This is Me

8.7K 688 7
                                    

"are they really sisters? " ya fada yana kallon sauran 'yan ajin. Duk ajin ya dauka "eh sir sisters ne, baka ga suna kama ba?" ya sake kallon mu yana girgiza kai, "ni ban ga kama ba" Hafsat ta kara kulewa ta hade rai sosai, shi kuma sai ya kalleta yayi dariya yace "ok Big Sister, kiyi hakuri na takura ma kanwarki. In babu damuwa to in dawo desk dinki mana maimakon nata?" Ya fada da alamar tsokana a muryarsa, Hafsat ta bude baki tana kallonsa da mamaki, sannan tayi cikin kufula tace "a'a yi zamanka anan" yayi dariya sosai har habarsa ta lotsa sannan yace "dama nasan zaki ce haka, nima kuma nafi son zama anan" ni dai duk ina jinsu bance komai ba. Sai da period dinsa ta fita sannan yace min "kar ki manta alkawarin mu, ni kadai nasan abinda zanyi miki in kika yi min irin ta rannan" da haka ya fita daga ajin.

Yana fita Hafsat ta jawo kujerar ta kusa da tawa tace "alkawarin me mutumin nan yake magana akai? Yaushe kuka hadu har kika yi masa alkawari ba tare da na sani ba? " na kalleta nace "wani lokacin Hafsat ina mamakin mutane in suka ce na fiki surutu, sa idonki yayi yawa" nan Hafsat ta kuma kuluwa tace "au haka ma zaki ce ko? Duk abinda nakeyi fa dan ke nakeyi. Mutumin nan daga ganin sa ba mutumin kirki bane, bana son kowacce irin alaka a tsakanin ku. I am trying to protect you" nace " ni kuwa ina mamaki duk sanda kika ce Ibrahim ba mutumin kirki bane ba, how do you know? Kin san kullum daddy yana ce mana never judge a book by it's cover, ba dai dai bane ba kawai ki yanke hukunci akan mutum ba tare da kin fahimce shi ba" tace "OK kina so ki gayamin cewa ke kina so ki fahimce shi kenan ko? " nace mata "exactly " Amira ta taso tazo gurin mu tace "pls guys not here, zamuyi maganar in munje hostel" Hafsat ta cigaba da balbalin fada ni kuma na tashi kawai na fita daga class din. Kan veranda na zauna ina tunanin yadda zan bullowa wannan lamarin, nasan Hafsat akan gaskiyar ta take fada, duk da ina da karancin shekaru amma na gane duk abubuwan da Ibrahim yake min da duk kwana kwanar sa nasan inda ya dosa. Kuma ni kaina ba sai wani yayi min fada ba nasan nayi kankanta da zuwa inda ya dosa. Abu na biyu kuma Ibrahim bayarabe ne, ni kuma bafulatana bana jin tarayyar mu dashi zata yi kyau. Murmushi nayi sanda na lissafo fuskar Mommy inta samu labarin ina dating yoruba guy. Amma koma menene zai kasance yau zamu zauna muyi magana da Ibrahim, zan bukaci ya fada min duk abinda yake zuciyar sa ni kuma zanyi masa bayanin cewa abin ba me yiyuwa bane. Ina so mu samu maslaha a tsakanin mu.

Da aka tashi bayan munyi sallah munci abinci Amira ta ja mu dakin su tana so ta daidaita tsakanin mu da Hafsat. Na zauna a nutse na yiwa Amira bayanin abinda yasa nake son muyi magana da Ibrahim. Muna ta maganar mu Hafsat tayi banza ta rabu damu, saida Amira tace mata "baki ce komai ba Big Sister" ta fadi big sister din da tsokana, irin yadda Ibrahim ya ce mata dazu a class. Ta juyo ta kallemu tana yamutsa fuska tace "She can do as she wants, ni dai tasan cewa komai tayi kamar tayi a gaban Mommy ne dan wallahi sai na gaya mata. Kuma ta san ba zata yi mata da dadi ba" Amira tace "Haba Hafsat pls let her go, inta dawo zata gaya mana duk abinda sukayi dashi daga nan za muyi shawarar me zata yi next" Da kyar Amira ta lallaba Hafsat ta barni na tafi da sharadin cewa duk abinda yace min zanzo in gaya mata.

