya take kawance emergency na asibitin Nassarawa. Idan kin yi raayi za ki iya zuwa" kit! Ta kashe wayar tana mamakin irin mugayen halayen da Hindatu ta koyo.
Sai taji gabanta ya fadi dam! Daga larurar idon nan Hajiyarsu bata cika ciwo ba. Sai taji jikinta yayi sanyi da ta tuna rabonta da ta leka gidan ma ta manta. Hidindimu sun mata yawa.
Sai ta dau motarta kawai ta wuce asibitin. Ko da ta isa sauran kannenta ne akan hajiyar suka gaisheta sama sama ta amsa a banzace. Daga nan sai ta fara borin kunya
" wani irin abu ne haka? Saboda tsabar rashin hankali hajiyar ta kwanta tun jiya a rasa wanda zai kira ni a waye ya fada mun sai yanzu? Sai ka ce wata bare"
Babu wanda ya tankata a cike suke da ita tam!Sai suka bar ta da halinta kawai dama su suka dage a kira ta, hajiyar cewa tayi a kale ta.
Ta kara da cewa
" Bani takardar magungunan da ba a siya ba na je na siyo"
Wannan maganar ce ta sa hajiyar ta dago kai a hankali ba don tana gani ba ta ce
YOU ARE READING
Mai Tafiya
AdventureLabarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeri...