Na jima a tsaye ina kallon kofar da ya rufe bayan ya fita, me wannan mutumin yake nufi ne? Ni wannan ko a kafa aka daura min shi ai na gwammace in dau wuka in datse kafar in huta. Na zauna akan kujera na dafe kaina da hannayena. Dear Ibrahim, is this our destiny? Sai kuma naji haushin kaina, why am I even thinking of Ibrahim now. Me yasa har yanzu na kasa cire shi daga raina? Shekara biyu kenan rabona dashi, shekara daya kuma da yin aurensa, maybe har sun haihu by now. Jiki ba karfi na tashi na shiga daki na kwanta kusa da Hafsat.
Tun muna yara dama ni bana son Munnir sam bai yi mun ba, ballantana yanzu da ya kara habaka, I must be strong, I must pray hard, in nemi zabin Allah kuma nasan Allah ba zai zabar min Munnir a matsayin miji na ba. Ina nan kwance inna ta shigo take cewa "waye ya ajiye kudi a palour?" Nace mata "Munnir ne" ta ajiye akan dressing mirror sannan ta fara yi mana fadan mun kwanta da la'asar bayan munsan babu kyau.
A ranar da daddare har nayi bacci na fara jin hayaniya sama-sama, na farka sai naji a compound ake yi, na tashi da sauri na fita palour sai naga Hafsat a tsaye a bakin window tana leƙawa, na karasa kusa da ita ina tambayar ta "lafiya" ta yi min alama da inyi shiru. Nan muka cigaba da leƙen tare.
Hajja ce take balbalin fada "ai ba haka mukayi dashi ba, ce min yayi ba zasu tafi ba sai an daura aure, kuma yanzu kawai sai ace min wai gobe zasu wuce?" Baffa yace "kai Muhammadu mai yasa kayi mata alkawarin da kasan ba zaka iya cikawa ba?" Daddy yace "Baffa ni abinda nace shine, in har an samu fahimtar juna a tsakanin yaran to baza mu bar garin nan ba sai an daura aure, kuma ai daga zuwan Manniru yau ba za ace har sun fahimci juna shi da Maimunatu ba, abinda nake gani shine kar ayi gaggawar auren nan ya zama an bata zumunci maimakon a gyara shi, a bari idan yaran sun daidaita tsakanin su shikenan"
Hajja ta katse shi da cewa "yo yaushe zasu daidaita tsakanin su bayan zaka dauke yarinyar ku tafi? Ai in ma so ake su daidaita sai a bar yarinyar anan yadda za suke ganin juna" Kawu Aliyu yace "Hajja rayinyar nan fa karatu take yi, ya za'ayi a raba ta da karatun ta? Daga Manniru har Maimunatu 'ya'yan mu ne, ba za mu so mu tauye wa wani hakkinsa ba, tunda yarinyar nan tace bata son shi a rabu da ita, Hajja zamani fa ya chanja, yanzu da da ba daya bane, idan da anyiwa yara aure ba tare da son ransu ba suna hakura yaran yanzu zasu zo su bata mana zumuncin mune. Maimuna yarinya ce mai hankali wallahi, Manniru ba shi da kunya sam, kuma ya girme mata nesa ba kusa ba, ni dai Baffa ina ganin in akayi wannan hadin an tauyewa yarinyar nan hakkinta kuma zata iya ta kullace mu har abada"
A raina nace "God bless uncle Aliyu, Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira" na jingina kaina wanda already ya dau zafi a jikin Hafsat ina cigaba da sauraron mahawarar da zata iya chanza rayuwata gabadaya. Baffa naji ya fara magana "kai Manniru kana son auren Maimunatu kace ko?" Nayi sauri na leqa window, Munnir na gani a zaune a gefen Hajja, murya kasa kasa yace "eh baffa" Baffa yace "to shikenan, na baka damar ka cigaba da neman auren ta daga yau har zuwa ranar da zata gama karatun ta, idan kafin nan ta amince tana sonka shikenan" da sauri Munnir yace "Baffa shekara uku kenan fa nan gaba, ni ina zan iya zaman jira har na tsahon shekaru?" tas, naji saukar mari daga hannun uncle Aliyu zuwa fuskar Munnir, inajin Hafsat tana dariya kasa2, nan uncle Aliyu ya rufe shi da fada "Baffan kake musawa magana? Rashin kunyar taka takai har haka?" Baffa yace "rabu dashi Ali, idan ba zai jira ba ya nemo wata a aura masa, ni na gama magana" daga nan ya mike yayi hanyar part dinsa.
