Bayan Wata Uku
Rayuwa tana tafiyar mana sosai cikin jin dadi. Dan ni kam a bangare na bani da problem. Su Hajiya tun ranar da suka zo na kora musu bayani basu sake dawowa ba, su Fa'iza su na dan zuwa kadan kuma sam ban taba daure musu fuska ba. Amira ma ta dawo twice, mu kan danyi hira kadan amma sam na kasa sake wa da ita kamar da, mun koma kamar strangers. Kullum kuma in tazo bata da zance sai na aure, ta gaji da zaman gida yanzu aure take so dan yanzu kullum suna cikin samun sabani da mamanta.
A bangaren Sultan kuma tunda ya gama hutun angwancin sa ya koma aiki ya zama busy, dan kullum sai dai akai masa lunch dinsa office, sai bayan la'asar yake dawowa, amma kuma in ya dawo din in ba dole ba baya fita ko kofar gida sai dai in zashi masjid. Kullum companyn sa kara haɓaka yake yi, dan yanzu da kansa yake karbar kwangilar gine gine yana yi, na government ko kuma na private mutane. Sultan ya rike addini sosai dan har mamaki yake bani yanzu, karatun qur'ani kam kullum sai yayi safe da yamma, wani lokacin na yamman muyi tare.
Ni kuma babu abinda nake yi a gida sai koyon girki, dan a yanzu Asma'u tafara bari na ina yin abincin da kaina, sai dai ta dan ci gyarana kadan, a raina nakan ce 'ashe ma abin babu wahala, kawai sa kai ne' tun daga kan main dishes, snacks, drinks babu abinda Asma'u bata koya min ba, har abinciccikan mutanen ketare, tace so take yi in na fara yi wa Sultan girki duk abincin da yaci idan ba nawa bane ya ji ci salam. Duk abinda kuwa na dafa ko Sultan baya nan sai na ajiye masa na bashi yayi tasting, Sultan kam ko abin bai yi dadi ba cewa yake yi yayi dadi duk da nasan wani lokacin alkunya kawai yake yi min, amma kuma sosai yake nuna jin dadin dedication dina dan yasan dan shi nake koyon kirki, dan in faranta masa ba wai dan kaina ba.
Soyayya tsakanin mu kuwa kullum karuwa take yi, ni da na dauka da anyi na dokin aure shikenan amma ashe ba haka abin yake ba, stamina din Sultan har mamaki take bani, dole na na yawo jakar magungunan Daada na cigaba da amfani dasu dan kar yaga gazawa ta.
Mun je gida ranar da Daddy ya dawo daga England, tunda akayi biki na sai ranar naje gida, da gudu naje na rungume Mommy, ita kam kallo na kawai take yi dan gaba daya na chanja, nayi kiba na kara chika, fata ta har wani yellow take yi saboda haske. Sau da yawa in kawayena suka zo sukan tsokane ni suce ko ciki ne dani, amma ni nasan bani da komai, dan cikin wata ukun nan ko tsallaken period ban taba yi ba.
Ranar a gida Sultan ya barni na wuni. A lokacin ne Amina take bani labarin yadda suka kare da Ibrahim, naji dadi duk da dai tace min yace bayason jin labarin Sultan, kawai shi fatansa if am OK shikenan, nan take min complain cewa he is becoming a little bit attached nayi dariya nace "then it is going more than I expected" ta bata rai tace "ya zaki ce haka. That guy is still madly in love with you, I am feeling like yana kulani ne because I am his only link to you"
Nace "in that case then alakar ku ba zata dore ba and you don't have to worry tunda ke you are not getting attached, da zarar yayi realising ni da ke da banbanci shikenan zaiyi tafiyar sa" na fada ina studying dinta, tayi shiru tana kallon gefe ta kasa hada ido dani, na dafa kafadar ta nace "or are you too getting attached to him?"
Ta dan ture hannuna tace "shirme ma kike fada. Ni bai ma yi min ba, too arrogant for my taste" nayi dariya, amma na riga na fahimci abinda nake so na fahimta, Amina has fallen in love with Ibrahim, sai dai tsorona daya kar zargin da take yi akan sa ya zama gaskiya, cewa yana kulata ne saboda ni. In dai har zai so ta, I will want him to love her as Amina, not as moon's cousin or as moon's look alike.
Sai kuma ta dan turo baki tace "amma yana da matsala, in muna tare sai yayi ta kokarin kama hannuna, ni bana son wannan dabi'ar" Nace "yi hakuri Amina ta, abinda nake so ki gane shine, Ibrahim was born and raised in yoruba land, they are Muslims and then they are yorubas, su a gurinsu it is nothing dan saurayi ya rike hannun budurwarsa"
YOU ARE READING
Maimoon
RomanceIt is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny that totally changed her and left her hanging on a thin thread of her real self. It is a story about...