Na sake daga ido na na kalle shi naga still yana tsaye a inda yake, sai dai ya saka hannayensa a aljihun wandonsa yana karewa gurin kallo, as if he owns the place.
Securities ne masu sanye da kaya masu tambarin Hilton suke ta kara shigowa cikin restaurant din, sai a sannan na lura cewa kusan rabin mutanen gurin shi suke kallo amma shi daga dukkan alamu bai ma san anayi ba. Ba zato ba tsammani kawai sai ganin idonsa nayi cikin nawa, nayi sauri na dauke kaina na wayance da daukan kofin tea na da ya kusa sandarewa na kurba.
A lokacin ne naji wani security a kusa da inda nake zaune yana yin waya "oga mutumin ka ne fa ya shigo yanzu, eh shi kadai ne yallabai, gamu nan duk mun shigo ciki muna observing dinsa in case ko zai yi halin nasa. Ok sir" na tabbatar akan mutumin da ya shigo yanzu ake waya, a raina nace "interesting, so you are a trouble maker".
Na sake kallon inda yake tsaye sai naga kamar wanda na kira shi, ya juyo direct ya taho wajan table dina. Nayi sauri na dauki cokali na fara juya tea dina duk da cewa babu abinda na kara a ciki, zuciya ta kamar ta fito waje, na shiga uku, kodai mutumin nan baya son kallo ne kuma yaga ina ta kallonsa shine zai zo ya kwada min mari? Na kasa daga ido na ballantana in tabbatar gurin nawa ya taho.
"Assalamu Alaikum" a firgice ba dago kaina, na kuwa ganshi a tsaye a gaba na. Duk yadda naso in hana kaina kallonsa amma na kasa dauke ido na daga fuskarsa. Fatarsa chocolate ce mai haske, misali ace ka hada coffee ka zuba masa ishashshiyar madara, tas take cike da alamar kulawa da jin dadi. Tunda nake ban taba ganin idanu masu kyau irin nasa ba, farare ne tas masu maiko, bakin ciki kuma ba baki bane ba, light brown ne, wannan ne ya kara tabbatar min da cewa ya hada jinsi da fararen fata. Girarsa mai yalwar gashi ce, lips dinsa jajawur tamkar ya shafa jan baki mai turuwa. Fuskarsa ba mai tsaho bace ba kuma bata cika fadi ba, tana zagaye da kwantaccen saje wanda ya sha gyara. Gashin kansa a hargitse, amma daga gani kasan ba gashin hausawa bane.
Finally na dauke ido na daga kansa na cigaba da aikin juya tea din da yake gabana, ina jin kamar zuciyata zata fado cikin kofin gabana, sai da nayi gyaran murya sannan can kasan makoshi na amsa masa sallamar sa "Amin wa alaikassalam"
Yace "mind if I join?"
Mind If I join? Wani ya taba gayamin exactly wadannan words din. Ibrahim, a library, maganar da muka fara yi daga ni sai shi ranar da naki zuwa class dinsa.
Na kirkiro murmushi, at least ba mari na yazo yayi ba, nace "bismillah, zauna babu wani abu" sai da ya zauna sannan na tuna cewa har yanzu fa juya tea nake yi. Na dauki kofin na cigaba da sha, da shi da ruwan fanfo basu da maraba sai sugar. Na dan saci kallonsa ta saman kofin hannuna kawai sai muka hada ido shima yana kallona, a tare muka yi sauri muka dauke kai.
Ya danyi gyaran murya yace "so.. Me zaki ci?" Na nuna masa kofin hannuna nace "tea nake sha" ya wani bata fuska kamar abin kyankyami yace "tea? Are you telling me kin baro gida kin taho nan dan ki sha tea? In fact restaurant din nan ma basu iya tea mai kyau ba, what is so special about it?"
A takaice nace masa "bana jin yunwa ne shi yasa" wani murmushi yayi min wanda sai da naji shi har kafafuwa na yace "in kika ga abinda zanci yanzu, dole ki ji yinwa" daga nan ya daga murya yayi magana da budaddiyar murya yadda nima kaina sai da na dan tsorata "Wai babu waiters ne a gurin nan?" Ya dawo da dubansa kaina yana murmushi mischievously, sannan murya can kasa yace min "enjoy the show".
Wait, I know that smile, sai yanzu na tuna a inda na san shi, a tv, suna fada shi da wani mutun akan titi police suka zo suka yi arresting dinsa. Dan sarkin Abuja, Sultan, yes, haka naji ya Walid ya ce sunansa, a real big time trouble maker, no wonder daga shigowarsa aka cika gurin da securities. Wait, hakan yana nufin ina zaune a table daya da criminal kenan?
Ta gefen idona naga securities guda biyu sun zo gefen mu sun tsaya, sannan sai ga wata waitress nan tazo da sauri ta kawo masa menu ta ajiye a gabansa, daga ganin ta kasan a tsorace take, nima ta ajiye min a gaba na, na daga mata hannu alamar bana bukata, bai dago kai ba yana duba menu din gabansa yace "don't worry, I will order for you. Please don't say no" bance komai ba har ya gama bada order dinsa ta tafi.
YOU ARE READING
Maimoon
RomanceIt is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny that totally changed her and left her hanging on a thin thread of her real self. It is a story about...