Nan gurin ya hargitse kowa yana fadin albarkacin bakinsa, kuma daga dukkan alama fiye da rabin mutanen gurin basa bayan wannan hadin saboda duk suna yabon halayena tare da kushe da Allah wadaran halayen Munnir, Inna sam bata cewa komai, Hajja kuwa sai kumfar baki take har da cewa duk sanda mukayi kwantai kar a kawo mata. Munnir kuwa tun daga inda nake nake hango yadda ya murtuke fuska yana bin kawunnan mu da mugun kallo.
Washe gari tun assuba muka fara wanka muna fitar da akwatinan mu, Inna ta zo ta saka mu a gaba da nasiha "ku kyautata addinin ku, ku bi iyayenku, ku tsarkake zuciyar ku daga mugun nufi akan kowa, in kuka yi haka Allah ba zai munana rayuwar ku ba, kullum in za kuyi addu'a ku nemi zabin Allah, kar kuce 'Allah ka bani kaza ko Allah ka yi min kaza' gwara kuce 'Allah ka zaba min mafi alkhairi a duk al'amurana'. Ku yawaita karatun alqur'ani dan shi kariya ne, musamman ayatulkursiyu, ku mayar da ita tamkar babbar kawarku kullum ta kasance a bakin ku, in zaku kwanta bacci kuyi alwala, na tabbatar muku in kuka rike wannan duk wani mugun nufi na mutun, aljani ko shaidani ba zai same ku ba".
Kiri2 sanda mukaje yiwa Hajja sallama taki kulamu, haka muka taso muka fito, Hafsat tace a hankali "kinyi wa kanki" muna fita waje naga Nuraddeen tare dasu ya Walid, muka gaishe su muka wuce. Na shiga gaba Hafsat ta zauna a baya tunda tare zasu zauna da Mommy, ba tare da Amina zamu tafi ba sai ta karasa hutun ta anan zata same mu a Abuja, ya Walid ne zai tuka mu. Ina zama sai ga Nuraddeen yazo yana tsokana ta "amaryar yayan mu" sai na samu kaina da daure fuskata, yayi dariya yace "congratulations though, naji yadda aka kare maganar jiya" nayi masa murmushi nace na gode, ya juya yace "gashi nan yazo sallama bara in san inda dare yayi min" sai da ya matsa sannan na hango Munnir yana tahowa inda motar mu take, sai a lokacin nayi nadamar fito war mu da wuri, da mun sani mun jira Mommy dan nasan duk rashin kunyarsa ba zai yi a gaban Mommy ba dan zata iya kwakkwada masa mari. Na yi sauri na dauko wani katon bakin glass na saka wanda ya kusa rufe rabin fuskata, yana karaso wa na daga glass din motar, ga mamakina sai naga ya zagayo ta side din driver, ya shigo ya rufe kofar, daga dukkan alama bai san da Hafsat a motar ba, na dauke kaina tamkar ban san ya shigo ba, murya can kasa yace "ba gaisuwa" nayi banza na rabu dashi, ya sake cewa "shine kika ce da kawu ambassador ba kya so na ko?"
A zahirin gaskiya ni Daddy bai tambayeni ba, asali ma bamu taba maganar dashi ba, nasan ya fadi haka ne saboda shima baya son wannan hadin. Ji yayi bani da niyyar cewa komai ya sake cewa "ina so ki sani, yanzu na fara sonki, kuma zan cigaba da bin wannan tsohon har sai ya amince da maganar nan dan ni yadda nake jinki bazan iya jiran 3 years ba" still no reply from me, na juya kaina ma ina kallon daya side din, kawai sai jin hannunsa nayi a fuskata yana kokarin juyo dani in kalle shi, Hafsat tana daga baya tace "hey, don't" a tsorace ya juya ya kalleta, duk da ban juya ba na tabbatar harararsa take yi, yace "hey, yaushe kika shigo?" Tace "tun kafin ka shigo, naji komai" yace "sa'ido fa babu kyau, musamman a harkar miji da mata" Hafsat tace "not even in your dreams".
