Ibrahim ya kawo mana kaya babu laifi, kayan tea, biscuits da drinks. It must have cost him dukkan albashinsa.
Sati daya bayan nan ya zo yayi interview din, bayan wata daya kuma aka aika masa da offer dinsa har ibadan. A week after that, ya tattaro ta dawo abuja.
An bashi gida a staff quarters. Nan take ya fara siyayyar kayan gida, komai ya siya sai ya gayamin ni kuma sai in gaya masa menene next abinda ya kamata ya saya. I wanted to help him with money amma nasan ba zai karba ba, kuma bama nason yasan financial status din family na.
Farko sai aka bashi ss2, class din da ya dauka during service shi kuma ya dage lallai baya so shi ss3 yake so, a cewar sa ya saba damu tunda mu ya dauka sanda yana service. Sai da kyar suka bashi SS3 din, ranar bakinsa har kunne yana murna yazo yake gaya mana, sannan kuma an bashi sports master. Yanzu kam da yawa daga 'yan ajin mu sun san alaka ta da Ibrahim tunda sam yanzu baya boye abinda yake ranshi, ni ce dai nake dan ja da baya. A haka har muka yi hutun first term. A cikin hutun abubuwa da yawa sun faru, na farko Allah yayi wa baban Amira rasuwa.
Asalin su Amira 'yan kano ne, baban ta babban mutum ne sosai, yana da manyan 'ya'ya a kano sai aiki ya mayar dashi Abuja, ita kuma uwargidansa tace sam ba zata koma Abuja da zama ba tunda ta tara iyali a kano. Nan 'yan'uwansa suka hada musu auren zumunci da maman Amira ya taho da ita Abuja. Amira ce kadai 'ya a tsakanin su tunda shekarunsa sunja sosai. Sam 'yan uwan Amira babu wanda ya damu da ita balle mahaifiyarta, dan haka sai mutuwar tayi musu zafi sosai.
Maman Amira bata san komai na dukiyar Baba ba sai gidan da suke ciki a abuja, duk harkokin dukiyar sa da manyan 'ya'yansa yake yi. Matarsa ta kano ta dage lallai sai a sayar da gidan sa na Abuja a hada kudin da sauran dukiyar sa ta kano sannan a raba gadon. Ita kuma maman Amira bata son sayar da gidan saboda bata son tashi daga abuja tunda nan ta saba dashi, daga ita har Amira.
Alakar kawancen da take tsakanin mu da Amira da kuma wadda take tsakanin Mommy da Maman Amira ce ta saka Mommy tayi tsayin daka akan maganar tunda ita lawyer ce har sai da taga an bar musu gidan a matsayin gadonsu, bayan gidan kuwa babu abinda suka tsira dashi, hatta motar da maman Amira take hawa sai da aka karbe. Maman Amira sec sch kadai tayi, dan haka babu zancen neman aiki, ga Amira ita ko secondary school din bata gama ba. Mommy ce ta biya wa Amira school fees na second and third term sannan ta biya mata kudin SSCE din da zamu yi nan bada jimawa ba.
Muna komawa pc tayi taron Muslim students ta sanar mana cewa akwai musabaqa da federal government take shiryawa, ance a bada daliba guda daya da zatayi representing din school din mu, dan haka mu zaba a tsakanin mu wa muke ganin zata iya. Nan take muka zabi Amira, kuma tace ta yarda zatayi, muna ta murna sai pc tace zata hada ta da malami guda daya wanda za su ke yin tilawa tare kafin likacin musabakar. Muka tashi daga taron muna ta yiwa Amira murna.
Da daddare after islamiyya sai Ibrahim yace da Amira ta tsaya yana son ganinta, inajin haka nasan shi akace yayi coaching dinta. Nan muka tsaya tare. Sai da aka gama tafiya sannan yazo yace mata "congratulations Amira, naji abin alkhairi, Allah ya bada sa'a" muka ce amin. Nan suka fara tsara yadda zasuke karatun ni kuma ina jinsu ina dan bada tawa shawarar. A karshe suka yanke shawarar zasu keyi daga magrib zuwa isha. Haka kuwa akayi, kullum in munyi sallar magrib sai Amira ta zauna a masallaci tare da Ibrahim har sai munzo sallah isha tukunna mu tafi islamiyya tare.
