The Dinner

7.8K 670 4
                                    

Sultan's POV

Ya jima yana kallon motar har ta bace. Sannan ya juya ya shiga motar sa ya figa a guje ya dau hanyar palace. Yau dama sam bai yi niyyar fita daga gida ba wata unexpected yunwa ce ta tashe shi daga bacci kuma ta saka dole ya fito neman abinda zai ci, yunwa ce ta fito da shi ko kuma destiny ne, ya danyi murmushi tare da kallon wayarsa da take kan dash board.

Tun daga nesa ya danne horn din motar sa, dama ya saba kullum abinda yake yi kenan, kowa sai yasan sultan ya shigo, ko mutun yayi bacci sai ya tashi. Yana shiga direct part dinsa ya wuce yayi packing a inda yake ajiye motocinsa. Direct bedroom ya nufa, yana shiga ya kalli kansa a cikin mirror sai ya bata rai yana kallon squeezed rigar sa "damn it" ya fada tare da cize lips dinsa sannan ya fada kan gado da kayan sa complete har takalmi. Ya lumshe idonsa yana tuno every detail na fuskarta, it is like brain dinsa tayi automatically saving hotonta. "Hafsat" ya furta a hankali. Tunda yake bai taba yin serious budurwa ba, 'yammatan da yake haduwa dasu duk club girls ne da zasu yi rawa tare and that's all. Shi ba manemin mata bane sam, he consider it dirty.

Ya dauko wayarsa ya dubo number dinta da yayi saving yana murmushi a ransa yana yabawa kansa dabarar da yayi na karbar number dinta maimakon shi ya bata tashi, dan yasan ba lallai ne ta kira shi ba. Ko ta karasa gida yanzu? No, unguwar da ta yi masa kwatance tana da dan nisa, bara ya bari a dan kara jima wa tukun. Ya ajiye wayar tare da gyara kwanciya. Har after 12 yana kwance a haka kuma baiyi bacci ba, ya sake dauko wayar yayi dialing "The number you are trying to call is currently switched off, please try again later" "damn you MTN" ya fada tare da jan tsaki.

A cikin daren ya kira number takai sau goma amma still switch off ake gaya masa, maybe charge dinta ne ya kare, ya fada a ransa, amma baiji dadin haka ba saboda yana son ko yayane ya sake jin muryarta kafin yayi bacci.

Washegari tunda yayi sallar asuba yake zaune yana kallon agogo, jira kawai yake yi yaga gari yayi haske ya kira ta. 8:00 ya sake dialing number ta amma still switched off. Damn it, kar dai ace wrong number ta bashi, in haka ne kuwa to tabbas address din ma wrong ta bashi. Ya mike da sauri zuciyar sa tana bugawa ya shiga wanka, nan da nan yayi ya fito. Duk gayun sa yau da sauri ya shirya cikin usual body hug kayansa.

Agogon hannunsa ya duba yaga karfe goma, yasan tunda Takawa yana gari to duk mutan gidan suna falonsa yanzu. Shima direct can ya wuce, duk masu gaishe shi a hanya babu wanda ya kula, yana shiga yaga Takawa a zaune a kan shimfidar da ake masa ta cin abinci a tsakiyar palour,  Hajiya tana kusa dashi daga hannun dama Abbas kuma daga hannun hagu, daga gefe kuma Saratu ce da Fa'iza. Daga dukkan alamu hira suke suna dariya har Takawan, shigowar Sultan ce tasa Takawa ya hade girar sama data kasa tamkar bai taba dariya ba, Sultan ya karasa gabansa ya durkusa "barka da assuba" bai samu amsa ba kuma dama bai sa ran zai samu ba.

Ya mike ya koma kusa da Hajiya ya zauna tare da gaishe ta itama, ta amsa sannan ta saka hannu ta dan shafa gashin kansa a hankali "yaron kirki yau kuma da wuri aka tashi haka? Ko wani gurin za'a je ne?" ya girgiza kai yace "no Hajiya, part din Amir kawai zan shiga nace bara in shigo in gaisheku"

Abbas yace "yaya Sultan barka da assuba" Sultan ya kirkiro murmushi yace "Abbas, ya kake?" Su Saratu ma duk suka gaishe shi daga nan sai kowa yayi shiru.

Sultan ya danyi jim a zaune sai kuma ya mike yace "Hajiya bara inje" tace "to yaron kirki, a dawo lafiya" ya karasa gaban Takawa ya sake durkusawa "a huta lafiya" nan ma babu amsa.

Sai da ya fita ya turo kofa sannan yaji muryar Takawa sun cigaba da maganar da suke yi da Abbas. Ya runtse idonsa zuciyarsa tana masa zafi sannan kuma ya saka hannayensa a aljihunsa yayi gaba.

Kamar yadda yayi tsammani, rashe rashe ya tarar da Amir yana ta shirgar bacci, Allah ne kadai yasan jiya karfe nawa ya kwanta bacci dan tunda yace Solomon ya zo gari to yasan sai sun raba dare a club.

MaimoonWhere stories live. Discover now