Suna cikin haka Mommy ta fito, da sauri ya juyo gurina yayi min blowing kiss tare da cewa "sai munyi waya" ya fice, a tare mukayi tsaki ni da Hafsat. Yana fita gurin Mommy ya tafi ya durkusa yana gaisheta, Hafsat tace "chusa kai ba kwarjini" Mommy ta amsa masa fuskarta a sake sannan ta karaso mota. Su Daddy ma duk suka shiga motar su shida ya Habeeb da faruk, sai motar security a gaba, muka tafi.
Tun daga ranar har muka koma England kullum sai Munnir ya kira ni a waya, na rasa a gurin wanda ya samu numberta, a haka har hutun mu ya kare muka koma school.
Shakara daya tazo ta wuce muna ta karatu, har shekarar ta wuce babu Ibrahim babu labarinsa, Munnir kuwa har yau yaki hakura duk da maimaita masa da nake yi kullum cewa bana son sa. Amira ma muna da contact da ita tana ci gaba da karatun ta a abuja. An tura mu clinicals, Daddy ya saka aka tura mu asibiti daya da Hafsat wanda kuma yake kusa da gida, amma ita tana bangaren gynecology ni ina neurology, Amina ma an samar mata admission ita da Faruk sun fara karatu, yaya Walid ya gama, ya Habeeb kuma yana project dinsa.
Na koyi abubuwa da dama a asibitin nan, anan na kara sanin irin baiwar da Allah yayi wa bil adama, naga yadda ake bare kan mutun ayi masa aiki a kwakwalwa sannan a mayar a rufe, na koyi yadda ake yin hemisphecrotomy inda ake chire rabin kwakwalwar mutun a bar masa rabi kuma ya tashi lafiya lau. Na koyi abubuwa da yawa wadanda nake sa ran zan dawo Nigeria in yi.
A asibiti na hadu da Mahdi. Nasha ganinsa tun a school amma bamu taba magana ba saboda ba. Rannan mun fito daga wata theatre ina zaune ina hutawa kawai sai naji anyi min sallama, na daga kaina sai na ganshi, na amsa masa cikin mamakin accent din hausa da naji a bakin sa. Fari ne tas, irin farin da har jaja yake yi kamar in ka taba jini zai fito, kirar jikinsa dai dai misali, komai nasa kamar shi yayi wa kansa, sam bai yi kama da hausawa ba. Ban gama mamaki ba sai ji nayi yace "sunana Mahdi Datti Sufyan, ni dan garin kano ne, unguwar gwauron dutse. Naga kamar kema 'yar Nigeria ce ko?" Sai a lokacin hankali na ya dawo kaina, sannan na fahimci cewa na bude baki ina kallon sa, nayi sauri na rufe bakina nace "wait Datti Sufyan? The name sounds familiar" yayi dariyar data bayyana kyawawan jerarrun hakoransa yace "yah... My father is kind of famous in kano" ya zauna a kusa dani yace "baki gaya min sunan kiba amma" na sake tattaro hankali na nace "sunana Maimoon Muhammad Dikko, I am Nigerian also, I.." Ya katseni "ambassador MD?" Nace "kasanshi ne?" Yace "yeah..... Da akwai sanda baba yazo ya kaini embassy gurinsa, yace in ringa zuwa ina gaishe shi, amma kinsan halin students ban taba zuwa ba. So you are his daughter?" Na gyada kai ina murmushi, yace "nice to meet you Maimoon" nace "nice to meet you too Mahdi"
Thank and I love you all.

VOCÊ ESTÁ LENDO
Maimoon
RomanceIt is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny that totally changed her and left her hanging on a thin thread of her real self. It is a story about...