Naje nayi wanka na shirya a tsanake, dama ni ko a gida ba kwalliya nake ba ballantana a school na saka hostel wears dina, har na nada vail dina sai kuma na chire na dauko dogon hijab din Hafsat na saka. Ina fita na nufi library, tun daga nesa na hangoshi a zaune a side din library din da table a gabansa dauke da littattafai, amma kuma ba karatun yakeyi ba waya yake dannawa. Na karasa da sallama, ya dago kai ya kalleni da murmushi a fuskarsa, daga gani ya dade a zaune a gurin. Ya nuna min kujerara kusa dashi yayi min nuni da in zauna. Maimakon in zauna a kusa dashi din kamar yadda ya bukata sai na dauki kujerar na zagaya daya side din na zauna ina fuskantar sa. Ban gaishe shi ba nace masa "am here, what do you want ?" Ya sake yin murmushi yace min "good evening ma'am" sai kuma naji kunyar ban gaishe shi ba nace "good evening sir" ya cire glasses din idonsa yana murza idon yace "har na fara tunanin baza ki zo ba, na dauka yau ma Hafsat ta hana ki zuwa" na kalleshi da mamaki nace "ya akayi kasan ita ta hanani zuwa rannan? " yace "da ban sani ba, sai dazu data ce min ita sister dinki ce sannan na fahimci ita ta hana ki zuwa" muka yi shiru baki daya na wani lokaci sannan ya cigaba da magana a hankali "am sorry for shiga rayuwar ki da nayi kwana biyu. Nima bansan menene yake hawa kaina ba tun zuwa na makarantar nan, ina so ki fahimci cewa bani da wani mugun nufi a kanki sai alkhairi insha Allah. Tun ranar da kika amsa question dina a class naji kin burge ni sosai da sosai, bayan na fita daga ajin ku na je staff room nayi tambaya akan ki anan na fahimci cewa you are a genius" nayi saurin katse shi nace "am not genius" yayi dariya yace "research ya nuna cewa babu genius din da ya taba yarda cewa shi genius ne" ban bashi amsa ba na sunkuyar da kaina kasa. Ya cigaba da cewa "tun daga nan na zama interested akan ki, lokacin ne nayi miki offering friendship. Kuma ina saka ran babu wani abu da zai rusa friendship din mu" ya sake yin shiru kamar ya gama magana sai kuma yace "ita zuciya tana da wahalar fassarawa, na kasa fahimtar me zuciya ta take nufi dake. Kullum sai inji ina so in ganki, inna ganki kuma sai inji bana so mu rabu, in ban ganki ba kuma sai inji na rasa farin ciki na" ya sake yin shiru yana shafa gashin kansa. "What do you want from me?" na sake tambayar sa a karo na biyu, kaina a kasa, yan yatsuna sarkafe da juna. Ya yi tagumi da hannayensa duk biyun ya sauke lumsassun idanuwan sa a kaina sannan cikin muryar rada yace " ina so ki kara hakuri dani mu cigaba da friendship din mu, nasan wannan feeling din da nake ji a kan ki zai wuce wata rana. Ina so please kiyi tolerating dina for the time being. In kina ignoring dina zan iya aikata wani abun da ba dai dai ba". Na dago kaina na kalle shi da alamar tambaya nace "wani abu da ba dai dai ba kamar me kenan?" Ya dan kalli gefe yana tunani sannan yace "I don't know. I just don't seem to control myself when it involves you. Maybe watarana in kin ƙi fitowa in ganki in samu kaina da bin ki zuwa hostel din ku" ya karasa da murmushi a fuskarsa. Na danyi karamar dariya ina hango yadda za'a biyo shi da gudu ana yi masa ihun gardi. Sai kuma na girgiza kaina nace "you can't. You won't" Ya dafa hannayensa a kan table din tsakanin mu ya sunkuyo ya saka idonsa cikin nawa yace "I might. Kamar yadda na gaya miki I have totally lost control of myself over you. I don't seem to differentiate what is right and what is wrong anymore. And I need your help tun kafin in fada rijiyar da ba zan iya fitowa daga cikin ta ba. Please, just, tolerate me"

MaimoonDonde viven las historias. Descúbrelo ahora