Gaba na ne ya fadi da muka hada ido da Munnir wanda ya kasa ya tsare yana kallon duk wanda zai yi min magana. Na tabbatar Sultan yana shigowa zai hangoni tunda ina kan high table, yana gani na kuwa zai taho, Allah ne kuma kadai yasan abinda zai faru tsakanin sa da Munnir.
Na rada wa Hafsat "two minutes, ina zuwa" ta yi sauri ta rike hannuna alamar bata so in tafi in barta, nayi mata alamar yanzu zan dawo. Cikin friends din mu na ɗan shiga, ina kallon Munnir ta gefen idona yana bina da kallo, sai da na tabbatar baya gani na sannan nayi hanyar entrance da sauri.
Ina zuwa kuwa na ga Sultan ya dunkule hannunsa ya naushi wani mai gadi, nan na nan jini ya fara fita ta hanci ta baki, maybe ma hakori ya fita, wanwar gayen ya fadi a kasa yana gunjin azaba, Sultan ya durkusa kusa dashi, na dauka ma hakuri zai bashi, sai naga ya goge jinin daya bata masa hannu a jikin rigar gayen, ya mike tsaye yace "who is next?, dan rainin hankali har ni zanzo ince zan shiga guri ku ce min card admit ne, da card din da admit din duk naci uwarsu gaba daya"
Da sauri na karaso gurin cikin tashin hankali nace "what the hell are you doing" sai a lokacin ya ganni, hannu duk biyun ya saka a cikin gashinsa yana matsawa baya a hankali tare da cewa "shit" na durkusa gurin mai gadin da aka daka wanda har yanzu ya kasa tashi na fara jera masa sannu cikin kulawa, da sauri sauran guards din suka karaso suka kamashi suka tafi.
Na mike ina kallon Sultan daya kasa hada ido dani nace "what are you doing here?" Ya karaso kusa dani yace "am sorry" sai a lokacin na lura da wanda suke tare, zasuyi kusan tsaho daya da Sultan amma bazan tantance kibar saba saboda uban kayan daya loda a jikinsa duk kuwa da yanayin zafin da ake ciki, kansa yasha kwal kwal amma kuma ya bar saje a fuskarsa.
Kallo daya nayi masa na maida kallona kan sultan wanda yasha kwalliya dan daga gani wannan shigar ta musammance. Har yanzu ya kasa magana ni kuma na bata rai na tsare shi da ido. Abokinsa ne yace "so, kece wannan Hafsan da ta hana abokina bacci kenan, you are really worth the trouble" sai a lokacin na tuno cewa ashe fa ce masa nayi sunana Hafsat. Na dan yiwa abokin murmushin yaƙe sannan na kuma mayar da idona kan Sultan na sake cewa "uhum, ina jinka, me ya kawoka nan?"
Ya sake hargitsa gashin kansa sannan yace "I just wanted to see you ne, please, number da kika bani bata shiga, shine naje address din shima na tarar wrong ne da kyar yarinyar gidan ta kawo munan" nace "OK, ka ganni zaka iya tafiya yanzu" ina fadin haka na juya zan koma ciki, da sauri yasha gaba na, fuskarsa kamar wani abin tausayi "please kar ki koma" nace "serious, bani da lokaci, biki muke yi, na tabbatar yanzu ma nema na akeyi a ciki" da sauri yace "OK, at least ki gaya min sunanki na gaskiya, ki bani number din ki ta gaskiya" ya saka idonsa cikin nawa pleadingly, kawai sai naji na daina jin haushinsa, ya danyi murmushi tare da cewa "pretty please" na danyi murmushi nima kadan.
Abokinsa ne yace "OK, lokacin introducing dina yayi" daga ni har Sultan babu wanda ya kalleshi, sam ya kasa dauke idonsa daga cikin nawa, ni na fara dauke kaina nace "I.....I really must go inside" yace " OK, sunanki na gaskiya" nace "Maimunatu" ya dauko wayarsa yace "phone number?" Har na fara fada masa sai ya dakatar dani yana karkada hannunsa "not again, an sha ni na warke" ya miko min hannunsa "bani wayarki" na gane me yake nufi dan haka nima nayi dariya tare da mika masa wayar, ya karba ya saka number dinsa yayi dialing, da kiran ya shiga wayarsa sai da ya dauka ya tabbatar shine sannan ya katse ya daddanna, na fahimci saving number dinsa yayi a waya ta sannan ya miko min.
Ina karba naga an bude kofar hall din an fito, a tsorace na waiga, yaya Habeeb na gani a tsaye yana kallon mu ni da Sultan, sai kuma ya koma ya maida kofar ya rufe. Na sauke ajiyar zuciya nace "zan koma kaga already ana nemana" ya gyada kai yace "it is OK, nagode sosai, and please don't block my number" nayi murmushi nace "I won't" na juya na kama hanyar komawa ciki, naji abokin sultan yana cewa "hey, bakayi introducing din mu ba fa".
VOCÊ ESTÁ LENDO
Maimoon
RomanceIt is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny that totally changed her and left her hanging on a thin thread of her real self. It is a story about...