Bayan mun koma gida da sati daya daddy ya zo. Ranar duk mun hadu a main falo muna kallo, ina kwance a cinyar mommy tana yi min tsifa, Hafsat kuma suna playing chess ita da Ya Habeeb wanda yanzu ya gama SSCE dinsa yana jiran result, da Faruk. Ya Walid ne kadai baya nan tunda su basu samu hutu ba. News aka fara daddy ya karo volume muma duk sai hankalin mu ya karkata akan TV din. Titi aka nuno chike da hold off ana ta hayaniya can gaba kuma wasu motoci ne guda biyu suka yi crossing suka rufe titin ruf babu hanyar wucewa.
A kusa da motocin kuma wasu samari ne sun takarkare suna ta jibgar junansu kamar Allah ne ya aiko su. Camera tayi zooming fuskokinsu ga mamakina sai naga daya daga cikin su dariya yake yi shi kamar game ne abin a gurinsa, dayan kuma sai huci yake yi da alama dariyar dayan ce take kara kular dashi kuma daga dukkan alama me dariyar yafi shi karfi. Daddy ne yayi gyaran murya yace "Habeeb wannan ba Sultan ba ne?" Ya Habeeb ya dan kalli TV yace "Hmm shine fa daddy, yana nan sai abinda ya kara gaba" Mommy tace "ai dan baka zama sosai ne, mu yanzu ai mun saba da labarai akan Sultan, kusan kullum zancen kenan. Ni na rasa wanne irin yaro ne wannan. Daga yau a kama shi da drunk driving, gobe fada akan titi ya kama yaran mutane yayi ta jibga, jibi kuma sai kaji ance yaje yayi terrorizing unguwa. Kuma wai an rasa mai daukan mataki akan sa, wannan wacce irin rayuwa ce"
Daddy yace "ba laifin sa bane, laifin maimartaba ne. Ni bansan yaushe ya chanza hali ba, mutum ne shi mai zafi sanda muna makaranta" da sauri muka hada baki with excitement ni da Hafsat muka tambaya "Daddy dama sarki abokin ka ne?" yayi dariya yace "ba abokina bane, kawai dai munyi makaranta tare, department din mu daya dashi a Oxford, first degree da second, amma ba abokina bane, tunda ni talaka ne a lokacin su kuma 'ya'yan masu kudi ne. Muna haduwa dai in za'ayi taron Nigerian students. Ni lokacin tsoro yake bani, wato kato ne gashi baki ga zafin zuciya" duk mu ka kwashe da dariya.
Ya Habeeb yace "ah bara mu je mu siyo alkyabba, ai ni daga yau na zama dan sarauta tunda babana sunyi makaranta daya da sarki"
nan ma dariyar muka sake yi, bayan anyi shiru daddy ya cigaba da cewa "bayan mun gama masters ne, munyi applying for PhD sai na daina ganin sa, na tambaya akace sun dan samu problem ne da babansa akan yarinyar da yake so, shine uban ya chire shi yace a daina karatun. Nasan yarinyar dan ina yawan ganin su tare, balarabiya ce, I can remember in na gansu har dariya nake yi, shi bakikkirin ita fara tas, kyakykyawa ce sosai"
Muka yi dariya ganin yadda Mommy ta turo baki kamar yarinya tana hararar Daddy.
Na juya na sake kallon screen din TV naga police sun zo scene din an raba fadan, wanda aka kira da Sultan ya kama police guda daya da kokawa sai da suka taru akan sa sannan suka saka masa ankwa, He was still grinning. Anan camera ta tsayar da hotonsa, reporter ta fara lissafo irin crimes dinsa amma da an kama shi za'a sake shi saboda dan sarki ne. Na kura masa ido ina kallonsa. Kyakykyawa ne first class, kana ganin sa kaga half cast, fatar sa golden brown mai kwalli da daukar ido. Idanun sa dara dara farare tas, hancinsa kamar an auna da fuskarsa, lips dinsa tamkar ya shafa jan baki. Bashi da tsaho sosai amma fa a murde yake dan sai da police uku suka hadu sannan suka iya rike shi.
Na dauke kaina ina aiyana yadda rayuwar sa take. What is his story? Kawai na samu kaina da tambayar Daddy "Daddy to an yi auran?" Yace "auran wa?" Ya amsa daga alama kowa a falon ya bar maganar sai ni, "Auran balarabiyar, naga wannan kamar halfcast ne" daddy yayi shiru yana kallon hoton sultan a TV sannan yace "gaskiya I can't say ko anyi auran ko ba'ayi ba" Mommy tace "anya kuwa anyi? Dan na taba shiga fadar amma matar sarkin da na gani bahaushiya ce, and she is far from being very beautiful" ta fada tana sake hararar Daddy "kuma na lura Sultan din dan ta ne dan lokacin tana ta fada wai an tafi dauko shi daga airport da wrong car, specifically ya fada yace ga motar da yake so a dauko shi amma aka ki. Gaskiya ina ganin kamar itace ta bata sultan" Daddy ya girgiza kai kawai yace "Allah ya kyauta".
VOCÊ ESTÁ LENDO
Maimoon
RomanceIt is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny that totally changed her and left her hanging on a thin thread of her real self. It is a story about...