Born For This

9.9K 712 11
                                    

Jin bance komai ba yasa Sultan yayi ajjiyar zuciya yace "am sorry, maybe it sounded like an insult to you. Allah ya baki hakuri. Kawai dai na fada ne saboda ni bana iya rike abu a raina. I don't deserve you, I know. Kawai dai na dauka for once maybe zan zama lucky" na kalleshi ina girgiza kaina nace "am not saying no Sultan, am just not saying yes. Duk wannan abin yayi sauri da yawa, bamu dade da haduwa ba. I don't know you and you don't know me and....... It is very complicated" ya cire glasses din idonsa ya dora akan dash board yace "look ba fa cewa nayi zan turo iyayena ba ko something like that, am just asking for your permission to love you"

Nace "na sani, amma still, indai har soyayya ce dole a kafa ta akan yarda da juna da aminci. Kafin in ce ina sonka ko bana sonka dole sai na sanka first. Sultan I don't even know your real name, babu abinda na sani a tare da kai"

Guri ya samu a gefen titi yayi packing ya juyo yana kallona sosai, yace "saboda rannan kin tambayeni about my mother and I cut you off shi yasa kike cewa haka ko?" Nace "well, yes, na gaya maka almost everything a kaina amma kai ka kasa gaya min komai, ta yaya kake so in fara relationship da kai ba tare da nasan komai a kanka ba?" Yace "I didn't tell you anything about my mother because I don't know" ya buga hannunsa akan steering alamar ransa ya fara baci.

Nayi shiru bance komai ba ina gudun kara bata masa rai. Mun jima a zaune sai ya fara magana "Kince baki san real name dina ba, it is Abbakar Sadiq Abdallah, for some unknown reason babana ya saka min sunansa, a game da mahaifiyata kuma bansan komai akanta ba kamar yadda na riga na gaya miki, it is as if she didn't exist, babu wanda yake maganar ta, abinda na sani kadai shine sunanta, shima kuma a jikin birth certificate dina na gani. Tun tasowa ta a gidan kakana na taso, kakana wanda ya haifi mahaifina lokacin shine sarki ba Takawa ba. Duk duniya zan iya cewa daga shi sai Amir zan iya nunawa ince wadannan suna sona dan soyayyar da ya nuna min sanda yana da rai ko 'ya'yansa bai nuna wa irinta ba. Tun ina yaro nasan Takawa shine babana amma kuma tun a lokacin nasan baya sona, dan har yanzu ina tuna lokacin da in yazo gidan zan kama rigarsa in rike ina kuka shi kuma yana ture ni har sai na fadi sannan yayi tafiyarsa. Kakana lokacin shi zai daukeni yayi ta rarrashina. Gata kam a lokacin na gani, duk abinda nake so shi za'a yi min, babu wanda ya isa yayi min tsawa ko fada koda kuwa Yaya ce, Yaya itace kakata wacce ta haifi babana, dan haka na taso a sangarce, babu mai sani babu mai hana ni, wani lokacin sai in zauna inyi ta kuka ince ni gurin Mommy na da Daddy na zanje ko wanne yaro yana gurin iyayensa banda ni, a irin wadannan lokutan ne marigayi sarki ya dauke ni ya kaini orphanage ya nuna min yaran gurin yace 'kaga wadannan yaran su basu san uwarsu ba basu san ubansu ba, basu san kowa a dangin su ba, kai kuma kasan babanka, kasanni ni kakanka, kasan dukkan danginka na gurin babanka to kamata yayi ka godewa Allah', a orphanage din Allah ya hada ni da Amir"

Na kalleshi da sauri ya gyada min kai "yes, Amir is an orphan. Babarsa tana haihuwarsa ta dauke shi daga shi har mahaifarsa ko cibiya bata yanke masa ba ta ajiye shi a kofar orphanage ta gudu. Kakana shi ya rada masa sunansa Abdallah shine ake ce masa Amir. Sanda yake kai ni orphanage ya hada ni da shi, tun a lokacin muke abota da yake halin mu yazo daya na kiriniya kuma jinin mu ya hadu, daga baya in munje in zamu taho sai yayi ta kuka yace sai ya bi mu, sai kawai kakana yayi adopting dinsa ya saka mu a makaranta tare, komai tare muke yi dashi har yau."

"Lokacin da kakana ya rasu ne rayuwata ta chanza gaba daya, I was ten years old then, nayi ta kuka akayi ta rarrashi na naki hakura, Takawa yana zuwa ya kama ni ya daure min hannaye da baki na ya saka ni a dakina ya rufe kofar. Haka na kwana ina kukan zuci babu bakin yin kukan ga uban dauri da nasha, sai washegari sannan ya aiko aka kunce ni kuma yace in na sake kuka sai ya kuma daureni. Daga ranar nasan na rasa soyayya a rayuwata. Hankali na bai kuma tashi ba sai da aka nada babana sarki, ya dauko iyalansa wadanda ko saninsu banyi ba tunda baya bari inje gidansa ya dawo palace. Ni na riga na saba duk abinda nake so shi zanyi, tun da ya dawo gidan kuwa sai ya zamana duk abinda nayi no matter how small ba zai yi min fada ko nasihaba sai dai ya saka dogaran sa suyi ta dukana, wani lokacin har Amir za'a hada a daka koda kuwa ni kadai nayi laifin"

MaimoonWhere stories live. Discover now