So ai ruwan zuma ne, idan ka sha ka ba masoyi!
Niamey, Niger Republic
Rokaiyatou ta cigaba da kallon hanya yayin da take wasan kasa a kofar gidansu ta ga ta inda Momodou zai bullo ta ruga. Can ta ji an kwalla ma ta kira "Rokaiyatou"! daga kan da za ta yi sai ta hange shi ba ta yi wata wata ba ta fyalla gida a guje. Yarinya ce da ba za ta wuce shekara 8 ba jikinta ku san duk tsummokara. Ba ta yi wata wata ba ta fada bayan babarta ta kwakumeta ta ce
" Momma, frère Momodou shiddawo ya tardoni ina wasan kasa"
Uwar ta tunkude ta daga jikinta cikin hausarta ta zallar kananci ta ce
"Ke kaleni, ku je can ku karata"
Momodou ya shigo da riga "long sleeve" fara da shudin wando bayan sa goye da jaka irin ta yan makaranta, ya sa safa da kambos. Ya nufi bayan Momma ya janyota da kunne ya murda ya ce
"Mi na gani kina yi waje?"
Ta na ta jan kunnen kokarin yakicewa shi kuma ya kalli momma kamar me neman bayani ta dago daga tsintar shinkafar da take ta ce
" Rokaiyatou, K'...ai kadan ka gani..kamar mai aljanu..ai duka kawai zaka ma ta sai ta ji a jikinta"
Ya kura ma ta ido hawaye kwance male male a fuskarta, gashinta mai tsawo da yawa ya cukurkude ga kasa kamar an yi yaki. Kafafuwanta butu butu kamar tayi hakan rijiya. Sai kuma ya ji tausayinta ya kama shi da ga rigar jikinta yar yaloluwa da yawan wanki ya sa ta kode ta jeme. Abubuwa dayawa suka cigaba da yawo a kansa duk da karancin shekarunsa dan yanzu ma yake aji shida yana neman gama makaranta.
Ya janyota suka zauna akan tabarma yana kakkabe ma ta gashi ya ce
" kin yi abinci dai ko?"
Yana so ya ji ko ta ci abinci.
Ta girgiza kai ta ce" yanzu dai Momma za ta dahwa"
Ya juya ya kalli shinkafar da ake tsinta 'yar kut a faranti wacce ya san bai wuce a ci ta da mai ba. Ya bude jakarsa mai dauke da yar " cooler" na abinci ta yan makaranta , dankali ne ko tabawa bai yi ba ya sa a gabanta. Ta fara ci da budu budun hannayenta ba tare da yace ta je ta wanko ba, ya cigaba da kallonta. Momma ta dube su tayi murmushi ta ce
"Kai dai baka son cin abincinka, sai dai ka kawo wa kanwarka"
Murmushi yayi. Sai ya sa hannu ya zaro biskit da wani dan lemo ya ce
"Wannan kuma sai kinyi wanka, ba ki son wanka ko?"
Ba ta kula ba cin abinci kawai take. Ya kalli. Momma ya ce
" Ina ruwan da za tayi wanka?"
Ya kama haba tace" Au har wani ruwan wanka zan ke ajiye ma ta? To sau nawa zan ajiye"?
Murmushi kawai yayi ya nannade hannun rigarsa ya doshi inda rijiya take. Ya jefa guga ya fara jan ruwa har ya cika wani dan karamin bokiti. Sai ya yafito yarinyar da hannu ya ce
" je ki dauko sabillo"
Ta shiga daki ta dauko ya ce ta tsugunna ya fara wanke wannan kan na ta dikin dikin har sai da ya fita tas. Ya kalli Momma ya ce
" Dan Allah Momma ki kai ta bayi ki ma ta wanka"
Ta yi murmushi ta mike tana cewa
"Tou momodou na Rokaiyatou ai idan ban taso ba ba zaka kaleni ba"
Ta zo ta karbe shi. Ya dauki jakar makarantarsa tana kallo ya zaro kudi ya cusa a karkashin farantin shinkafar nan yayi tafiyarsa ba tare da ya waiwayo ba. Ta gyada kai a hankali a cikin ran ta tana tunanin irin kaunar da momodou ke yi mu su sai ta raya a ranta ko dan Rukaiyatou jininsa ce? Ta kawar da wannan tana mai la'akari da cewar duk 'yan gidan ma ai yanuwanta ne to amma wa ta ishi kallo? Momma ta cigaba da dirzar Rokaiyatou da sabulu ta na mai ayyanawa a ranta , ko ya rayuwa za ta yiwu ba Momodou?
Washegari da safe Rukaiyatou na tsaye a kofar kangon gidansu tana hangen wani tsararren bene mai bakin gate tana so ta ga fitowar frère. Gida ne tangameme wanda kallo daya za ka masa ka san an zubar da dukiya. Can aka bude tangamemen gate din motar da take kai yan makaranta ta fito. Tun daga nan ya fara kwalla ma sa kira tana daga ma sa hannu. Da ma ya san tana tsaye domin al'adarta ce yin hakan. Yana isowa zasu wuce shi ma ya daga ma ta hannu suna ta dariya.
YOU ARE READING
Mai Tafiya
AdventureLabarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeri...