The Broken Heart 💔

7.9K 592 4
                                        

Kuka nayi sosai ni kadai babu mai rarrashina. Sai da nayi na gaji dan kaina nayi shiru. Na kashe radion na chire CD din na fito daga motar. Ta kofar baya na shiga gidan saboda bana son ganin kowa. Direct saman mu na hau na shiga daki na turo kofa. Na zauna a kan gado ina kallon rubutun jikin CD din.

I LOVE YOU.

Nasan Ibrahim yana sona but how much? Ni a tunani na in kana son mutum zaka so ka kasance tare dashi, ya kamata ace komai runtsi komai tsanani ace muna tare, we can face anything together. Amma yanzu ya tafi, ya kuma kashe wayarsa ma'ana baya son magana da ni, sannan kuma yace min "I love you?". What kind of love is this?

Na jawo kafafuwa na na dora akan gadon da dunkule a guri daya. I wished sanda ya fara cewa yana sona nace masa no, da ban saba dashi ba ballantana har inyi kewarsa. Da yanzu bana jin radadin da nake ji a zuciya ta. Na saka hannuna na jawo bargo na ƙudunduna.

Wa yace da Ibrahim na damu da kudinsa ko rashin kudinsa? As long as we are together, that's the only thing I wanted. A hankali na mayar da idanuna na rufe.

Kaina ne yake bala'in sara min, idanuwa na sunyi min nauyi. Da kyar na motsa ido na ina son in bude su amma na kasa. Muryar Mommy naji can nesa tana maimaita sunana "Moon3" na motsa bakina amma na kasa magana. Can nesa naji Daada tana to fa min adduoi sai kuma naji kukan Mommy kasa-kasa. To ita Mommy mai ya sakata kuka? Ko har yanzu zancen da Daddy yayi mana ne a ranta? Ita kuma Daada me ya kawo ta dakin mu? Ita da bata shigowa part din mu in har daddy yana nan.

Na tattaro dukkan karfina na bude ido na dan in tabbatar me yake faruwa. Ga mamakina sai naga dakin ya chanza min, ya koma kamar dakin asibiti, ga ledar ruwa nan a sakale a kusa da gadon da nake kuma daga dukkan alama ni ake karawa ruwan saboda igiyar hannuna ta shiga.

Mommy tana zaune akan kujera a kusa dani ta jingina kanta a jikin Daada wacce take tsaye a kusa da ita tana lallashinta. Dama Mommy ta saba, in dai wani a cikin mu bashi da lafiya to ta ringa kuka kenan har sai ya warke. Na kalli daya side din gadon. Hafsat ce a zaune a zabga tagumi fuskar ta da alamar damuwa.

To da gaske ni ce bani da lafiyar kenan tunda nice a kwance.

A hankali na furta "Mommy" ta dago jajayen idanuwanta ta kalleni sannan ta kalli Daada wacce itama ni take kallo. Gaba daya suka karaso kusa dani Mommy ta rike hannuna mai dauke da drip. Nace "mommy wai bani da lafiya ne?"

Da sauri mommy tace "lafiyar ki kalau my daughter, kawai zazzabi ne kike yi, maybe ma malaria ce" Mommy bata iya karya ba dan haka tana fada na gane ba haka bane. Hafsat ta fita sai gasu sun dawo tare da likita. Dan matashin saurayi ne haka dogo marar kiba. Ina ganin sa gaba na ya fadi. Ibrahim. This is not Ibrahim. Ibrahim is gone.

Na rintse idona kaina yana cigaba da sara wa. Doctor din ya auna ni yace "zan sake yi mata allurar bacci saboda ciwon kan, kar a tasheta sai ta tashi da kanta, in ta tashi sai mu sake gwada jinin nata mu gani in ya sauka"

What? Me likitan nan yake nufi in jini na ya sauka? Yaushe ya hau ballantana ya sauka? Shigar allura naji a cinyar hannuna daga nan kuma shikenan.

Sanda na sake bude ido na Mommy na sake gani a zaune a inda take, amma ta chanza kaya, fuskarta harda kwalliya. Da sauri tazo kusa dani ta zauna tana murmushi. "Sannu Moon, ya jikin naki?"

Nima nayi mata murmushi nace "da sauki Mommy" ta dauki wayarta tana waya, daga alama Ya Walid ta kira, naji tana ce masa na farka su shigo. Ba'a jima ba sai gasu complete har Daddy. Duk sunyi kwalliya kuma kowa da murmushi a fuskarsa. Nan da nan dakin ya hargitse da hayaniya kowa a cikin su na kokarin jawo attention dina zuwa wajensa. Daddy ne ya, dauko wata sabuwar system kirar apple, red colour, yace "surprise!!" Ya miko min, na tashi zaune da sauri, ciwon kan ya ragu sosai, na karba ina godiya, yace "get well soon sunshine" sannan yayi min kiss a goshina, the same spot da Ibrahim yayi min ranar da zamu rabu.

MaimoonWhere stories live. Discover now