A bangare na kuma lokaci daya girma razo min, ni kaina bansan yaushe ba sai gani nayi kayana duk sunyi min kadan. Kirjina kullum kara chika yake haka hips dina, har saida nakai ga komawa aron kayan Hafsat ina sakawa ita kuma tace sam ba zata yiwu ba sai dai in aika gida akawo min wasu kayan. Ina aika wa kuwa sai ga kaya akwati guda duk size din Hafsat kuma dana saka sai naga duk sunyi min dai dai.
Wata ranar sport muka saka sport wears kamar yadda muka saba muka fita. Ni dama basketball nake yi tun jss1 haka Ibrahim ma, duk ranar sport tare muke yi dashi kuma ya iya sosai saboda yana da tsaho. Ina zuwa na tarar dashi already a field da wadansu staff su biyu tare da students wadanda mostly 'yan kallo ne. Ban yi wata wata ba na shiga muka fara bugawa, amma sai na lura Ibrahim hankalinsa sam baya kan ball din, duk ya zama distracted, ya kasa scoring ko kwallo daya, gashi ana neman cinye team din mu, nan na tafi gurinsa da niyyar in tambayeshi mai yake damunsa sai na lura gaba daya ransa a bace yake. Ina zuwa kusa dashi sai kawai naga ya chire jacket din daya daura a kugunsa ya kama kokawar saka min, na kwace daga hannunsa cikin fada nace "what is wrong with you?" ya dora min jacket din akan kirjina yace "just go and play table tennis or snooker, ai ba sai lallai kinyi basketball din ba" raina naji ya fara baci, nace "saboda me? Kullum ba basketball din nake playing ba? Dan me yau zaka ce wai inje inyi snooker bayan kai ne ma kake bata mana game din" wani kallo da yayi wa kirjina yasa naji kafafuwana duk sun sage, kallon kawai yayi min na gane ma'anar me yake nufi, wata kunya ce naji kamar zan narke a gurin. Bai ce min komai ba ya jefar da ball din hannunsa ya juya ya bar field din.
Daga baya na naji wasu sababbin coppers suna cewa "wannan Ibrahim din dan bakin ciki ne wallahi" wani hawayen takaici naji yana taho min, nayi sauri na mayar dashi. Da sauri sauri na zura jacket din Ibrahim na bar gurin. Ina jin wata tana kwalla min kira na rabu da ita. Can kasan wata bishiya na hango Hafsat ita kadai tana zaune akan kujera ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya da novel a hannunta tana karantawa. Itama sport wears din ne a jikin ta amma tayi rolling farin vail har saman kirjinta. Na tsaya a gabanta nace "why didn't you tell me?" Ta kalleni da rashin fahimta tace "tell you what?" Na zauna kusa da ita nace "ba za kiyi min fada kice kayan jikina suna bayyana jikina ba, kika barni na fito mutane suna kallona?" Dariya tayi ni kuma na kara kuluwa, sannan tace "kusan shekaru biyu da suka wuce na taba fada miki magana akan Ibrahim sai kika ce min you are old enough to make decisions for yourself, to dan me yanzu kuma zan yi miki magana, tunda you are not blind. Yanzu ai kin dauki darasi ko?" Na kara bata rai bance mata komai ba. Kamar daga sama naji yana cewa "barka da hutawa big sister" duk muka kalleshi Hafsat tana dariya tace "ni fa bana son big sister dinnan, sai inji duk tsufa ya kamani" suka yi dariyar su su kadai. Ya zauna kusa dani naja kujera ta na matsa yace min "am sorry, bai kamata inyi miki magana a cikin mutane ba, amma bazan iya hakura mutane suna kallonki ba" Hafsat tayi gyaran murya tace "Hello, ina nan fa" ya kalleta yace "in ba zaki tashi ba to ki toshe kunnuwanki" ni dai bance musu komai ba dan duk haushi suke bani duk su biyun.
Tun daga ranar na koma saka dogon hijab irin na Hafsat, 'yan sport team din mu kuwa tun suna nemana har suka hakura.
Muna gab da fara SSCE Amira tace min sun daina karatu da Ibrahim. Na tambayeta dalili tace babu komai kawai tana ganin ta iya duk abinda ya kamata ta iya. Washe gari muna class aka kira ta a staff room, shiru shiru bata dawo ba sai na tashi na bi bayanta. A hanya muka hadu da ita. Abinda na gani a fuskarta ya bani tsoro, na tambayeta "Amira lafiya, ko a gida ne wani abu ya faru?" Wani kallo ta yi min wanda naji tamkar ta doka min guduma aka, cikin sarkewar murya tace "me kika biyo ni kiyi min kuma, nace na fasa karatun dashi ba shikenan ba? To yanzu na fasa musabaqar ma gaba daya, kije kiyi na bar miki, besides you are the golden one ai, you are so perfect that you must have everything that you want. You can have him, you can have the musabaqa and everything else"
Ta bangaje ni da kafadar ta ta wuce. Ni sam ban gane ina maganganun Amira suka dosa ba dan ni a iya sanina banyi mata komai ba. Kuma ban taba ganin ta a irin wannan yanayin ba. Tana tafiya sai naga Ibrahim ya fito daga office din PC muka hada ido ya girgiza min kai alamar kar inyi magana ya tafi.
Tunda muka shiga class Amira ta kifa kanta a desk take kuka, kowa ya tambayeta sai tace babu komai. Hafsat tace a rabu da ita, dama tun mutuwar babanta she has not being herself maybe mutuwar ta tuna. Ana tashi Ibrahim yazo ya kira ni ya tambayeni ko zan iya yin musabaqar? Da mamaki nace masa "Amira fa" yace "tace ta fasa" na tambaye shi dalili yace bai sani ba. Muna zuwa hostel nayi wa Hafsat bayanin duk abinda ya faru. Tayi shiru sannan tace "Are you sure babu wani abun a tsakanin su?" Naji maganar ta kamar kibiya a zuciyata amma sai na maze nace "wani abu kamar me fa?" Ta kalleni da nutsuwa tace "Amira ba haka take ba, in har ta gaya miki wadannan maganganu to da akwai dalili, kuma they have been spending a lot of time together lately, maybe something happened".
Maganar Hafsat ta shige ni kuma nayi niyyar zan samu Ibrahim inji daga bakinsa. Dama yanzu mun daina lectures sai dai revisions ko kuma muyi tutorial. Dan haka muna zuwa class na tafi staff room na cewa Ibrahim ina son ganin sa. Mu ka fito tare muna tafiya, direct na tambayeshi nace "Me ya hada ka da Amira?" Ya tsaya yana kallona yace "bangane ba, wani abun tace nace mata" nan na fada masa duk maganganun da Amira ta gaya min, yayi shiru bai ce komai ba. Direct na sake tambayar sa "is Amira in love with you?" Yace da sauri "what? Me yasa zaki fadi haka" na sake cewa "are you in love with Amira?" Da karfi yace "hell no!!"
Nayi shiru saboda naga yana son yayi min ihu a cikin mutane. Sai da muka jima a tsaye muna kallon kallo sannan ya fara magana "OK, na jima da sanin cewa amira tana so na, tana dannewa saboda she is your friend, ni ma kuma ban taba nuna mata na sani ba, but I know the signs. Yanzu da muka fara karatu da ita sai ya fara zama worst har bata concentrating akan karatun sai dai tayi ta tambaya ta things about me and other stuffs, to sai nayi suggesting cewa mu gayyato ki kizo muke yin karatun tare, shine taji haushi tace ta fasa karatun, na gaya wa pc kuma shine tace ta fasa musabaqar gabadaya, sai dai ke kiyi tunda nace dake nake so muyi karatu" tun daya fara maganar nake sauraron shi ina jin wani daci yana taso min a baki na, ji nayi kamar in rufe shi da duka, amma dana kalleshi sai naga iyakacin gaskiyarsa yake fada min. Na juya da sauri zan bar gurin ya kamo hannuna, wani mugun kallo na jefa masa nan da nan ya sake ni nayi gaba. Ina jinsa yace "Maimunatu 🙏please "
Vote vote vote
YOU ARE READING
Maimoon
RomanceIt is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny that totally changed her and left her hanging on a thin thread of her real self. It is a story about...